← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 267

Sashe 10

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wani ne, a makaranta ta taba ganinsa, shine yanzu suka hadu a Lagos kuma wai tana son sa auransa zatayi" ta qarasa tana fashewa da sabon kuka kalmar auran data fada tana mata ciwo.

Mama da taji bacin rai ya mata dirar mikiya saboda ko kusa kalaman ta babu na hankali a ciki bata ma fahimci me take nufi ba, daga Nabila taga wani tana so zata aure shi se ya zama dalilin da zata ri ga wa mutane irin wannan Haukan a gida, cikin kaushin murya tace mata

"Kinsan ni ba sa'ar wasan ki bace da zaki zauna kina gaya mun shirme, zaki fada mun dalilin kukan ko sena saba miki yanzun nan"

"Wallahi Mama gaskiya na fada miki, wai son sa take yi ni Kuma bana so, akan me duk mazan duniya zata ce shi take so? Wallahi baze aure ta ba sedai ta tafi can ta samu wani"

"Saboda uwarsa ce ke ko ubansa? Meye ma hadinki dashi da shiga sharafin rayuwarsa?" Mamanta sake fada cikin bacin rai kamar zata kai mata duka, se Umaimah ta miqe tana ci gaba da kukan tace

"Bani da hadi dashi amma wallahi baze aureta ba sedai ya tafi can ya nemi wata matar badai ita ba, haka kawai ya aure ta na ringa ganin shine mijinta ai bazey...." Dukan da Mama ta kaiwa bakinta yasa tayi shiru, tsawa ta daka mata tana nuna mata hanya tace "fita daga nan fitinanniyar yarinya da bata qaunar a zauna lafiya. Tsabar neman masifa ina ruwanki da sabgar ta? Kiji da kanki mana ko kuwa baqin ciki kike mata ta samu miji ke kina zaune kin rasa?
To kici gaba karki fasa daga mana hankali a gidan nan dan ubanki idan kika kaini bango ni kaina bansan abinda zan miki ba Umaimah".

Fada sosai Mama ta ringayi dan abin ba qaramin qona mata rai yayi ba, tama kasa gane kan dalilin wannan rashin hankali amma shikenna zatayi maganinta ne.

Umaimah kuwa har dare tana ta ciwon rai, idan abin ya ciwo ta ta zura kanta cikin pillow ta fasa ihu dan Mama ta ce wallahi ta sake jin muryarta seta mata dukan mutuwa a gidan, tasan kuma zata aikata dan haka ta qule a daki tasha kukanta ita kadai, tambayar da takeyiwa kanta data rasa amsa shine wai duk wannan abin da takeyi a wanne dalili me?
Meye hadinta da Khalil din da har taje jin wannan zazzafan Kishin akansa? Ko kuwa kishin nata ya burunqasa ne ya zama akan kowa da komai ma yinsa take? Toh ita dai koma yaya ne tana kishin *Khalil*, kishi me tsanani da bata zaton ta taba yiwa wata halitta shi.

Washe garin ranar data fita aiki ta nemi qaramar waya ta dora layinta akai tunda waccen ta tashi daga aiki. Messages din Nabila ne suka ringa shigowa na martani akan abinda Umaiman ta fada mata, ta kuma sake jaddada mata se tayi soyayya da Khalil, "Idan ma sonsa kike sedai kuwa Son nan ya kashe ki dan wannan karon yafi qarfin ki, kina ji kina gani zamuyi aure sedai ki hadiyi zuciya ta mutu shashasha mara hankali" Message din qarshe kenan na Nabila daya shigo wayar

Yanda kasan zatayi aman wuta saboda bacin rai haka ta shiga neman Layin Nabilan amma yaqi shiga alamar tayi blocking di ta kenan, kiran ta mayar kan Fauziyya ita din ma yaqi shiga, "bakin su daya kenan?" Ta ayyana a zuciyarta. Kwafa tayi idanunta suka kada sukayi jajir ta shiga turawa da Nabilan saqo kamar haka

"Ko a mafarki kika ganki tare da Khalil ki tabbatar da kin fara irga kwanakin da suka rage miki a duniya dan ni Umaimah se nayi Ajalinki, idan kuma kina ganin wasa ne kuma kin cika mara kunya ki bari mu hadu" ta tura mata.
Ajiye wayar tayi ta hade hannu biyu tareda dora qafa daya kan daya tana girgizawa, jiran Amsar Nabila take amma har aka kwashe kusan awa biyu bata yo reply ba, excuse ta dauka akan bata da lafiya ta tattara kayan ta ta tafi gida lokacin tashin su beyi ba dan ba zata iya ci gaba da zama a gurin.

Seda ta kwashe sati tana jinyar zuciyarta akan kishin wanda bema san tana yi ba, Alwashi kala kala taci akan haduwarsu da Nabilan duk randa Allah yasa sukayi ido hudu zasu kwashi yan Kallo kuwa.

QARSHEN QAWANCEN UMAIMAH DA NABILA.

Watan kusan biyu kenan da faruwar wancan Al'amarin, zuciyarta tayi sanyi hankalin ta ya dawo jikinta har tana jin haushin kanta akan abinda ta aikata. Ita da kanta ta yarda da shirmen da tayi be kamata ba kuma akan wanda be ma san tana yi ba ita a yanzu bata tsammanin ma idan ta ganshi zata gane fuskarsa sabon tsahon lokacin data dauka bata ganshi ba.

Tana so ta nemi Nabila ta bata haquri amma wata zuciyar da take saka ta aikata mugun abun ta hanata, gaya mata take ai ba laifi tayi ba kuma ita Nabilan ita ya kamata ta fara neman ta ta bata haquri sannan su shirya da wannan ta shashantar da maganar ta fita akanta.

Tayi sabon saurayi a gurin aikinsu, Balarabe Isha, yana aiki a ma'aikatar da take bautar qasa bangaren Finance. Ba yaro bane a qalla zeyi shekara Arba'in sun kuma samu kyakykyawar Fahimta dashi dan har yana zuwa gida hira gurinta sun ma fara shirye shiryen saka manya a maganar.
A yanda ya gaya mata Matarsa ce ta rasu yana kuma da yara hudu, dukda yace matar ta rasu amma hakan be hana baqin kishinta motsawa akan Matar da bata ma duniyar gaba daya ba, Sumayya sunanta wannan dalili yasa ta debi karan tsana ta dora akan duk wata me suna Sumayyan.

Ko a hanya aka kira sunan in sha Allahu seta bankawa me sunan Harara tayi tsaki. Sauqin da aka samu Balarabe Isah na matuqar qoqari gurin kiyaye duk abinda ze motsa mata da Kishin nata dan yana matuqar sonta da gaske.

Ranar wata Juma'a bayan sun taso daga aiki ya dakkota ze kawo ta gida, suna tafe suna hirar su gwanin dadi dan sosai Balarabe yake ririta Umaimah duk wani abu da ze sosa ranta baya yinsa. Suna tafe sun shiga layinsu kenan aka kirashi a waya da yake wayar na ajiye a tsakiyarsu ne karaf Umaimah taga sunan me kiran 'Wife'.

Wani qululu daya taso mata ta hadiye ta kalli Balarabe da yayi tsilli tsilli da ido kamar wanda aka qure tace "ka daga mana ba kiranka ake ba" ta fada a dake, sosai take kokawa da abinda yake taso mata, so take ta koyi haquri da dauke kan da kullum ake ce mata bata dashi.

Shiru yayi yana aikin rarraba ido ga wayar se qara take dan kiran na katsea wani ya sake shigowa, Tsawa da daka masa akan ya dauki wayar kamar wani danta dan ta kasa riqe bacin ranta, kai Dole ma taci kutumar uban mutumin nan dan ya goge mata hadda iya hadda. Ya yaudareta yace mata matarsa ta mutu  nufinsa se ta aureshi sannan zataje ta tarar da wata kome? Ai kuwa da a ranar daga shi har matar sedai suyi kwanan barzahu sedai duk yanda zaayi da ita ayi.

Daga inda take tana iya jiyo muryar matar se shagwaba take masa akan tana jiransa fa yazo ya kaita gidan biki ana rana bazata iya fita ta hau Napep ba, Allah sarki Balarabe zufa yake sharewa kota ina yanda kasan wanda ya zauna akan kunama, magana yake so yayi amma ya kasa se kawai ya kashe wayar ya ajiye yana kallon Umaimah data tsura masa ido kamar me nazarin ta inda zata shaqeshi ta aika shi lahira.

"Kace mun ta mutu, yanzu daga lahirar ta kiraka kenan?" Ta tambaye shi ido ta akan sa, Balarabe ya hadiye miyau qut saboda yanda tayi bala'in yi masa kwarjini nan ya shiga laluban kalaman da ze kare kansa dasu, dakyar ya iya cewa

"Dagaske nake Matata Sumayya ta rasu shekaru uku kenan yanzu, bayan rasuwarta da shekara daya akayi mun madadi da qanwarta da suke uba daya Surayya dukda bana sonta amma haka na karba ko dan saboda Yarana da banida me riqemun su saboda Mahaifiyata ta tsufa bazata iya kula dasu ba, amma ki yarda dani badan ina sonta na aure ba, nayi ne kawai saboda samun mafita, kuma yanzu a shirye nake dana rabu da ita saboda ke"

"Sedai ka saketa ka auri uwarka Balarabe, kuma yanda ka cuceni ka bata mun lokaci ka yaudareni kaima Allah yasa ayiwa yarka, wallahi ko kallon sani ka sakeyi mun se na maka rashin mutunchin da bazaka manta dani ba" ta fada cikin Fushi kafin ta bude motar ta fice, badan tana tsoron karta tijara shi a wajen a jiyota daga cikin gida ranta ya baci ba da wallahi seta masa rashin mutunchin da har ya mutu baze manta da ita ba.

Haka ta shige gida sukuku babu wanda yasan abi da ya faru tasha kukanta a daki washe gari tayi qaryar bata da lafiya dan haka bataje aiki ba.

Kiran gaggawa ta samu daga makaranta akan wasu takaddu basu cika ba na credentials dinta, dole ranar litinin ta debi original din duk wata takadda data san zaa buqata a makaranta ta tafi. Seda ta gama duk abinda zatayi a Academic Office har zata fice daga makarantar tace bari ta leqa Office din Sir Nasir su gaisa saboda anyi zaman mutunchi dashi.

Tun daga bakin qofa tutarensa yayi mata sallama, daga ciki take jiyo muryarsa yanayiwa Nasir din bayani akan abinda bata san ko meye ba. "Kinji Husky voice dinsa Umaimah" Kalaman Nabila suka dawo mata, lokaci daya taji ranta ya baci kamar ta juya se kuma ta tura qofar office din nan rai a hade kamar wadda ta kawo saqon mutuwa.

Nasir da Khalil suka juyo a tare suka zuba mata ido, Nasir ya saki murmushi yace "wata sabon gani, Hajiya Umaimah ce yau a office din mu bismillah shigo mana".

Qarasa shiga ciki tayi ba tareda ta kalle su ba tayi musu kudin goro ta gaishe su, haka kawai take jin haushin Khalil din da bema san abinda take ba se faman doka mata murmushi yakeyi.
Chapter 10 · 0% Book details