← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 260 OF 267

Sashe 260

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KHALIL
Yana office yana qarasa wasu ayyuka besan magriba tayi ba seda kiran wayar ya shiga ya daga yaga lokaci, cikin muryar gajiya yayi sallama tare da ce mata
"Afuwan Love, aikine ya riqeni amma gani nan tahowa yanzu in Allah ya yarda duk kewar tawace tasa kika kasa haqurin jira?"

"Dady nice" muryar Bibi ta katseshi, seya dafe kansa, Allah yaso ba qata baranbaramar yayi ba. Cire wayar yayi da kunnensa yana qarasa hade takaddun gabansa dan yasan wayar Bibi ba qarewa take ba baze wuce qorafi bane an mata wani abun ba zata iya jiransa ya dawo ba zata kira a waya dan haka yace mata
"Meya faru sweetheart har kun dawo daga gurin Momyn taku ne?" Kamar tana jira kawai tasa masa kuka,da sauri ya aje takaddun hannunsa ya dauki wayar ya mayar kunnensa, yanda take kukan harda shashsheqa ya bala'in daga masa hankali take ya fara hasashe hasashen meya faru?

"Kiyi shiru gani nan zuwa gidan ok" yana gama fada ya kashe wayar ya zirata a Aljihu ya dauki abinda yake buqata badan ya gama aikin gabansa ba ya tafi gidan. A waje ma ya ajiye motar ya taka da qafa yana shiga ya tarar da Mu'ayyad zaune bakin qofar shiga falonsu ya rafka tagumi a fuskarsa zaka karanci damuwa sosai gabansa ya sake yankewa ya fadi, to meya faru ne? Mu'ayyad dinna ganinsa ya miqe tsaye amma ya kasa yin magana Khalil ya matsa kusa dashi ya kama hannunsa yana cewa
"Wai meya same ku? wani abu akayi a can gidan ne?"

"Dady.." Mu'ayyad din ya kira sunansa se kuma ya sunkuyar da kansa qasa ya kasa cigaba da magana Khalil ya zuba masa ido yana karantarsa, Mu'ayyad yarone me shiru shiru sosai sam bashida hayaniya ko kadan halinsa sak na takwaransa Mahaifinsu yana kuma da qoqarin shanye damuwa da wuya kaga ya furta fushi ko ya nuna a fuskarsa dan haka yasan yanzun dole da akwai wani abun daya faru.
"Ina Bibi?" Ya tambayeshi swya bude baki kamar baya so yace
"Tana ciki, kuka takeyi tun dazu taqi tayi shiru".
"Me akayi mata take kuka kai kuma meya bata maka rai?" Khalil din ya sake jefa masa wata tambayar aeya kuma sunkuyar da kansa kafin ya dago kamar an fizgo maganar daga bakinsa yace
"Momy ce zatayi aure, saura 4 weeks".

Yanda kasan wanda ya harba da bindiga haka yaji har seda ya saka hannu ya dafe qirjinsa da yaji tamkar ze fado saboda razana da zancen Mu'ayyad din.
"Aure" ya maimaita kalmar a fili Mu'ayyad ya daga masa kai kafin ya qara da cewa
"Tace na roqeka ka amsa wayarta ko minti daya ne ka bata tana so kuyi magana". Tabbas yaji abinda yaron yake cewa amma kwakwalwarsa bata iya fassara masa ba, se kawai ya tura qofar ya shiga yana tafiya kamar wanda ya fito daga sahara saboda yanda wata irin kasala take bin qabobinsa tana riqe su.
Humaira na tsaye gaban Dining tana gyara kwanuka yanda ya bude qofar yasa ta waiwaya ta kalleshi, daman tasan duk inda yake dole yana hanya tunda an taba yar gwal. Yanda taga fuskarsa da yanayin sanyin jikinsa yasa ta ajiye abinda takeyi ta nufeshi tana cewa

"Lafiya kuwa?" Tayi saurin tareshi saboda tuntuben da yayi da jirgin Adil ya tafi kamar ze kifa qara yunqurawa yayi yana yin taku biyu ya sakeyin baya kamar wanda Jiri yake diba seta riqeshi a jikinta, yanda taji zuciyarsa na bugawa da qarfi ya saka ta ce masa
"Ka zauna Dady bari na dakko Mayafina mu tafi Asibiti baka da lafiya" swya girgiza mata kai dan harshensa ya masa nauyi Mu'ayyad dai na tsaye a bayansu ya harde hannaye a qirji ya miqa masa hannu ya matso dakyar ya iya cewa
"Ku kamani muje sama Jiri kawai nakeji nayi stressing kaina da yawa da nayi bacci zan dawo daidai".
Badan ta yarda ba kawai dan ya kafe akan lafiyarsa qalau din suka kamshi zuwa saman saboda yanda jikinsa ya saki ba zata iya riqeshi ita kadai ba. Har kan Gado suka kaishi ya zauna ta fita da sauri ta dakko masa ruwa tana fita Bibi ta shiga da kukanta tana cewa
"Dady wai Momy au...."
"Shut up and get out" ya buga mata razananniyar tsawar data saka Humaira sakin Bottle din hannunta babu shiri ta toshe kunne, Bibin da yayiwa tsawar kuwa rikicewa tayi ta durqushe a gurin kukan data shigo dashi ya bace bat se rawa da jikinta ya dauka kamar mazari saboda tsoro.

Kallonsu yayi gaba daya se kuma yaji wani iri a hankali yace
"I'm sorry, banyi niyyar na tsorata ku ba. Ina buqatar hutu yanzu ku fita kawai kar wanda ya sake shigowa idan bani na buqata ba". Yana rufe baki Bibi ta fice da gudu har sannan jikinta rawa yakeyi dan tunda take Dadyn be taba daga mata murya balle yayi mata tsaya irin haka, Humaira ma fita tayi jiki a sanyaye a ranta tana tunanin to meya faru ne me ya saka Khalil din birkicewa haka?

Kallon Mu'ayyad yayi dake tsaye ko gezau beyi ba har sannan hannayensa harde yana kallon Khalil din shima, wani abu me daci ya hadiye kafin ya bude baki da kyar yana kallonsa yace
"Wa zata aura?"
"Nima ban sani ba, tace ka kirata nasan zata gaya maka" ya bashi amsa seya daga masa kai kawai dan maganar qara harzuqo masa zuciya takeyi. Ya ringa juyi akan gado yama rasa tunanin me zeyi, aure? Umaimah? Abubuwan da suka ringa masa yawo a kwakwalwa kenan. Har gurin qarfe goma ya gagara qulla komai, kamar ya kirata yanda ta buqata to me zece mata ko me zata ce masa ma idan ya kiratan? Badai aure zatayi ba taje tayi shi meye nasa a ciki?

Yana kwance yana malelekuwa, tunawa da yayi da ko sallar Magriba beyi ba gashi har anyi Isha tuni ya sakashi miqewa dole yana dafa bango saboda ciwon da kansa yake masa ga jiri ya shiga bandaki. Seda ya watsa ruwa kafin ya rama sallolinsa, yana zaune ya janyo wayarsa dake kan gado dan tun yana sallah take kawo haske saboda a silent take, missed calls din Humaira ya gani seya miqe jikinsa a matuqar sanyaya ya fita daga dakin. Tana zaune a falo gaba daya ta firgice itama baya zaton ko abinci taci ya qarasa kusa da ita ya zauna murya babu amo yace
"Ina yaran?"
"Sunyi bacci" ta bashi amsa tana kallonsa seya kallo agogon dake jikin bango, goma harta gota ashe ba qaramin lokaci ya bata a kwance ba. Janta yayi jikinsa yana cewa

"Kuyi haquri dazu na tsorata ku raina ne a bace ita kuma tazo tana yi mun kuka"
"Amma ka tsoratata sosai, dakyar tayi bacci tana ta kuka ni kaina kukan ne kawai yaqi zuwar mun amma tunzu nake so nayi, waye ya bata maka rai " da yaja ka huce akan mu?" Humaira ta fada tana dora kanta a qirjinsa, yanda zyciyarsa take bugawa ya sakata dagowa ta kalleshi ta sake cewa
"Kaji bugun zuciyarka kuwa? Dan Allah ka gaya mun meya sameka?"
Murmushi yayi yana maida kanta qirjinsa yace
"Babu abinda ya sameni, wani abu ne dai yake damuna amma na roqi Allah nasan ze yaye mun"
"Tunda kace Allah ka gama komai, amma idan ba zakaje Asibiti ba ka kira azo gida a dubaka dan wannan bugun zuciyar ya wuce normal ga jikinka ma yayi zafi"

"Humaira, na gaya miki lafiyata qalau da nayi bacci koma menene ze dena, ki dena damun kanki" ya fada a tausashe dole tayi masa shiru kusan minti biyar ta miqe ya kalleta yana tambayar ina zataje tace Abinci zata kawo masa
"Naqoshi, bazan iya ci ba" ya bata amsa kai tsaye, seta dauki dankwalinta dake ajiye tana cewa
"Gara naje na gayawa Hajiya kawai qila ita idan ta maka magana zakaji ya zakace mun lafiyarka qalau bayan gashi nan jikinka duk ya nuna baka da lafiya"
"Saboda kawai nace bazanci abinci ba shine zaki gayawa Hajiya? To ki kawo mun Tea, cikina ya cushe bazan iya cin wani abu me nauyi ba" ya fada yana kwanciya. Ta kawo masa Tea din da cake harda maganin ciwon kai dayace yana damunsa yana sha ya koma daki ya kwanta, damuwar data shiga ta sakashi dole ya saisaita kansa amma abin yafi qarfinsa, kafin safiya zazzabin gaske ya rufeshi da ciwon kai me tsanani sannan bugun zuciyarsa ya qaru sosai har qirjinsa yana dagawa. Duk yanda Humaira tayi dashi akan su tafi Asibiti yaqi, yasha paracetamol kawai yaci gaba da kwanciya a cewarsa stress ne daya samu hutu ze warware nan kusa qasan ransa Allah kadai yasan irin jinyar da yakeyi.

Idan ya tuna wai Umaimah zatayi aure zata zama mallakin wani bashi ba se yaji kamar yayita kwala ihu. Hajiya da taji shi shiru tun dare be shiga ba ga safiya tayi har gurin goma nan ba babu labarinsa ta taka dakyar saboda jiki daya motsa mata itama kwana biyu taje bangaren nasu dan ta duba ko lafiya ta saba yaran ma kafin su fita makaranta duk zasu shiga yau kuwa babu wanda ya leqata. A Kitchen ta tarar da Hunaira na hada masa faten dankali dan yaqi cin komai da sukayi na kari yace shi yake so, ta gaida Hajiyar, yanda ta ganta sukuku ya sakata tambayar lafiya take idon Humairan ya kawo ruwa tana gaya mata Khalil bashida lafiya tun jiya kuma yaqi yaje Asibiti. Hajiya ta ringa masa fada yanda taga jikin nasa dole ya tashi badan yaso ba suka tafi Asibitin ruwa aka fara daura masa kafin sauran gwaje gwaje ya biyo baya Likita yace musu da Malaria yar kadan se damuwa itace ta haddasa masa bugawar qirji da ciwon kan. Ranar a Asibiti suka wuni, Hajiya ta sakashi gaba da tambayar meyake damunsa da har yake neman ya kwantar dashi ciwo amma ya kafe akan babu komai shi ba damuwa bace ayyukane da suka masa yawa kwana biyu dan Anwar baya nan shine kawai gajiyace, badan ta yarda ba ta rabu dashi sedan likitan yace kar su ringa matsa masa su barshi ya samu wadataccen hutu tukunna.

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 89
Chapter 260 · 0% Book details