← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 265 OF 267

Sashe 265

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan Allah Hajiya ku yafemun, ki roqar mun suma su yafe mun abinda nayi musu" Umaiman tayi magana a karon farko dan tunda ta gaida Hajiyar take kuka, Hajiya ta jata jikinta tana cewa
"Sau nawa zan maimaita miki Umaimah mukam baki mana komai ha idan ma da akwai mun yafe, Allah ya rigada ya qaddaro duk abubuwan da suka faru bamu da yanda zamuyi kuma na godewa Allah da hakan yasa kika gane kuskurenki kuma kika gyara daman haka ake son mumini na kwarai idan yayi kuskure ya gane ya tuba ya nemi yafiyar ubangiji sannan ya guji sake maimaita abun a gaba, Allah yayi muku Albarka ya cigaba da yi muku jagora a rayuwa in sha Allahu zanzo idan kin tare naga dakinki kinji" haka ta ringa lallaba Umaiman har tayi shiru ta bar kukan, ta jima sosai a gida har seda tayi sallar Magriba Abba ya dawo suka gaisa kafin Driver daya kawota yake jiranta ya dauketa suka tafi.

Washe gari haka aka tattarata aka kai gidan KB da take ji kamar kurkuku aka kaita. Basu tarar da matar gidan ba dan muqullin qofa ma yaronsa ya bawo ya kawo musu daga Kasuwa se bayan sun shiga sannan wasu Mata suka zo a matsayin yan uwansa suna ta bada haqurin rashin zuwa dauko Amarya wai wadanda aka saka su kaisu ne basu je da wuri ba sun tafi kuma ya kirasu yace ai har an kawo Amarya ma. Ita dai tana lafe akan gado ta kasa yin koda kwakwkwaran motsi tunin wannan sabuqar rayuwa data shigo kawai takeyi seda yan rakiyar tata sukayi Magriba kafin kowacce ta kama gabanta aka barta ita kadai tsuru kamar mayya a gida. Ta gaji da zaman daki ta fito tana leqa falon, qato ne ya kuma tsaru dakyau dakuna uku ne a ciki da a zaton ta daya na matar gidan daya kuma qila na yara ga qofar kitchen nan da take hango ciki saboda qofar irin ta glass ce batayi gigin shiga ba ta koma daki taci gaba da jan carbi har akayi Isha babu Ango babu matar gida tana zaune har ta fara gyangyadi sannan taji motsin ana taba Get ta zabura ta miqe, Windon dakinta a cikin compound din yake dan haka ta leqa, motar Kb ta gani ya fito yaci uwar babbar riga kamar gaske ya ringa kwaso ledoji yana shiga dasu falo harya gama kafin ya shiga dakin lokacin ta koma bakin gado ta zauna.

Bakinsa a washe kamar wani soko ya nufeta yana cewa
"Sorry Amaryata mun barki ke kadai, go slow aka samu yau a hanyar Kasuwa na fito tun kafin Magriba amma babu hanya kuma na tsaya na siyo miki kazar Amarci" ya qarasa yana wani kashe mata ido daya. Takaici kamar ta kwada masa mari seta juya fuska tareda jan tsaki ya tsaya cak a inda yake murmushin fuskarsa yana bacewa yace
"Na miki uzurin yau kadai amma ki sake mun tsaki ki gani, dallah malama tashi an ma fasa tarairayar taki zanje nayi wanka kafin na fito ki shirya mun Abinci a Dining kuma ki dumama komai kafin k ajiye".
"Wato auran yaro dai beyi ba" ta fada a zuciyarta kafin ta miqe tabi bayansa dan ta tabbata bayan Tijara ga danyan kai a tattare dashi shiyasa har yake gwada yar qashi da matarsa to ita dai na zata bashi wannan qofar ba, umarni dai in ya bata zatabi tunda qinyin kamar ta sabawa Allah ne baya ga haka ita ba zama ya kawota gidansa ba gara ta koma taci gaba da zaman gidansu ya fiye mata alkhairi akan wannan rayuwar takurar da ake neman jefata.

Seda ta dumama komai kamar yanda yace ta shirya masa akan Dining din nama ne sunfi kala biyar harda wani farfesu, shi ta bari a microwave din ta koma daki kafin ya sakko, tana shiga taji yana kwala mata kira kamar ze tashi gidan ta koma yana tsaye daga kan Matakalar bene Matar gidan da bata san sanda ta dawo ba na tsaye daga bakin qofarta ita kuma wata busashishiyar mace fara tas kamar Aljana ta harde hannaye tana kallon Mijin shi kuma ya kalli Umaimah data fito ta tsaya tana kallonsu gaba daya
"Kin gama Baby" ya fada yana mata wannan murmushin nasa data tsana a yanzu seta daga masa kai ta fara tafiya hanyar kitchen din tana cewa
"Saura pepper soup din bari na dakko"

"Kan kutumar uban nan Kabiru, kitchen dina kace ta shiga tayi maka girki ko Yaya" Abida ta fada har sannan tana tsaye a bakin qofarta, Umaimah ta waiwaya ta kalleta sau daya ta qarasa shigewa kitchen din, shi kuwa kan Dining ya wuce abinsa ya zauna yana duba abubuwan data ajiye ta fito ta bowl gadan gadan Abida tayi kanta ta kauce mata saboda abinda ke hannunta da zafi bata ma zata da niyya tayi kan nata ba seda taga ta sake durfafota babu bata lokaci ta dauke Umaiman da mari abinda ya sakata sakin kwanon naman ya fadi qasa ya fashe ya watsar musu a qafafu musammab Abidan dan a kan qafarta ma ya fadi ta fasa ihu tana cewa
"Kika qona ni, wlh bazan yarda ba se kin gane kurenki yau a gidan nan" Marin da Kb ya kwasheta dashi ya sakat sakin Umaimah babu shiri se kuma ta juya kansa ta shiga zaginsa kamar bama gujiya Abu kamar wasa se gani tayi ya tube jallabiyya damben da taji labarin sunyi se gashi akan idonta kici kici suka kama kokawa ya sameta ya ringa tamola da ita yana bugawa da qasa amma saboda qarfin zuciya irin nata bakinta be mutu ba ta ringa zaginsa, ita dai taja gefe tana kallon ikon Allah, ya gama casa Abida ta bakinsa da fada kafin ya kalleta a fusace yace

"Ku gyara gurin, kuma wlh se anyi lissafi kun biyani kudina ai ke kinsan ban gaji Asara ba daga kudin namana harna plate din tunda bada kudin uban wata a cikin ku na siya ba" ya wuce fuu ya dirarwa Namansa ya hau ci Umaimah kam taga abinda ya girmi tunaninta yau, wannan bala'i har ina ko awa biyar cikakkiya batayi a gidan ba. Duk dukan dayawa matar nan ga mamakinta haka ta tashi ta dakko tsintsiya se ita kuna ta hado ruwan mopping suka gyara gurin kamar yanda yace Abidan na kuka tace
"Wlh se kin san kin qona ni kuma kinsa ya dakeni" ta shige dakinta seya kalli Umaimah data rakata da kallo yana cewa
"Zo nan sweetheart bar yar abu ta kazan uba yanda kika san Jaka in ba'a daketa ba bata gane komai, zo kici kazarki da Allah karta bata mana daren Amarcin mu dan na fara chaji kinsan hadi me kyau aka mun saboda na gurji Amarci son raina".

Badan kar itama ta karbi rabon dukan ba ta qarasa amam ta gagara cin komai se madara kofi daya itana dan ya matsa mata ne, yana tsaye ta wanke komai daya bata ta adana sauran abubuwan kafin ta shiga dakinta nan ma ya kafa ya tsare wai ta shirya su hau sama. Yanda tsarin qasan yake haka saman shima yake harda kitchen da komai dagani daman tsarin mata biyu akayi tunma daga yanda Matakalar take acan gefe za'a iya yin katanga a cireta daga falon a fasa qofa ta waje amma saboda baqar mugunta beji ze iya yin hakan ba. Ya bude mata dakinta na saman suka shiga, gadon da aka saka harya fi na Qasan kyau, babu batun sallah balle aje ka wata soyayya ko tarairayar dayace daman ya fasayi ya afka mata, ta ringa kuka kamar zata hadiyi zuciya ta mutu, shekara takwas rabonta da abun gashi a yanayin da yazo mata shiyasa taji jiki matuqa shi kuwa sambatu harda na banza fadi yake babu Asararre irin Mijin daya sakota shi kam idan da wannan dadin ko uwarsa zata kashe ai ya yafe mata baqin cikin maganganun nasa suka qara qume mata zuciya, be barymta tayi bacci ba sannan tsabar bala'i tun Asuba ya tasheta wai taje ta hada masa abin kari da wuri ze fita ta rasa me zata ce masa tafiya kanta dakyar takeyi kamar wata yarinya haka ta sakko qasan ta zauna a kitchen din ta ringa kuka na rashin mafita.

Ta dumama masa Ragowar Namansa ta dafa Tea harta gama komai ta ajiye bataji motsin matar gidan ba jikinta yayi rau da zazzabi tana gama ajewa ta shige daki ta kwanta se ganin mutum tayi akanta wai ze qara na safe ba yanda ta iya haka yayi mata yanda yaga dama ya tashi ya fita, ta tuna zamanin da ana tarairayarta ana mata soyayya me kashe zuciya amma seta ga dama take yarda dashi se gashi daha daren jiya zuwa yau ta dandana kudarta a gun wanda ta tabbata idan ta masa gardama se an hada da tiyata za'a gyarata dan a haka ma ji take kamar ta samu matsala. Daze fita ya leqa daki ya ajiye mata dubu biyu kudin cefane, ta rasa abin cewa jin yana fada mata abinda zata dafa kuma za'a kai masa kasuwa qarfe dayan rana ake zuwa daukar Abincin ita dai ta amsa masa da toh tana addu'a a ranta Allah ya kawo mata dauki yana fita baccin wahala ya yi awon gaba da ita.

Saukar sanyi kamar na ruwa ruwa taji a jikinta cikin baccin, tayi juyi tana tunanin ko mafarki ne dan a zahiri babu abinda ze kawo ruwa dakin saboda na farko ba lokacin damuna bane kuma ko hakanne a qasa take ba sama ba balle ace Silin ne yake yoyo dukda ma POP ne dasu, jin fa da gaske ruwan yake zubowa dan gaba daya jikinta ya jiqe yasa ta miqe da sauri tana dube dube, hancinta ya shaqo mata warin wani abu kamar fetur, bata qarasa tunanin ba ta miqe da qarfin gaske ta bude qofa saboda hango Abida da tayi tsaye a jikin window da Ashana a hannunta tana qoqarin qyastawa tana fita daga dakin kuwa ta cilla Ashanar taje wuta ta kama dakin balbal ko ina. Yanda kasan wadda aka jonawa lantarki haka jikinta ya ringa rawa ta fice daga falon sukaci karo da Abidar na shigowa ita kuma
Chapter 265 · 0% Book details