← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 258 OF 267

Sashe 258

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kanta ta gayawa Maman Asad haduwarta da Abdulwahab din, ta ringa murna ita ta gayawa sauran da Mama gaba daya suka tsaya akan shawarar kar Umaiman ta kaishi gida kai tsaye. Ta kaishi gidan Baba Abdullahi, shawarar Maman Asad din take Nuratu tace babu wannan maganar dan ta tabbata kawunda kansa ze fara watsa gayyar dan yayi rantsuwa duk wanda yazo neman auranta seya gaya masa komai dan baza'a hada baki dashi a cuci mutum ba haka kawai taje ta illatashi. Nuratu tace mata ta kaishi gidan Maman Asad din, suyi zancen su a can idan sun daidaita sun gama shirya komai sannan se yaje ya gaida Abba da yan uwansa base an gansu tare ba bare aje a lalata maganar tun kafin taje ko ina. Da wannan maganar sukayi Na'am, zuwansa na farko ta kaishi gidan a can sukayi zancensu tayi matuqar qoqari gurin sake bayyana masa wacece ita da Mugun HALIN KISHInta da yayi sanadiyyar mutuwar auranta amma seta gagara fada masa aika aikar da tayiwa Khalil da irin diban Albarka da tayiwa surukarta, ai Allah ma bayason wanda yake aikata laifi sannan ya ringa fada cikin Alfahari.

Abdulwahab yace yaji ya gani ya kuma yarda tunda har ta iya fada da kanta to dagaske take da cewar ta canza,ya sake jadda mata da cewar yana tsananin sonta kuma yasan bazata samu matsala da matarsa ba dan tana da haquri da kawaici ya tabbatar daga bangaren ta dai ba za'a taba samun wata matsala ba sannan kuma ba gida daya ma ze ajiye su ba, ita Umaiman ze tafi Abuja da ita saboda ita Hauwa tace tafi son zaman Kano yana daga babban dalilin daya saka yake son qara aure dan ya gaji da zama haka a can kuma zaman nasa yafi yawa a Abujan akan Kano ba kuma yaso ya shiga haqqinta yayi mata dolen komawa can shiyasa ze auri wadda zata yarda ta bishi a karan kanta.

Daga nan soyayya ta falle a tsakaninsu, dukda bawai tana Jinsa har cikin zuciyarta bane amma ta karbeshi kuma zata aureshi a rashin wanda zuciyartata take da muradi. Zuwan da yayi yau din kamar yanda suka tsara zeje ya gaida su Abba sannan qarshen sati iyayensa zasuje nema masa auranta, duk wasu shirye shirye sunyi nisa hatta da matarsa ya hadasu a waya sun gaisa haka Mamansa da qanwarsa guda daya ita kam tuni suka qulla zumunchi tana yawan kiran Umaiman itace dai bata shige mata.

Suna tafe yana janta da hirarsa ta barkwanci kamar yanda ya saba amma gaba daya yaga yanayinta ba kamar kullum ba dan haka yayi shiru ya qara musu sautin kidan dake tashi a radion motar, dama tunda ta fito yaga idonta ya tambayeta meya sameta tace masa zazzabi takeyi shiyasa fuskarta da idonta suka kumbura, yace su je Asibiti taqi, a cewarta taje an bata magunguna suna gida. Haka suka qarasa gidan, ta rigada ta sanar dasu zuwansa dan haka sun shirya. A falon Abba aka saukeshi, suka gaisa a mutunce Anty ta gabatar masa da abinda aka tanadar masa, tambaya daya biyu Abba ya gano Mahaifinsa Alhaji Sale sun zauna a kasuwa tare Rumfuna uku ne tsakaninsu, baban nasa ya gamu da paralysis kusan shekara goma yanzu abinda yasa suka bayar da hayar rumfar kenan dan babu me kula da gurin yaron shagunan nasa suka ringa Almundahana su kuma duka yayansa aikin gwamnati sukeyi babu wanda ya maida hankali a kasuwa dan haka ya bada hayarta kawai sukayi gwanjon kayan ciki.

Hira sosai suka sha da Abban, shiya kwatanta masa wani Alhaji Zakari da yake nan qasan layinsu shima dai tate suke a Kasuwar kuma Aminin Alhaji Salen ne sosai Abdulwahab din yace tabbas ai ko jiya ma Alhaji Zakarin yaje duba Alhajin nasu, komai yazo da sauqi ma tunda abin na gida ne. Be bar gidan ba seda sukayi sallar Magriba, ya cikasu da Alkhairi Umaimah na kwance ya kirata a waya akan ze tafi. Seda ta rakashi har bakin motarsa ya tafi kafin ta koma ciki tana kallon Samarin da suka maida musu da qofar gida Majalisa duk saboda suka giftawarta ko wani yazo gurinta suyi rige rigen bata ta. Komeye ribarsu a soke aure oho.

Zuwan Abdulwahab da kwana biyu waliyyansa sukayi waya akan zasu tambaya tunda har Abba sunyi waya da Alhajin nasu an qara tantanto juna. A daren ya kira Umaimah yake ce mata ta kira Abdulwahab suje suyi duk wasu gwaje gwaje daya kamata ace anyi tun kafin magana tayi qarfi base abu yazo ba kuka ba fata ba a samu wata matsala da zata iya hana auran saboda ita AS ce. Tana barin gurinsa ta kira Abdul din, abin dariya abin haushi wai shi a shekarunsa bema san Genotype dinsa ba, koda za'a daukeshi aiki kawai zuwa yayi aka masa medical report din ba tareda an gwadashi ba ta ringa masa masifa kamar wani danta, sune suke yaqi da cin hanci da Rashawa amma suna aikatawa ya ringa dariya kawai, washe gari kuwa da sassafe yazo suka tafi Asibitin dan jirgin yamma zebi ya tafi Abuja.

Seda gabanta ya fadi da taga Asibitin da sukaje, Asibitin Dr Al'amin inda suke zuwa a gidan Khalil. Seda ya biya kudin duka gwaje gwajen da za'ayi musu, tana jinsa yana waya da wani likita da yace Abokinsa ne ya sanar masa baya Asibitin amma kafin su gama ze shigo.

A office din Abokin nasa suka zauna bayan an dauki Jininsu, Abokin ya ringa kallonta, ita dai ba ta sanshi ba dan ko lokacin da take zuwa ba zaton suntaba haduwa gaba daya ma tunda sukaje Wata Nurse daya ta gani data sani a gurin duk sun canza ma'aikata amma shi wannan se wani kallon qurilla yake mata ya tambayi sunanta kuwa yayi sau uku harda wani gayyato wani Likita wai su gaisa da Abokinsa da Amaryarsu shima ya tasata a gaba yana kallo har seda ta tsargu ta ringa duba jikinta ko akwai abinda ta saka da ya ja suke kallo ta amma taga babu, Hijab ne dogo har qasa ta dora akan doguwar Rigar Atamfar data saka qafarta ta saka safa fuskarta da hannunta ne kadai a bude to me suke kallo a jikinta? A haka dai aka kawo musu sakamakon Gwajin komai yayi daidai sukayi sallama da Dr da daya Abokin gulmar da ya kirawo suka kama hanyar gida. Seda suka tsaya yayi mata siyayya sosai dukda tace bata so ya barshi amma ya kafe har yana cewa ai yanzu ta zama responsibility dinsa dole yayi mata.

Be zauna ba yana sauketa ya tafi saboda be qarasa shirin tafiya ha kuma sun bata lokaci a Asibitin, ta shiga gida da tulin siyayyar da yayi mata da kuma sakamakon gwajin da sukayi, ta rigada ta makara itama dole ta haqura da fita aiki dan haka ta shige daki ta kwanta dan ta dan yi bacci kafin lokacin dora Abinci yayi.

Abdulwahab ya isa gidansa ya tarar da matarsa Khadija cikin damuwar da tunda ta dawo daga gidansu jiya ya ganta a ciki. Dare yayi sanda ya dakkota dan haka be tsaya ya fahinci maganar da tazo masa da itan ba. Tana zaune akam gado inda ya fita ya barta ya sake tarar da ita da alama ma kuka tayi ya matsa kusa da ita yana taba wuyanta yace
"Wai Dija baki da lafiya ne? Tun Jiya na lura dake gaba daya baki da walwala tunda kika dawo daga Sallari ko wani abun ne ya faru acan?"

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 88

A maimakon ta bashi amsa seta fashe masa da kuka tana cewa
"Nidai Abban Fahimah maganar auranka, ban hanaka ba amma dan Allah banda ita ka auri koma wacecena yarda amma banda wannan Umaiman".
Sakinta yayi ya miqe yana mata wani kallo kafin ya dauke kansa yana cewa
"Kar muyi haka dake Dija, karki lalata mana farincikin mu muna zaman lafiya kin karbi maganar nan seda abu yazo gab zaki tayar da hankali, duk wanda ma ya zigaki yace kizo ki tayar mun da hankali I'm sorry to say ke zasu cuta dan ni babu abinda ze saka na canza ra'ayi tunda tuntuni munti ta da wajewa babu yanda za'ayi yanzu kuma kizo mun da wata magana gara ma ki sanyaya zuciyarki, gobe za'a kai kudi na gaya miki kuma sati takwas za'a saka" yana gama fada ya shiga zuba kayansa a akwati ganin bata hada masa ba dan ita take shirya masa kayan.

Kuka ta ringayi duk yanda tayi qoqarin fahimtar dashi akan wacece Umaiman yayi biris yaqi fahimtarta, data ishe shi da cewar Kishine na bala'i da Umaiman yace mata ya sani, babu abinda ta boye masa kuma a hakan yaji ya gani ze aureta ya kwashi kayansa ya bar mata dakin dan gani yakeyi kawai taje gidansu ne sun zugota zata zo ta fara masa wani koke kokeb banza bayan komai da saninta kuma da yardarta yakeyi, daman yasan babu yanda za'ayi salin alin ayiwa mace kishiya ba tareda tayi tashin hankali ba. Saboda kukan nata da wuri ya bar mata gidan bayan ya jaddada mata aure babu fashi gara ma ta saki ranta taci gaba da sabgoginta kishiyar da ba gari daya ma zasu zauna ba to me ze dameta.

Ita kuwa Khadija tashin hankalin data shiga bayan jiya taje gida yayarta Ummia dake zaman gida take sake tambayarta wadda Abban Fahiman ze aura dan tunda ta gaya mata sunan Yarinyar take tunanin kamar ta santa bata haqura ba kuwa seda ta binciko inda tasan Umaiman. Ta nunawa Khadijan hotonta tace tabbas itace. A tsakar gida ta zauna ta ringa basu labarin Umaimah da tijararta tun suna poly ta santa dan sun taba hada saurayi ma a lokacin da ta gano ta hada ita da saurayin tayi musu Tijara a Lecture hall ta dire tana basu labarin Upgraded haukan Umaimah da irin ta'asar da tayi aka sakota shekara bakwai kenan tana zawarci.
Chapter 258 · 0% Book details