← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 267

Sashe 98

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi bazan yarda ba, na rantse da Allah seka san ka dakeni se an bimun haqqina a kurkuku zaka qare rayuwarka shegu jinin masifa jinin bala'i yayan Karuwa" Umaimah ta fada cikin Kuka se ya sake zabura zeyi kanta Maman ta shiga tsakani tana cewa
"Na haneka Isma'il duk abinda tayi mana Hadiza taja, da bata fita tayi abinda takeyi ba babu wanda ya isa ya zo ya zage mu amma shikenan ita ta ja mana" Maman ta qarasa tana fashewa da kuka

"Wallahi idan bata fita daga gidan ba sena Halakata sedai duk abinda za'ayi mun ayi" Isma'il din ya sake zabura Maman ta tare shi tana kuka ta juya kan Umaimah data gama tsorata tace
"Ki tafi baiwar Allah ki fita dan Allah kodan cikin jikinki karki sake jaza manata wata Masifar" bata ma qarasa ba Umaimah ta kwashi qafafunta daman tun sanda ya mareta ta cire takalma haka ta fita daga gidan kamar wadda aka harbo Salman na hangota ya taso daga majalisar daya zauna cikin tashin hankali ya shiga tambayarta meya faru. Bata amsa shi ba ta shige mota, seda suka fita daga layin ta sake fashewa da wani kuka cikin ihu tace

"Wallahi tallahi bazan yarda ba, qanwarsa tabi mun Miji sannan yazo ya dake ni na rantse da Allah se nayi qararsa se an bi mun haqqina" Kuka takeyi kamar zata qarar da Hawayenta shidai Salman yama rasa abinyi. Fuskarta ta kumbura suntum ga jini faca faca akai, so yake ya tambayeta gida zasu ko Asibiti amma yana tsoron karta huce a kansa dan haka ya kama hanyar gida kawai.

Motar su Umaimah na fita daga layin Adaidaita ya dire Hadiza, tun daga soro ta fara jiyo Kukan Mahaifiyarta ga Muryar Yaya Isma'il yana maimaita "kiyi haquri Mama kar kiyi mata baki"
Gabanta ya yanke ya fadi, yau kuma wane sabon tashin hankalin Khausar ta hada mata? Take ta tuna da abinda ta gaya mata dazu da safe

"Kin dauka na qyaleki ne ko to ba haka bane na barku ne se kun sakan kance kafin na sake kunno muku da wani sabon tashin hankalin. Keda kwanciyar hankali a rayuwarki Hadiza se ranar da na samu cikar burina da kika dade kina wargaza mun, na dade ina dakon wannan lokacin, kuma yanzu na samu wadda zata aiwatar mun da komai ta daidaita rayuwarki hankali kwance".

Gabanta ya yanke ya fadi ta shiga karanto duk addu'ar data zo bakinta, kasa shiga gidan tayi ta tsaya a Soron, tsoron abinda zata tarar ya cika mata zuciya amma idan bata shiga ba ina zataje? Zata qara wa kanta wani laifi da zargi a zuciyar Maman ne dan ko a yanzun tunda ta taho cikin taraddadi take dan ta zarta lokacin tasowarta daga aiki saboda wani case da sukaje kashewa a wani gida.

Shahada kawai tayi ta shiga gidan da Sallama, Mama da Isma'il suka dago a tare suka kalleta ba tareda sun amsa mata ba. Jiki a sanyaye ta qarasa gabansu ta durqusa kan guiwoyinta bakinta na rawa ta bude da niyyar magana Isma'il ya daka mata wata tsawa yana cewa
"Wacece waccen kika janyo tazo taci mutunchin mahaifiyar, Matar waye a cikin Yan iskan da kike bi" ya qarasa a tsawace se tayi saurin ja da baya tana girgiza kanta ya taso daga gaban Maman ya biyota yana cewa

"Ba magana nake miki ba Matar waye waccen"
"Wallahi ban santa ba Yaya, shigowata kenan banga kowa a qofar gida ba" ta fada a gigice ganin yana nufota fuskarsa babu rahama
"Matar Khalil, haka naji ta ambaci sunansa" Mama ta fada daga inda take se Hadiza tayi sak a fili ta maimaita
"Khalil kuma, me matarsa zatazo yi a godan nan?"

"Ubanki tazoyi, wato da nace ki rabu dashi ba auranki zeyi ba ashe baki barshi ba kuna ci gaba da yawon shashancinku ko? To a kanki zan huce zagin da tazo tayiwa Mahaifiyarmu har cikin gida" Isma'il ya fada kafin ta yi yunqurin tashi ya kai mata qafa ta koma ta zauna tareda fashewa da kuka

"Ka barta Isma'il duniya ce idan bataji maganar mu ba zataji tata" Mama ta fada cikin kuka itama seya juya ya fice daga gidan yana huci kamar sabon zaki, da ace zoo sake ganin yarinyar nan seya mata dukan mutuwa sedai duk uban da ze faru ya faru. Hadiza kuwa yana fita ta rarrafa gaban Mama tana cewa

"Wallahi Allah shine shaidata Mama ban taba aikata duk abinda kike zargina dashi ba Khausar bata ni takeyi a gurinki ko yanzu ita ta turo wannan matar saboda kafin yanzu ma taso ta hada mana wata qullin Allah yafi qarfinta shine ta sake qulla wani, amma wallahi Mama bana tareda Khalil, na rabu dashi tun sanda kuka umarce ni wallahi sharrin Khausar ne ita take hada komai"

"Ki tashi ki bani guri Hadiza tun kafin kisa zuciya ta debeni na furta miki abinda bazaki so ba" Maman ta fada seta miqe tsam ta wuce daki tana ci gaba da kukan da yake nuna quncin da zuciyarta take ciki. Me tayiwa Khausar a rayuwa da take saka mata da haka?
A iya saninta tsakaninsu babu komai se Alkhairi, qawarta ce tare duk sukayi fadi tashin rayuwa tundaga secondary har Jami'a zuwa yanzu da suke aiki guri daya a duk tunaninta bata hango wani abu data tabayiwa Khausar da har zata nemi ramuwarsa yanzu ba.

Wayarta ta ciro a jaka ta shiga neman layin Khalil amma kamar koda yaushe bata shiga, dabarar yi masa magana a WhatsApp tazo mata se tayi saurin kunna Data, da lambarta da take WhatsApp kan abinda ya shafi aiki tayi masa magana cikin Sa'a yana Online.
"Matarka tazo gidan mu yau, me ya kawota?" Ta tura masa ta zauna zaman jira shiru shiru har kusan minti Ashirin be duba ba dukda har sannan yana Online din se kawai ta ajiye wayar jiki a sanyaya ta fita tayo Alwala. Ta dade tana kaiwa Allah kukanta akan ya wanketa a gurin Mama ya kuma tonawa duk me nufinta da sharri Asiri.

Umaimah.
Hijabin kanta taja ta rufe fuskarta ta shiga gidan, Mama da Anty harda sauran yaran na tsaye cirko cirko a tsakar gida tana shiga Mama tace
"Ahaf me na gaya miki yawonta ta tafi gashi nan ta dawo duk kun tada hankulanku a banza" ita dai bata saurara na ta shige daki, kai tsaye bandaki ta shiga ta cire Hijabin jikinta ta tsaya gaban mudubi tana qarewa fuskarta data canza kamanni tashi daya kallo. Kuka ta sake fashewa dashi idonta kansa radadi yakeyi mata musamman bangaren da ya mareta bangaren ya kumbura suntum idon yayi ciki.

Seda tasha kukan ta sannan ta kunna ruwa ta fara wanke fuskar, ganin bazata fishsheta ba ya sakata fita ta window ta kwalawa Salma kira tace ta dora mata ruwan wanka ta koma kan Gado ta zauna tana ci gaba da share Hawaye zuciyarta ta ayyana matakai sunfi dubu da zata dauka akan Hadiza da Ahalinta amma duk wanda ta hasaso se taga ai yayi kadan akan abinda suka mata. Ta bibiyar mata Miji kuma taje jin ba'asi wanta ya daketa wallahi basu isa ba.

Ummu-salma ta kawo mata Ruwan ta tsaya tana kallonta ta falla mata harara tareda daka mata tsawa ta fita daga dakin da sauri
"Munafuka" ta fada tana sakin tsaki kafin ta tashi dakyar ta shige bandakin tayi wanka. Sosai ta gasa jikinta da fuskarta da ruwan ta kuma samu sauqin kumburin amma fa ba duka ba ta fito ta saka doguwar Riga ta tada sallar Magriba da Isha.

Ummu-Salma na fita jiki na rawa ta tafi dakin Mama, a can ta tarar da Salman da shima shigowarsa kenan dan ya koma ya shawo Man da dazu be samu zuwa ba ganin Maman suna magana yasa ta juya seta dakatar da ita tace
"Salma ya akayi?"
"Am bari naje Mama ku gama se na dawo" ta fada tana juyawa saboda hararar da Salman din yake aika mata. Yasan sarai munafunci ta kawo dan ita haka take duk wani tsegumi na gidan zakajishi a bakinta.

"Zonan" Mama ta sake fada seta shiga tana rarraba ido Mama ta sake cewa ya akayi?"
"Daman, daman na kaiwa Yaya Umaimah ruwan wanka ne shine naga fuskarta ta kumbura sosai kamar ko faduwa tayi inaga ko Kuka tayi" ta fada tana satar kallon Salman se Mama ta daga mata hannu alamar taje ta kuwa fita da sauri kafin ta juya kan Salman tace

"Zaka fadamun inda kukaje ko se na hada dakai duka naci ubanku"
"Nidai Mama wallahi a waje muka hadu tace nazo na kaita Asibiti, seda muka dauki hanya tace Na'ibawa zamuje kuma koda mukaje a waje na tsaya ta shiga wani gida ban kuma san abinda tayi ba ta fito a yanda kuka ganta muka taho bata ce mun komai ba har muka zo gida" Salman ya fadi iya gaskiyar abinda ya sani. Mama dake kallonsa ta sauke ajiyar zuciya tace

"Shikenan tashi kaje Allah ya rufa asiri" ya miqe yana cewa
"Amma dan Allah Mama kar kice mata na gaya miki komai, kinsan Halin Yah Umaimah seta huce a kaina"
"Kaje abunka" Maman ta sake fada daga nan tayi shiru ta zubawa Tv ido dukda ba kallon abinda ake yi a ciki takeyi ba illah kogin tunani data tafi.

Umaimah ko ranar ko abincin dare bata fito taci ba kuma babu wanda yayi mata tayi haka ta kwanta seda cikin dare taji Yunwa na neman ranta kafin ta sanqami Burodi da ta kada madara da Milo a ruwan sanyi tasha, washe gari kuwa da wurwuri tun farar ta fita da kanta ta dora ruwan Wanka ta zuba wani a falask da zata sha shayi ta qule a daki. Batason a tuhumeta, kuma yanzu duk wanda yaga fuskarta seya tambayi meya faru.
Chapter 98 · 0% Book details