← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 267

Sashe 29

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Se kuma dukkan su suji tsoron Allah su zauna da junansu Amana kar wani ya cutar da dan uwansa" ta fada murya a cunkushe dan ta gaji da wadannan tambayoyin na titsiye.

"Idan har kinsan duk wadannan abubuwan da kika fada me yasa ke bakya girmamani" Khalil ya fada yana kallonta, se ta dago kanta data duqar qasa ta kalle shi itama, yar banzar zuciyar ta tana ce mata "kice saboda shi ba mijinki bane" ta kirkin kuma tana kwabarta,

"Magana nakeyi kinyi shiru, Umaimah me yasa bakya ganin qimata, kin raina ni bakinki yana iya furta mun duk kalmar data zo miki a duk sanda kika ga dama, a gabanido na kike zagina ki zagi yan uwana hakan yayi miki kama da suffar mace ta gari wadda take neman Aljannar ta a gurin Mijinta? Ko kuwa kina ganin tunda bamu rigada munyi aure ba dan haka kina da damar da zaki yi mun duk abinda kika ga dama?

Toh bari kiji, halin da kika nuna a waje shine ze bani haske akan halinki acikin gidana bayan munyi aure, tun daga waje bakya shayin ki kalli idonaki zageni Umaimah ki jefeni da kalmomi marasa dadi a haka kike tunanin zan aure ki? Ban samu kwanciyar hankali dake a waje ba sanda baki zama doke na ba taya ya zanyi tunanin samun sa bayan na kawo ki gidana?

Gaskiya Umaimah ina tsoron abinda ze faru idan har haka kike, ba kuma zan daukarwa kaina damuwa na kai cikin gidana ina sane ba, macen da bata girmamani ba a waje bana tunanin zata girmamani acikin gida bayan data gama sanin koni wanene" Khalil yayi maganar cikin daga murya da dakiya gaba daya ya chanza daga Khalil din nan me sanyi ya dawo wani daban dan.

Kallon sa ta kumayi saboda yanda taji muryarsa har tsakiyar kanta kafin ta kalli can gefe tana qoqarin hadiye maganganun dake son fitowa daga bakinta dan a yanayinfuskar sa ta tabbatar yau baze dauki raini ko kadan daga gurinta ba, abinda yafi mata sauqi ta kama kanta ta kuma gyara bakinta dan haka ta maye gurbin kalamn tsiwar tata da cewa

"Kayi haquri nasan nayi kuskure, raina ne ya baci amma in sha Allahu bazan sake ba. Zan koyi yanda zan ringa sarrafa zuciyata akan kishinka" ta qarasa maganar cikin rawar murya tana janhanci kamar me son fashewa da kuka.

"Kar kiyi mun kuka" ya fada, kamar me jira kuwa sega hawaye shaaa sun fara zubowa, ta rigada tasan weak point dinsa, baya son kukanta ko kadan shiyasa take amfani dashi gurin karya lagonsa.

"Kinga ni ba kuka nace kiyi ba magana kawai mukeyi kuma dole na nuna miki kuskurenki saboda aure zaman aure zamuyi, babu yanda za'ayi mu tafiyar da rayuwa a haka babu girmamawa a tsakaninmu, bacin rai ai ba gushewar hankali bane da zesa ki manta matsayina a gurin ki ki gaya mun duk maganar da kika ga dama" Khalilya fada cikin kwantar da murya, se ta sake fashewa da wani kukan harda sheshsheqa tace

"Toh ya kake so nayi? Duk abinda nayi kishinka ne ya saka ni ba dan bana ganin girmanka ko na raina ka ba. Ina sonka da yawa Khalil ni kaina ban san irin son da nake maka ba, idan na ganka da wata mace ji nake yi kamar na shaqe kaina shi yasa bana sanin sanda nake fada maka magana mara dadi amma ka yarda dani na fika jin daci da haushin duk wata kalma mara dadi dana gaya maka, kuma nayi maka alqawarin bazan sake ba, tun waccen ranar nayi nadamar abinda ya faru na kuma chanza.

Alqawari ne nayi maka Khalil bazaka taba nadamar aure na ba, Zaka sameni me matuqar biyayya tareda gujewa bacin ranka, zanzamar maka baiwa banida wani aiki se aiwatar da unarninka muddin be sabawa Allah ba kuma inada yaqinin bazaka taba sakani nayi abinda ya kaucewa shari'a ba, amma nima ina roqonka daka tausaya mun, kar kayi amfani da raunina akan Soyayar ka ka cutar dani.

Ina matuqar kishinka ka tayani rufe duk wata qofa da zata kawo matsala a tsakanin mu dalilin kishi ni kuma nayi maka alqawarin zame maka duk irin matar da kake so. Bazan bawa idon ka damar ganin wani abu a waje kayi sha'awa ba ni kadai na isheka Khalil zan kuma tabbatar maka da haka dan seka bigi qirji wata rana ka gayawa duniya kafi kowa yin sa'ar mata saboda ina sonka Khalil, kuma farincikin ka shine nawa" ta qarasa maganar tana saka kwayar idonta dake jiqe da hawaye cikin tasa suka yiwa juna kallon tsakiyar ido n dan lokaci kafin ta janye nata tana ci gaba da jan shashsheqar kuka.

Wani irin yarrr yaji tundaga kansa har tafinqafarsa, yanda kasan wanda aka tsoma a baho dake cike da ruwan qanqara a lokacin sanyi haka haka jikinsa ya dauki rawa seda ya hada hannayensa biyu ya rungume kansa tare da rufe idonsa yana furta "Hasbunallahu wani'imal wakeel" a zuciyarsa a hankali sanyin da yake ji ya ragu nutsuwarsa ta fara dawowa, be dena ambaton Allah ba seda yaji komai ya daidaitar masa ya bude idanunsa da suka kada sukayi jaa lokaci daya kamar wanda aka watsawa yaji ya kalli Umaimah da kanta ke sunkuye har sannan tana kuka qasa qasa.

"Umaimah!" Ya kira sunanta cikin wani irin sauti, bata amsa ba illah sagowa da tayi ta kalle shi ta sake mayar da kanta qasan.
"Look at me Umaimah, look directly in to my eyes" ya sake fada cikin shaqaqqiyar murya yanda kasan shine yayi kukan ba ita ba.

Jiki a sanyaye ta dago ta kalle shi idanunsu suka sarqe. Ji takeyi tamkar yana cake mata ido da wani abu amma ta kasa janye idonta kamar yanda shima ya saka mata ido yana kallonta, sun kwashe kusan minti biyar a haka kafin Khalil ya bude baki yace

"Ina sonki, and i will prove it to you ranar da kika zama mallakina, zan riritaki zan baki gatan daya dace dake a matsayin ki na mace da Allah yayi muku daraja ta daban, and I am giving you this assurance, ni KHALIL ke kadai kin isheni a rayuwata Umaimah. Idan har kika ga wata mace bayan ke a duniyata to ki tabbata qaddara ce wadda babu wanda ya isa ya kauce mata kuma idan haka ta faru ina fatan dani dake zamu rungumeta da hannu biyu, amma ki sani baki da ta biyu a zuciyata duk kuma wani abu da ze zo toh bayan UMAIMATAH NE".

Yanda kasan ta taka rawar murna haka taji sanda yace ita kadaice a duniyarsa amma qarashen kalaman nasa suka datse murnar tata, wato yana fata kenanwata rana wata ta shigo rayuwarsu? Ita kuwa zata dawwa ma tana roqon Allah da karya nuna mata wannnan rana da ranta, dan kuwa bata san yaya zatayi ba. Tabbas idan bata kashe ko wacece ta shiga rayuwar Khalil dinta ba toh ita zata kashe kanta ta huta da baqin ciki.

Hannunsa daya kai fuskarta ya dawo da ita daga tunanin data tafi,
"Tunanin me kikeyi Amaryata?" Ya fada yana mata murmushi, seta mayar masa da martanin murmushin, a ranta tana jin dadin halin Khalil na rashin ruqo, yanzu sun gama wannan maganar kenan har abada sedai idan ita ta sake tayar da ita.

"Ke kikayi wannan cake din, yayi dadi sosai" ya fada bayan daya gutsiri cupcake din, seta girgiza kai tace

"Aa, amma zan tambayi Maman Asad inda ta siyo naje a koyamun tunda kana so"

"Thats my babe" ya fada yana kashe mata ido, kafin yaci gaba da cewa
"An kawo kaya dazu ko? I'm sorry i was supposed to tell you ban samu dama ba, koda yake laifin kine da kika shareni kwana da yawa bayand kika gama yimun barazana. Ni ai ban san yar sara suka bace ke se ranar" ya qarasa yana mata dariya, seta shagwabe fuska tace

"In dai akan ka ne ka kirani yar Daba ma, kuma ni ba qin kiranka nayi ba tun ranar bani da lafiya seda na kwanta a Asibiti kwana hudu".

Ayya sorry my princess shiyasa she nayita jina se a hankali, kinsan sati dayan nan was the longest week in my whole life saboda rashin ganinki da banayi, kawai na ringa rayuwa ne amma ni kaina nasan nayi loosing focus, God i can't imagine life without this my little troublesome lover" ya fada yana jan kumatunta irin yanda akeyiwa yara wasa.

Dariya suka saka gaba daya, daidai nan Yaya Hajiyayye ta shigo gidan. Seda ta gama daidaita parking ta fito daga motar dan yaran tuni sukayi gurin Khalil da gudu me aikinta kuma ta shige da Baby Ummu-salma.
A mutunce suka gaisa tana tsokanarsa Ango Ango se sunkuyar da kai yakeyi, ta faki idonsa ta gallawa Umaimah data qunshe fuska Harara dan taga aika aikar da tayi mata, daman tasan za'a runa ai kuwa seta biya kudinsa dan Mijinta ta siyowa shine zata kwashe ta bawa nata Mijin.

Yaya Hajiyayyen na wuce wa basu dade ba sukayi sallama bayan daya ce tayi lissafin abinda take da buqata na hidimar biki ta tura masa, shidai a bangarensa reception kawai zeyi bayan an daura aure tace masa ita ba abinda zatayi tasan dai Mama zatayi Kamu da Mothers eve, yace dai taje tayi tunani daga nan suka rabu akan idan sun shawarta abinda zasuyin zata gaya masa, ta raka shi har bakin Gate ya wuce gida.

A cikin gidan tana shiga kuwa Maman Asad ta tsareta seda tayi mata transfer kudin cake dinta cif sannan ta kyaketa bayan ta kwashe ragowar wai zasuci ita da yaranta gobe a kawowa Dadyn wani, ko a jikin Umaimah dan ita zuwan Khalil da daidaitawar su yau ya wanke mata komai. Haka tayi baccin farin ciki bayan da suka sha waya suka kuma kashe junansu da kalaman qauna masu tsuma zuciya.

Washe gari Asubanci tayi ta bar gidan tunda ta gama abinda ya kawota tao zaman me zatayi dan haka bata bari ma Maman Asad din ta tashi daga bacci ba ta fece dan karta tsayar da ita tace ta tayata girkin tarbar Mijinta.
Bayan ta isa gida ta kwanta ramuwar baccin safen kenan seda Imran autan Anty ya tadata wai taje Antyn tana kiranta.
Chapter 29 · 0% Book details