← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 173 OF 267

Sashe 173

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yanzu Malam ya za'ayi a shawo kan matsalar nan" Safina ta fada bayan da Malam din shima ya koma ya zauna yana wani munafikin murmushi da suka rasa na menene. Carbinsa ya sake dauka yaci gaba da motsa baki Umaimah ta zura masa ido kamar me son gane abinda yake fada ya gama surutunsa ya watsa carbin yace ta dauka jiki babu laka ta dauka ta miqa masa ya karba yaci gaba da ja zuwa can ya kalleta yace
"Da akwai aikin da zamuyi wanda ze iya dakatar da auran amma fa se kin bada hadin kai tukunna"
Shiru tayi bata ce komai ba dan haka yaci gaba da cewa
"Kusan ke zakiyi aikin ma da kanki nawa kawai tallafine na makamai da zasu taimaka miki amma fa kibi a sannu".

Nan ma shirun tayi se Safina ce tace
"Zatayi duk yanda aka ce Malam babu matsala in sha Allahu". Miqewa yayi ya sake shiga dakin dazu ya gama buruntunsa ya fito da wani kwando a hannunsa. Gurin da yake zaune ya koma ya shiga ciwo fararen robobi qanana yana ware kowanne da yan uwansa seda ya gama tsaf kafin ya bude jakar dazu ya ciro wata takadda. Sticker ce a jiki ko waccean rubuta yanda ake amfani da maganin ya ringa daukar roba daddaya yana mannawa yana tarasu a gefe seda ya gama ya sake tashi ya mayarda ragowar kayan ya dawo da Allo da tawada ya zauna ya fara rubutu, befi layi biyu ba yayi ya dago yana kallonta yace
"Ya sunanki?"
"Umaimah" ta bashi amsa kamar me ciwon baki ya rubuta ya sake tambayarta sunan Mijinta ta gaya masa, seda ya gama tsaf kafin ya kwalawa Amaryarsa kira ta fito jikinta na rawa tayi musu sannu ta durqusa a gabansa, ruwa yace ta kawo a kwano bayan ta kawo ya miqawa Umaimah Allon yace ta wanke, kamar wadda yake controlling haka ta karba ta wanke ya karbi kwanon a ciki wata yar jarka ya dure rubutun ya hada cikin sauran kayan daya ware kafin ya zauna yana kallonta ya shiga daga robobin yana cewa

"Wannan ko wanne da yanda zakiyi amfani dashi a jiki ki kula, kada a samu kuskure, sannan na wannan" ya ciro wani qulli daga Aljihunsa ya miqa mata yace
"Turarene a tsakar gida ake yinsa duk kuma wanda ya shaqi hayaqin bakinsa zai rufe ruf daga fadar abinda bakyaso. Ki turarashi a inda duk wani me fada aji akan al'amarin auran yake shikenan kin gama dasu, sannan wannan" ya sake zaro wani qulli a farar leda sabanin na farko da yake a baqa ya miqa mata yana cewa
"Ki samu kan Tinkiya, Tinkiya Mace ba Rago ba kiyi farfesun sa ki zuba wannan garin maganin a ciki, duk wanda yaci zaman lafiya tsakanin keda shi har abada babu wani sabani da ze saka shiga tsakani, duk wasu dangin Miji da suka saka gaba ki dafa ki basu suci an gama magana".

Ita dai Umaimah juya abubuwan takeyi a hannunta kawai amma tunaninta yayi nisa da inda suke, 'akwai aure,akwai mutuwa ga kuma mutuwar aure duk akan wa?' Abinda take ta tunani kenan, tana ji Safina na zabga masa godiya ta bude jakarta ta ciro kudaden da sun haura dubu dari ta ajiye masa ya miqe yana ce musu suci abinci kafin su wuce sannan ya juya ya fice daga falon bayan ya sake kallon Umaiman. Ita dai bata iya shan koda ruwa ba Safina ce ta tsakuri Abincin saboda Azalzalar Umaiman suka tafi. A hanya suna tafiya Safina na sake jaddada mata da tayi amfani da Abubuwan nan kamar yanda yace

"Ki kwantar hankalinki qawata kinsan fa binciken nan nasu sau da yawa basa ganin daidai se kiji zancen wani ya shiga na wani ta yuwu can wata yayiwa Istaharar tun dazu se a akanki Labarin ya fito" Safina ta fada ganin Umaimah ta zurawa hanya ido bata magana tunda suka fito. Ita kanta ta tsorata da jin zancen mutuwa daya kawo, a iya sani ta da Malam Sha yanzu kuwa be taba fadar abu be tabbata ba (wa'iyazubillah) toh babban abin fargabar shine waye ze mutu? Sanin wannan kuma se Allah. Haka suka qarasa gidan Safinan, Umaimah ta dauki motarta dan data Safina suka fita, bata zauna ba ta wuce gida faran faran babu sallar Azahar balle La'asar duk a yawon gidan Malam ta riske su.

Sanda ta isa gida Khalil be dawo ba. Dakinta ta wuce ta adana kayan data shigo dasu kafin ta shiga bandaki tayi wanla hade da alwala har zuwa sannan kuzarin jikinta be dawo ba. Sedata rama sallolin sannan ta kulle qofar dakin da muqulli ta dauko jakarta ta zazzage kayan a kan gado. Daya bayan daya ta shiga duba su, wani a abinci wani abin sha harda na dafa shayi se nata na amfani wasu a ruwan wanka gana tsarki da hayaqi duk dai gasu nan kala kala. Zuciyarta ta kasu biyu akan amfani da kayan ko akasin haka kuma kowanne bangare ya kasa rinjayar dan uwansa dan haka ta hade kayan ta maidasu jakar gaba daya. Kallon robar rubutun daya ce ta zuba masa a ruwan sha tayi, seta dauka ta riqeta a hannunta, dakyar ta haye saman saboda nauyin da jikinta yayi kai tsaye ta wuce inda Dispenser take ta kalli ruwan da yake ciki ya wuce rabi dan haka beyi mata wahalar dagawa ba ta cire shi, rubutun ta juye a ciki, tana so ta dandana taji ko ya canza taste amma bata san na menene ba, haka ta mayar da robar kai kafin ta wuce dakin Khalil din ta shiga gyarawa.
"Shi Aikin Asiri da kike gani se kin hada da kissa yake ci da wuri" abinda Safina ta gaya mata dazu da suna hanya kenan ta kuma jaddada mata data taushi zuciyarta ta nuna komai ba komai ba kawai ta zura ido taga ikon Allah.

Tsaf ta gyara masa dakin daman falon a gyare yake ta kwalawa Ruqayya kira akan ta kawo mata garwashi. Seda ta turare dakin da hayaqin da Malam din ya bata kafin ta shiga bandaki ta kashe wutar tayi flushing gawayin da ragowar maganin kamar yanda ya fada kuwa hayaqin bashida wari ko qamshin komai, yanda kasan bata saka komai ba se dan qaurin wuta dan haka ta zuba turare a bunner ta kunna bayan ta fesa Room freshener sanna ta koma qasa. Kunun da bata sha da safe ba ta sha yanzun dukda kwata kwata bataji yunwa badamur da take ciki ta cushe mata ciki, Ruqayya na kitchen tana hada abincin dare, Tuwo takeyi da Miyar Kuka kamar yanda yake a Time Table din abinda zasu dafa. Daki ta koma ta kwanta lamo, tsoro takeji haka nan zuciyarta taqi aminta data cutar da Khalil dinta amma ya zatayi? Bata da wata mafita idan ba wannan ba da bakinsa ya tabbaatar mata da aure zeyi ya hadata da wata a cikin zuciyarsa ya kuma raba musu kansa a shimfida abinda ba zata taba lamunta ba ko bayan ranta bata fatan Khalil ya sake auran wata mace, so takeyi ya dawwa babu aure har ya tarar da ita su sake ci gaba da zama tare a Aljanna.

Wannan tunanin ya saka ta miqe, Robar abinda yace ta zuba masa a Miya ta dauka dana shayi. Suna da banbancin kala dan haka ta cire takaddar jiki ta miqe ta tafi Kitchen din. A bakin qofa suka hadu da Ruqayya da ta dakko Fulasandata zuba abincin Khalil zata kai kan Dining, Ciki Umaiman ta wuce, kaitsaye ta bude butar shayin da Ruqayyanta dora ba tareda tunanin komai ba ta zuba abinda zata zuba ta mayar ta rufe haka ta zuba na miyar shima bayan Ruwayyan ta ajiye, har zata shiga daki ta tsaya ta kwalawa Ruqayyan kira ta fito daga Kitchen din da sauri
"Gobe idan Allah ya kaimu zan aikeki Abbatuwa da Safe, karki manta da kin tashi koda ni na manta ki tunamin" ta fada mata Ruqayya ta amsa da
"Toh Hajiya" kafin ta juya ta koma Kitchen din a ranta tana tunanin me yake faruwa kuma dan tunda Umaiman ta shigo taga yanayinta ba yanda take ba.

Kwanciya tayi a dakin sanyin jikinta ya ninka na dazu, sosai take zargin kanta da rashin kyautawa amma kacokan ta dora laifin akan Khalil, shiya ja duk abinda ya sameshi shine Sila.

KHALIL
Cikin matuqar bacin rai ya kama hanyar Qunchi dan har ya manta da Anwar zasu tafi seda yaci rabin hanya sannan ya kirashi yana tambayar be fito bane har yanzu yana ta zaman jiransa. Haquri ya bawa Anwar din kan cewar yayi gaba ya taho kawai, yana ganin Kiran Humaira amma ya qi dagawa, baya so ya sauke fushin da ba nata ba akanta shiyasa kawai ya tura mata saqo cewar yana tuqi idan ya tsaya ze kirata.

Gaba daya ransa babu dadi yayi aikin daya kaishi, se yamma Lis suka gama suka kamo hanyar Kano. Anwar ne yake tuqi shi kuma yana zaune a kujerar gefe ya jinginarda kansa baya yayi shiru yana tunani. Tunani barkatai suke yawo a kansa wai har se zuwa yaushe Umaimah zatayi hankali? Ya tambayi kansa. A kullum girma suke warawa shekaru na dada yawa amma ita tamkar baya takeyi kaifin tunani da hangen nesanta yana dada raguwa Kishi ai ba hauka bane da har ze saka tayi wasa da rayuwarsu, yanzu abinda tayi dazun da ace yazo da tsautsayi ko basu mutu ba ai zasu wahala musamman ita da tak da qarin wani nauyin a jikinta amma sam ita kamar mara tunani abinda yazo mata a zuciya kadai takeyi bata hangen abinda hakan ze iya haifarwa.
Chapter 173 · 0% Book details