← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 267

Sashe 47

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanzu ita Khalil yayiwa wannan cin mutunchin se kace ya samu Dabba sannan ya tsallaketa ya barta a haka? Jan jiki ta ringayi dakyar ta samu ta sauka daga gadon ta rarrafa ta shiga bandaki, a gefen bahon wanka ta durqusa bayan ta kunna ruwa ta shiga rera kukan baqin ciki, seda ruwan ya taru ta cicciba dakyar ta shiga ciki, ta kwashe sama da awa daya tana gasa jikinta tana kuka gaba daya jin qasanta take kamar ba'a jiki ta ba kai gani take kamar ya qarata ma ai kuwa bazata yarda ba dole ta dauki mataki akai tunda akan gaskiyarta take da idonta ta ganshi da karuwar kuma tayi magana ya hakke mata kamar wata Baiwarsa Allah yana kallo kuma seya saka mata.

Sanda ta fito Khalil ya dade dayin bacci abinsa tana tafiya kamar yar kaciya ta bude ledar magungunan da aka bata ta dauki Paracetamol tasha, seda ta qara hada shayi me kauri tasha kafin ta koma kan doguwar kujerar dake dakin ta kwanta tana jin jikinta kamar ana kwankwatsata tsabar yanda ko ina ya dauki ciwo.

Da Asuba daya tashe ta dakyar ta miqe shi kuwa har yayi shirin masallaci ya fice abinsa ya barta da matsar kwalla saboda yanda jikinta ya sakeyin tsami ga azabar zafi da takeji a qasanta se kawai ta zauna a gun ta shiga rusa kuka. Seda gari yayi haske ya koma dakin har sannan zuciyarsa babu dadi, idan ya tuna kalmar karuwa da take jinginashi dashi se yaji sam Umaimah bata dace da zama matarsa ba, bata ganin mutunchinsa bata qimanta shi duk menene ya jawo hakan.

Sanda ya shiga dakin beyi niyyar kukata ba amma ganin yanda fuskarta ta canza ta kumbura ya bashi tsoro dole ya qarasa kanta yana kallonta da alama ko sallar batayi ba tana nan yanda ya barta, murya a daure yace mata

"Baki tashi kinyi sallah ba ko?"
"Bazan iya tashi ba dan Allah ka kaini Asibiti jikina, marata ko ina ciwo yake mun inaga ma mutuwa zanyi" ta fada cikin kuka, seya kama hannayenta da niyyar miqar da ita ta fasa qara saboda azabar zafin da taji, da sauri ya durqusa a gabanta yana kallon yace

"Kwanta mu gani" ya fada yana qoqarin daga dogon Hijabin jikinta, bata da qarfin hana shi ba yanda ta iya ya bude jikinta ya kunna fitilar wayarsa ya haska, saurin kawar da kai yayi wani irin tausayinta ya tsirga masa. Sosai yaji mata ciwo dukda ba likita bane shi amma yasan wannan raunin ko ba'a dinke taba dole se an mata yan dabaru zata dawo dai dai, kallonta yayi yanda ta rufe ido tana tsiyayar da hawaye bayan duk ita ta jawo komai, bata jin magana ya rasa wace irin zuciya Allah yayi mata da sam bata san daidai ba se rashinsa.

A akwatinta ya dauko doguwar riga mara nauyi ya zura mata tana kuka dukda yanda ya ringa lallaba mata jiki kamar me taba kwai ya dauketa a hannu ya fita da ita, kafin su isa Asibitin seda yaji kamar shima ya fasa kuka saboda yanda ta gigita masa kwakwalwa da kokekokenta da ya tabbatar bayah na ciwo harda na jidalinta.

Sunyi sa'ar tarar da likita macece on duty a Asibitin daya kaita jiya ta ringa surfa masa bala'i kamar zata dake shi sanda ta duba Umaiman dan ita a zatonta ma Amarya ce daren farko, Alluran rage zugi da ciwo tayi mata ta bata wani magani na shafawa tace ba se tayi mata dinki ba ta dage da shiga ruwan dumi ta kuma ringa cin Nama me romo da fruits gurin ze warke kar kuma ta kuskura ta koma masa se taji jikinta ya dawo daidai so samu ta dauki kamar wata biyu tayi jinya shidai Khalil jinsu kawai yake tana wa Umaimah huduba a ransa yace
"Ba'a koya mata abin tsiya bama tayi inaga an bata lasisi".

Ranar haqura yayi da fita site ya kira ya bada uzurin Madam bata da lafiya, dukda be sakar mata fuska ba amma ya tsaya ya bata kulawa sosai dan motsi idan tayi seya tambayi me take so idan zata shiga bandaki kuwa daukarta yakeyi ya kaita ya kuma tsaya seya tabbatar da ta gasa jikinta kamar yanda Likita ta fada sannan ze rabu da ita.

Duk yanda Umaimah taso da ta samu kansa abin yaci tura dan ta fahimci fushin nasa me girma ne dan ba ita kadai ba ko kiransa akayi a waya daga yanda yake magana zaka fahimci yana cikin damuwa. Tayi nadamar abinda tayi ko babu komai da yanzu bata karbi sakamon wannan Azabar da take ciki ba abinda ko daren farkonta baya fuskanta ba gashi babu wannan sakin fuskar da tarairayar data saba dasu duk abinda yake mata kamar wanda akayiwa dole.

Da sukazo kwanciyar bacci ma kan kujera ya kwanta ya bar mata gadon, tayi masa magana ya mata banza seta saki kukan da dama yana maqale a wuyanta ya kuwa shareta data ishe shima ya saka Airpod ya toshe kunnensa dan kanta tayi ta gaji bacci ya kwasheta.

Khalil kuwa wani irin kallon takaici yabita dashi, a cikin halayenta yana daga abinda yake qona masa rai bata san idan tayi kuskure ta bashi haquri ba. Duk sanda abu ya hadosu sedai idan ya gaji da fushinsa ya sakko ko tayi ta rara gefe sa shagwabarta ta banza har ya sakko amma dai ace ta bude baki ta bashi haquri bata iya ba.

Shi gaba daya ya rasa ma inda ze sakata ne, bata da ladabi sam be kuma san yanda ta dauki rayuwar aure ba amma ze koya mata hankali, daga yanzu baze sake bari wata yaudararta tayi tasiri akansa ba, dole ta koyi ladabin idan ma bata dashi dan baze yarda su dora rayuwa a haka ba.

Washe gari jikin nata yayi sauqi dan haka ya fita gurin abinda ya kawo shi, honeymoon dai ya koma zamandoya da manja dan haka suka cinye kwanakin da zasuyi idan ya fice tun safe se dare ze dawo, kuma haka zaau zauna magana idan ba wadda ta zama dole ba ko tayi masa baze amsa ba. Tun Umaimah na daukar abin wasa har yazo ya fara damunta.

Koda suka dawo Kanon ma bata chanza zani ba sema qara tabarbarewa da zaman nasu yayi dan gaba daya ya fita a sabgarta takai ta kawo ko gaishe shi tayi sedai ya daga mata hannu wanda daman ba kullum ba ne take gaisuwar yanzu nema da aka shiga wannan yanayin take neman abinda ze sa suyi magana ta dage da gaisuwar.

Daman tunda suka dawo ya raba musu daki, acewarsa likita tace ta samu hutu sosai shi kuma baze iya jurewa suna kwana gado daya ba dan haka ta koma dakinta tayi jinyar, girki ma ya sauwaqe mata abin kari da kansa yake shiga kitchen ya dafa idan yaje aiki yaci na rana acan wata rana yayiwo take away idan ze dawo ko ya biya gidan Hajiyarsa yaci wadda ita a zatonta laulayinciki ne ya saka Umaiman bata iya girji dan haka idan yaje seta zubo musu ko haka kawai ma ta dafa abun kwadayi ta bawa Habiba ta kai mata.

Wasa wasa sun kwashe sati kusan uku a cikin wannan halin, tun Khalil najin wani iri akan matakin daya dauka musamman idan yaga ta zauna tayi shiru har ya zamana abin ya zamar masa jiki ya fara sabawa da rayuwarsa shi kadai.

Umaimah kuwa gaba daya ta fita hayyacinta musamman da laulayi yayi mata dirar mikiya ga rashin kulawar datake fuskanta daga bangaren Khalil gaba daya se abin ya hadu yayi mata yawa. Wauta da rashin wayo irin nata sun kasa barinta ta hango kuskurenta ballantana ta gyara sannan ta gaza gayawa kowa a nata shirmen zata iya fuskantar matsalarta ita kadai sedai abin ya zama ana bata goma biyar bata gyaru ba.

Wata safiyar Laraba ta tashi bata jin dadin jikinta, a kwanakin daman gaba daya qarfin hali kawai takeyi ita ba zazzabi ba ba wani takamaiman ciwo ba amma jikinta sam baya mata dadi se taji kamar tayita ihu ko zata ji sauqin abinda yake damunta gashi babu abokin hira ballantana ta fada masa damuwarta ya tayata koda kalamai masu dadi ne taji sanyi.

Tun asuba data idar da sallah bata koma ba saboda tana son magana da Khalil din gida take so taje dan tunda suka dawo bata fita ko ina ba. kusan kullum bata sanin fitarsa, data dan koma baccin safe sedai ta farka taga ya fita ko ta tarar da saqon kudin cefane ya ajiye mata a palour dukda itama ba girkin take ba yayime yayime kawai take taci.

Tana zaune ya fito daga dakinsa cikin shirin fita tsaf dashi kai bazakace yana da wata damuwa ba. Ta bishi da kallo dakyar ta iya tausar zuciyarta ta gaishe shi ya amsa mata a taqaice yana nufar qofa seta bi bayansa tana cewa

"Magana nake so muyi"
"Toh yanzu kuma? Gashi sauri nakeyi na kusa makara ko zaki bari sena dawo idan ba na sauri bane" ya fada yana qare mata kallo dan qarara ya hango ramar da tayi se dai ta qara haske da kyau.

Yamutsa fuska tayi tana kallon gefe tace
"Ni gidan mu nake so na tafi bani da lafiya ni kadai na san me yake damuna kar nazo na mutu a gidan nan babu wanda ya sani tunda ba'a damu dani ba"

"Me hali baze chanza ba" Khalil ya fada a zuciyarsa yana maimaita kalamanta a ransa da sam babu ladabi ko tausasawa a cikinsu a fili kuwa ya gyara tsayuwa yace mata

"Wa kika gayawa baki da lafiya kuma waye be damu dake ba?"

"Kai mana, daga fadar gaskiya gaba daya ka dena kulani ka fita harkata a gidannan sena shafe kwanaki magana bata hadamu dakai ba, nidai na gaji wallahi gida zan tafi gara naje inda ake sona ba zan zauna a inda ake zaman gaba dani ba" ta fada cikin karyewar murya tana shirin sakar masa kuka.
Chapter 47 · 0% Book details