← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 251 OF 267

Sashe 251

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Haka sukayi ta jajanta maganar har suka isa gidan Mama Hauwa ita dinma kamar ta goya Mama da Anty, yanda kasan akwai wata sanayya ta sosai tsakaninsu haka ta tarbesu basu jima sosai ba anan suka sube musu kayan barkar da Hajiya tace a tafi dasu can, Mama ta ringa godiya kamar me, a gidansuka bar Hajiya dan Salman ne ya kaisu ita zata jira Driver ya maidata gida suka tafi da santin kirkin Maman harda yayanta da suka tarar a gidan.

Da suka koma gidama wuni sukayi hirar fitar tasu, Umaimah nata zirga zirgarta tsakanin daki da tsakar gidan tana aiki duk abinda suke fada a kunnuwanta, idan tace batajin zafi duk sanda aka ambaci Matar Khalil tayi qarya amma babu yanda ta iya, Khalil ya zama tarihi a rayuwarta wanda ita tayiwa kanta silar rasashi ta sani kuma zata qare rayuqarta cikin nadamar abinda ta aikata ma kanta.

Wata uku da suka biyo baya yayi dadai da cikar Umaimah shekara biyar cif a cikin gidan ba tareda ta leqa koda qofar gidansu ba. Ita badan taji suna fada bama ta manta ba kuma ta damu data fitan ba to ina ma zataje? Wa take dashi da zata gurinsa yan uwanta ne kuma suna haduwa a gida a kaf qawayen nata data daukaka sama da komai babu wadda ta waiwayeta, har gara kwanaki Nuratu take ce mata ta hadu da Rufaida taje dubiya Asibinsu harta tambayeta, a lokacin murmushi kawai tayi duniya tayi mata karatu da yawa shiyasa sam bata damu ba da watsar da itan da sukayi ba, daman Mu'amalar da ba'a qullata domin Allah ai ba zata dore ba.

Tana kwance a dakinta sakamakon ciwon Mara data tashi dashi ranar saboda shirin zuwan baqonta aikin gidan ma Abin kari kadai ta iya hadawa Abba dakansa yace ta bari saboda yanda fuskarta ta nuna bata jin dadin. Tana kwancen ta jiyo sallamar Anty Hafsa da Maman Asad, bata iya tashi ba saboda yanda mararta ta daure mata tana jiyo hirarrakinsu a tsakar gida kafin suka shiga bangaren Abba dan yana gida. Sun jima acan dan har bacci ya fara daukarta taji muryar Maman Asad akanta bayan ta dana mata dukan daya farkar da ita tana cewa

"Yau halin ya motsa kenan, kina jinmu kika lafe a daki to se ki tashi dan wake nake sha'awa yau ga gari nazo dashi ki jefamun idan nayi da kaina bazan iya ci ba". Ta tashi tana yatsina fuska saboda yanda Cikinta yake karta mata Anty Hafsa kuwa cari ta shigayiwa Hajiyayyen tana cewa
"Ni ba cewa kikayi kinyi auta ba Hajiyayye? Asad fa Ya shiga Jami'a ki rufa masa asiri haka karku zo kuna jera Jego da matarsa"
Hajiyayye ta zauna gefen katifar Umaimah tana cewa
"Kai Yaya toh nawa ma Asad din yake Ashirin da daya fa, kuma wlh ni nayi niyya daga Afifa nayi auta Babansu yace ban isa ba tunda na hanashi qara aure sena haifo wanda yayi niyyar samun qari, ai shi yanzu hudu yake jira na qaro su zama goma nace wannan dinma Astagfirullah tsautsayine ina haifeshi ca zanyi su juya mahaifar Allah sa musu Albarka" suka saka dariya ita da Anty Hafsan Umaimah dai tana ta faman yatsina da gyara zama Anty Hafsa ta kalleta tace

"Qalau kiketa yatsina ke kadai, seta yunqura saboda jin kamar abu na zubo mata tace
"Marara ke ciwo"
"Aiko gashi nan kin bata jikinki, dan iskanci da a haka kike zaune kina period babu pad?" Maman Asad ta fada ita dai ta tattare rigarta ta wuce gaban Sif ta dauki Zani da panta kafin ta janyo qaramar Jakar da take zuba Yankunan da take amfani dasu saboda gudun datti ko qura ya tabasu ta dauki wanda zatayi amfani ta mayar ta rufe ta shige bandaki duk akan idon Maman Asad da Anty Hafsa. Jikinsu yayi sanyi qalau, Anty Hafsa ta tashi ta dauko jakar ta bude taga Tsummokaran da yawa ta kalli Hajiyayye tana cewa
"Yanzu da tsumma take amfani saboda Allah a gidan nan?"

Maman Asad ta sauke ajiyar zuciya ta miqe ta fice daga dakin itama ta maida mata da jakar tabi bayanta, a falo suka tarar da Mama na duba wasu Atamfofi da zata fitar duk suka zauna a sanyaye ta kallesu tana cewa
"Lafiya dai?"
"Babu komai" Maman Asa tayi saurin fada seta miqe ta dauki jakarta tana cewa
"Ina zuwa bari na karbo abu a bakin titi" ta fice.
Bata jima ba ta dawo da Babbar Leda ta shiga dakin Umaiman lokaci har tayi wanka ta shirya tana shan ruwan zafi, ta ajiye mata ledar tana cewa
"Gashi nan".
Umaimah ta kalli ledar ta kalli Maman Asad din seta ajiye kofin hannunta ta karba tana cewa
"Nagode, Allah saka da Alkhairi ya bar zumunchi"
"Amin" ta amsa mata kafin ta juya tavar dakin tausayin qanwar tata yana kamata.

Akan gado ta zazzage kayan, saitin man shafawa da sabulu ta gani Wanda ko ba'a fada ba masu tsada ne sanann zasu gyara fata, ga turaruka bodyspray, bodysplas da perfume harda oil Shampoo da condioner, Sabulan wanki da Omo Powder lip gloss, Harda su Eyeliner da Mascara ga Pad ta Virony me 32 guda hudu. Hawaye taji ya zubo mata data rasa na menene, ta sharesu kafin ta tattara kayan ta mayar cikin ledar ta zari Pad daya ta wuce bandaki, sedata gyara jikinta kafin ta dan fesa turare ta dauki ledar ta fita dakin Mama. A gabanta ta ajiye mata ledar tana cewa
"Maman Asad ce ta siyo mun"
"Allah ya saka mata da Alkhairi ya qara muku zumunchi" Maman ta fada ba tareda ta bude ledar ba, Anty Hafsa ta bude jakarta ta zaro dubu uku ta miqa mata tana cewa
"Wata yayi nisa idan munyi Albashi zan miki aike" ta karba tana godiya kafin ta miqe ta mayar da kayan.

Danwaken ta dora mata dan taji dama dama tayishi da dan yawa ko wani zeyi sha'awa aiko har Abba da ze fita sallar La'asar yaga tanayi yace zeci dan haka ta zuba masa ta kai masa bayan ya dawo. Se Magriba su Hajiyayye suka bar gidan, suna zaune da Mama bayan sallar isha suna kallo take ce mata
"Baki gaji da zaman gidan nan ba haka Umaimah? Ya kamata ki ringa fita kina ganin gari zaki rage wannan damuwar datake tsomareki ai".
Shiru tayi dan bata san me zata cewa Maman ba, ta fita kuma da izinin wa? Kuma ma ina zataje ita gaba daya ma bata sha'awar fitar, haka nan jikinta yake bata zamanta a gidan ya fiye mata Alkhairi yanzu tasan da yawa sun manta da ita duk ranar data fita aka fara ganinta kuwa labari ne ze dawo sabo, wanda bema san anyi ba yanzun ze sani.

Ganin tayi shiru yasa itama Maman bata sake ce mata komai ba, seda aka yi sati biyu a tsakani ranar Asabar bayan sun taso daga Islamiyyar da suke zuwa ita da Anty Umaimah na girki take ce mata
"An fara siyar da form na daukar sababbin dalibai, kiyiwa Abbanku magana a karbo miki ki ringa zuwa tunda wannan baqin ya fara washewa zaman ya isa haka"
Kallon kanta tayi, dagaskiyar Maman tunda ta fara wanka da Sabulu me kyau ta shafa mai me kyau ta washe, wannan uban baqin da tayi fatarta ta bushe har waskane tayi duk ya goge dukda bata koma Asalin kalarta na amma ta fara dawowa hayyacinta. Cikin In ina take cewa Maman
"Mama nayi masa magana kuma? Kin manta yace karna fita idan na gaya masa ze barni?"

"Ki tambaye shi mana idan ya hana srki haqura ki zauna kici gaba da girka tukunya" Maman ta bata amsa. Ta ringa juya maganar a ranta, ita kanta zata so ta koma Islamiyyar to amma bata so ta lalata shirin da suka fara da Abban in so samu ne zata cigaba da zama harse randa shi da kansa yace ta fita tunda ai yana sane bawai ya manta bane. Se washe gari Lahadi da Mama ta sake mata maganar cikin fushi tana cewa
"Dama ba karatun Addinin kikie so ba bayan harda rashin ratsa miki jiki da beyi ha yasa kika ringa tambele kina hauka a baya to se ki zauna ki qare rayuwarki babu wan babu qanin, keba aure ba keba neman ilimi ba bazan sake miki magana ba tunda baji kikeyi ba, dama na manta ne ai hali zanen dutse".

A daren ta samu Abba da zancen son shiga Islamiyyar, jikinta na rawa ga maganganun Mama ga tsoron yanda ze karbi maganar tata, ta sauke ajiyar zuciya ganin ya zaro dubu uku ya bata yana cewa
"Gashi nan ki bawa Antyn ku kamar haka tace mun kudin Hijabi da suka dinka kwanaki, idan na fita anjima zan karbo miki form din a Masallacin gurin Malam Babba, sauran Litattafai kuma seki duba anan duk ina dasu suna a nan suka samu". Ta ringa jera masa godiya kamar zatayi kuka kafin ta tashi har takai bakin qofa ya tsayar da ita, dakinsa ya fito ya miqa mata Wayarta da har ta manta da kalarta ma ita wlh.
"Gata nan, se ki siyi layi ki dora dan wancan qila sun siyar da number ko kinyi Welcome back bazeyi aiki ba".
Chapter 251 · 0% Book details