← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 267

Sashe 64

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki Umaimah tayi tace
"Ni wallahi na dauka ma wani abun ne saboda duk tsomaye aka tara a group din shiyasa suke ganin duk abinda tayi ko ta fada qaryane, nifa shiyasa kikaga na dena magana sosai tunda wata tace wai ina maqe murya idan ina magana suka nemi sumin taron dangi nayi musu tas shiyasa na rage kula yan group din nan dan naga duk masu kalan wayewa ne suke claiming su wayayyu ne, Maman Nihal kuwa ni  dana ganewa ido na zahiri akanta ai bazan musa mata ba, ai da nasan kallon da kike mata kenan na yar qarya da dake zamuje gidanta wallahi ki ganewa idonki, amma ki shirya Wani satin bakin qanwarta dukda da bazanje ba amma yanzu ko dan ke da sauran munafukan yan group zamuje, ga katin nan ta kawo mun dauka ki gani" Umaimah ta qarasa tana miqa mata hadadden katin gayyatar Kamun da aka Rubuta sunanta wato Zainab Ladan a matsayin me gayyata.

Rufaida ta karba tana bude baki cike da mamaki tace
"Dan Allah dagaske yanzu duk wannan Aljannar duniyar da take daukar hoto a ciki ki cemun gidanta ne, kinga wasu danqara danqaran daham da take sakawa kuwa kai ni Umaimah ina tantama gani nakeyi kamar dakko hoton irin hamshaqan matan nan takeyi a IG"

"Se kiyi ai, nan nan Third Get gidanta yake cikin sabuwar Abuja, qarshen tika tika dai ki shirya muje bikin qanwarta ki ganewa idonki" Umaimah ta sake fada,
"Aikuwa Allah ya kaimu dole ma naje na kashe qwarqwatar ido na dan indai da gaske itace wannan hamshaqiyar dole bikin na manya ne za'a gwangwaje.

Umaimah dai shiru tayi, tana jin kamar ta gayawa Rufaida zancen aron sarqarta da tayi amma tayi shiru haka suka ci gaba da hira har kusan takwas da rabi kafin mijinta ya kirata akan ya dawo suka fita ta rakata daidai sanda Khalil shima yayi fakin a qofar gidan.
Haka aka qarasa cinye sati daga Umaimah har Rufaida babu wanda ya samu zuwa bikin Hamida qanwar Maman Nihal, a ranar Umaiman ta tashi da ciwon Mara dan har seda sukaje Asibiti aka ce ba haihuwa bace da saura itama Rufaidan ashe Anam ce tayi fama da zazzabi seda aka kwana biyu ta shiga take gayawa Umaimah daga nan suka yanke idan Umaimah zataje asibiti zata rakata se su je gidan.

An yi bikin Hamida da kwana uku Maman Nihal ta aiko mata da uban hilin kayan fulawa na gara harda su soyayyun kaji da dambunsu ko wanne cikin Farin bokiti qarami, me delivery ta bawa ya kawo mata tana zaune kawai aka kirata wai ga saqo inji Maman Nihal Janbulo lokacin Habiba Qanwar Khalil da Sharifa qanwarta yar dakin Anty suna gidan saboda anyi hutun makaranta sukaje tayata zama saboda Khalil din be cika zama sosai ba saboda aiki.

Bayan sun karbo saqon ta bincike tas bata ga abinda take tsammani ba koda yake ya za'ayi ta bawa me delivery sarqa ya kawo mata itama ta bada tata ya kai mata ai ganganci ne seta shiga kiranta a waya, sau biyu ta kira wayar ta qaraci ihunta ba'a daga ba, tunanin yi mata magana a WhatsApp tayi dan daman tunda suka fara bikin basu yi waya ya kai sau uku ba sedai a WhatsApp shima atsaitsaye saboda Zainab din itace kamar uwar Amarya ita ce akan komai.

Dadi taji ganin tana online tayi mata sallama tareda godiyar kayan da aka kawo har tana cewa sunyi yawa kafin tace mata
"Da zan bada sarqar ki ya kawo miki se naji tsoro ban san ko na gida bane kin saba harka dashi kuma nayi kiran wayarki baki amsa ba"

"Kedai kice kina mun tunin sarqar ki Amma ni tawa ko shekara zatayi babu damuwa ki ci gaba da ajiye mun, taki kuma abinda yasa ban bayar ya taho da ita ba gaskiya ban sanshi ba wata ce ta hadani dashi Walid nake so na bawa ya kawo miki dan ma bazan samu shigowa da kaina ba dan yanzu haka ma kin ganni muna Aiport zamu tafi America kai Amarya, kinsan da na gaya miki babu yan rakiya se fa jiya uban mijin yace wai bazeyuwu ace babu wanda yaje yaga dakinta ba" Maman Nihal ta turo mata da dogon voice note, Mamaki ya kama Umaimah dan gaskiya bata tuna sunyi zancen Amwrica za'a kai Hamida ba ta dai gaya mata a Tarauni gidanta yake amma Mijin a Abuja yake aiki bayan biki zasu tafi can to qila kuma chanjin shawara suka samu abun na masu dashi, Vn din tayi mata tace

"Toh Allah ya kaiku lafiya ya dawo daku lafiya, babu damuwa ki bawa Walid din idan yazo kinga ma sena bashi takin"

"Kawo miki in sha Allahu bari naje an fara kiran mu idan mun sauka zamuyi magana" Maman Nihal ta bata amsa kafin ta sauka offline.
Warkaja min su sukaji gaba dayi da kayan gara, koda Khalil ya tambayi daga ina tace masa Mama ce tasa akayi mata tace tana so ya ringa mata fadan cin zaqi dukda be yarda Maman bace ta bayar sedai idanda kudinta ta saka akayi mata zata fake da cewa Mama qarshe da Habiba da Sharifa zasu wuce ya kwashe ya raba musu suka tafi dashi.

Seda aka kwashe sati biyu babu Maman Hanif babu labarin zuwan Walid, da farko Umaimah ta shiga damuwa amma data tuna akwai tata sarqar a hannunta se taga babu amfanin damuwar dan ko riqe waccen tayi tasan taci riba akanta dan wannan tafi tata daraja ko daga gani a ido ma.

Sati biyu a tsakani ta tashi da naquda, cikin ikon Allah zuwan su Asibiti a qasa da awa biyu se gashi ta haifo qaton danta me kama da Khalil kamar yayi kaki ya ajiye, haka suka tafi ziqau babu ko kyallen da za'a lullube jariri dashi dan dama shi Khalil be san ana tafiya da wasu kaya ba, a tasa wautar ma a Asibiti akw bayarwa duk se ayi maka bill ka biya shiyasa be taba ma tambayarta wani ko da akwai abinda za'a tanada ba, kayan barka da Hajiyar sa tayi masa magana kadai ya sani kuma ya gama dasu dab tuni ya bada kudin komai yace kar su siyi riguna dan basusan abinda za'a haifa ba.

Metron din tayi musu uzurin qila basu san haihuwa bace tunda a EDD dinta na farko ma tana da sauran kusan sati daya dan haka ta ari zani a gurin wata da take labor itama aka nannade yaron bayan an gogeshi tacewa Khalil yaje ya kawo abubuwan buqata.

Kaitsaye gidan Hajiyarsa ya nufa, kamar daga sama taji labarin haihuwar ga kuma zancen ai basu je da komai ba dan shi bema san me za'a dauka ba koda yake daman me suka ajiye a cikin gidan. Fada ta ringayi masa ta hada duk abinda ya kamata daga wanda suka siya sannan suka wuce can gidan tace ya dibo mata kaya kala uku masu zani, dakyar aka samu daya qarshe se dogayen riguna ya diba suka wuce Asibitin acan suka tarar da Mama da Anty harda Maman Asad dan ita ya fara kira ya gayawa ita kuma ta gayawa su Maman.

Sun tarar da Mama akan Umaimah tana surfa mata fada ga Jaririn da ya sha nadi a zanin Atamfa saboda sanyi a hannun Anty, Hajiya ce ta shiga tayi sasanci Mama tace
"Banda wauta da shirme Hajiya ka taho haihuwa babu ko rigar da za'a sakawa Jariri, daidai da Pad da zatayi amfani da ita fa se ara akayi ni na rasa me yake damun wannan yarinyar sam ace bazata ringa abu irin na masu hankali ba"

"Haquri za'ayi abin barkar dai an samu kai qalau duk komai daga bayane gashi nan an kawo se a mayarwa da wadanda akayi aron a gurin su" Hajiya ta fada tana nuna mata qatuwat Akwatin data shaqo da duk abinda tasan za'a buqata, hatta Tissue paper sedata dakko. Mama bata haqura ba seda ta kuma yi musu tas daga ita har Khalil din kafin ta kama hanya Salman da ya kaisu ya maida ita gida ta bar Anty dan daman abinda ya kaita kenan taje ta karantawa Umaiman.

A Asibitin suka kwana se washe gari aka sallame su aka wuce da ita gidanta tareda Anty da zata zauna mata kwana bakwai zuwa ayi suna kafin su koma can gidansu taci gaba da wanka dan haka sukeyin Al'adarsu.

Khalil be saka a ransa ze bari ta tafin ba dan baya jij ze iya rabuwa da Dan babyn nasa da yake ji kamar ya hadiye shi tsabar qauna, ance dashi yake kama amma shi yafi hango kamannin Umaimah a fuskar yaron dan idonsa, bakinsa duk nata ne hancin ne da yanayin fuskar irin nasa kawai shidai Addu'arsa Allah yasa karya kwaso masa halin Tijararta.

Jego me kyau Anty ta dage tanayi mata suna samun kulawa daga ita har yaronta da Khalil yayiwa huduba da sunan Mahaifinsa Umar Bayero zasu ringa kiransa da Mu'ayyad, ranar kwana biyar aka kawo kayan barka daga gidansu Khalil, kaya wane kaya dan bayan wanda ya bada kudi aka siya yan uwa da abokanan arziqi sun ringa kai nasu Aka hado komai rigijib lefen dangata aka kaiwa Umaimah washe gari kuma aka kawo na gidansu shima sunyi qoqari sosai da sosai sukayi Babyn da ita kanta kaya.

A ranar Maman Asad ta karbo mata dinkunan kayan da zatayi fitar suna dasu Wanda daban Khalil ya bada kudin aka siye su, kayane kala biyar Atamfa biyu, Lace biyu se Shadda guda daya da sukayi anko dashi zasu saka da safe. Duk wani abin amfanin suna an tanada kama daga abinci da sha da kayan rabo sunyi komai cikin tsari ranar suna aka yankawa Yaro manyan ragunansa guda biyu ga su Biscuit alawa da dabino duk wanda ya shigo barka yan unguwa se an bashi.

Da safiyar tasha kwalliya da danyar  shaddar da sukayi anko da Khalil, Habiba ce tayi mata dauri me kyau dan ita din gwana ce gurin kwalliya dan ma Umaiman tace ba sannan za'ayi mata make up seda yamna dan haka hoda da man lebe kadai ta saka aka ringa kashe musu hotuna da babynsu daya sha kaya na alfarma yana ta bacci abinsa.
Chapter 64 · 0% Book details