← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 235 OF 267

Sashe 235

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ya zakiyi kike tambayata, saboda sunce karki sake gaidasu se kiji ki dena gaishe shin saboda tsabar rashin tunani irin naki ai a lokacin nema ya kamata ki daura dambar gaidasun da duk wata kyautatawa da kika san zata saka zuciyoyinsu yin sanyi su sauka da fushin da sukeyi da ke amma se kika zauna kina jira su gaji da fushin su sakko su su nemi kushirya kome ashe ma ke kika haife su basu suka haifeki ba" Ruma ta fada fusace se Umaimah tayo saurin cewa
"Ba haka bane wlh..."
"Na sanki Umaimah babu abinda zaki gayamun wanda ba gaskiya ba na yarda idan na rantse bazanyi kaffara ba muguwar zuciyarki har a yanzu tana ayyana miki cewar abinda kikayi daidaine shiyasa kika qi Sasantawa da Mahaifanki ki nemi gafarar su to tun wuri idan kin shirya gamawa da duniya lafiya Umaimah ki san abinda kikeyi ki kuma maida Al'amuranki ga Allah shine kadai Mafita a gareki yanzu".

Maganganu masu shiga jiki Ruman ta ringayi mata ta fito mata da laifukanta ta kuma bata hanyoyin da zata gyara har wata nutsuwa Umaiman taji tana sakko mata saboda ta samu ta amayar da abinda yake cinta kuma an bata mafita in sha Allahu kuma zatayi amfano da duk abinda Ruman ta fada mata. Nisawa Ruma tayi ta gyara zamanta tace
"Toh yanzu ina yaranki, suna tare dake ko ya riqesu?"

"Suna gurinsa, tunda muka rabu ma se jiya aka taba kawo su kuma basu dade ba matarsa tazo ta daukesu" Umaimah data rafka tagumi ta bata amsa se Ruma tayi wani murmushi me ciwo tace
"Kayya kin gani ko? Duk haukanki da tashin hankalinki babu abinda ya hana gashi nan tana zaune dashi ke kuma kina gida cikin qunci da takura meye ribar abinda kikayi? Ai wlh Umaimah da ace kinsan me kikeyi tundaga sanda aka ce miki an rigada an daura aure ya kamatavki zubda makamanki saboda kinsan cewar yaqin ya wuce kan Khalil Ubangiji yayi ikonsa idan kika matsa abinda bazaki so ba ze faru gashi kuwa"

"Harta haihufa Ruma" Umaiman ta sake fada kamar zatayi kuka wani mugun kishin Khalil din yana taso mata amma tayi qoqari ta hadiye is Ruma ta tafa hannu tace
"Kinji ba, to qila da baki bar gidan bama ki mutu tunda baki yarda da qaddara ba Rabon sa na jikinta da a titi kike so ya haifi dan" se kuma ta kama baki tace
"Ikon Allah bashi da haqqinki nakasar da kika so ja masa Allah beyi ba".

Yanda kasan ta cakawa Umaiman Mashi a qirji haka taji, Khalil ya samu lafiya kenan yanawa yarinyar nan kalar abinda yake mata shiyasa harta kasa ganeta tayi qiba tayi fresh jiki duk madara kawai ta fashe da kuka ba tareda ta shirya ba tunanin Khalil na Mu'amala da Humaira kamar ze zautata
"Tab toh Allah ya kawo miki dauki Umaimah gashi can ana kiran sallah bari mu tashi nasan da an idar Barr ze dawo" Ruma ta fada tana yunqurawa Umaimah ta rage qarfin kukanta tana cewa
"Baki fada mun yanda naki al'amuran suka kasance ba se kawai ganinki nayi da ciki bayan tsahon lokaci"
"Wannan labarin wata rana ne Umaimah se hankali ya kwanta kedai kiyi hanzarin gyara alaqarki kafin lokaci ya qure miki" daga haka ta shige bandaki ta barta tana jan Majina.

A dakin sukayi sallah har bayan sun idar seda Ruma ta sake yi mata tunatarwa akan yawan ibadah,
"Ki daure Umaimah cikin dare idan kin juya ko raka'a biyu ce kiyi ki kaiwa Allah kukanki yafi kwanciyar da kikeyi alhalin ba bacci kike ba bakinki karya zauna shiru daga ambaton Allah kiyawaita yin tasbihi da istigfari sannanki rage damuwa dan babu abinda zata miki sedai ta haifar miki da ciwo ta lalata miki jiki ko a yanzu baki ga yanda kika koma ba kamar me ciwo duk ina gayunki Umaimah kalli fatarki yanda ta yamushe kamar ta tsohuwa"

"Uhm Ruma kenan har wani maganar gayu kikeyi keda kike cikin nutsuwar zuciyata data jiki ke kike buqatar kwalliya wa zanwa" Umaimah ta fada tana janye tagumi kafin Ruman ta bata amsa wayarta ta shiga qara ta daga ganin Mijinta ne yake kira ya sanar mata yana waje seta miqe bayan ta kashe wayar tana gyara gyalenta Umaiman ta kalleta tace
"Badai tafiya zakiyi ba?"
"Tafiya zanyi mana zamuyi waya idan kuma na samu dama gobe ko jibi zan dawo" ta bata amsa se Umaiman ta miqe tsaye itama tana cewa
"Na fada miki banida waya yanzu, dan Allah ki dawo Ruma wlh bakiji yanda naji dadin zuwan ki ba da zan samu ace kullum kizo dana rage kewa"

Dariya Ruma tayi tana cewa
"Lallai ko kiyi qoqari ki gyara kura kurenki zakiji dadin rayuwarki Umaimah dan rabuwarki da Khalil bashine yake nufin rayuwarki tazo qarshe ba kici gaba da Addu'a in sha Allahu zaki samu madadinsa a gaba" daga haka tayi waje Umaiman ta bita a baya kamar kazar da kwai ya fashewa gaba daya bata ji dadin kalaman Ruman na qarshe ba yanda ta nuna bata da sha'awar ta koma gidan Khalil kenan. A tsakar gidan suka tarar da Mama tana qarasa girki dare Anty na zaune daga bakin qofarta suna hira se sannan Ruma ta gaida Anty ta amsa da fara'a Mama tace
"Kin fito Ruma?"
"Na fito Mama ya dawo zamu wuce ne" ta bata amsa tana sunkuyarda kai, taso a daki suka tarar da Maman tayi mata magana amma babu komai zata dawo daga haka ta yi musu sallama Umaimah ta rakata bakin qofar shigowa kamar karta barta ta tafi yau din jinta tayi kamar sallah ta samu abokin hira.

Seda taji Ruman ta saki Get kafin ta dawo, gurin Mama ta wuce kanta a qasa tace ta kawo ta qarasa girkin
"Jeki abinki na gama kwashewa kawai zanyi" Maman ta fada jin haka seta wuce ta fito da kular da ake zubawa Maman ta sauke tukunyar Tuwon taja gabanta ta shiga kwashewa a leda ganin haka yasa Maman ta sakar mata ta wuce dakin Abba dan ta gyara Umaimah taci gaba da kwasar tuwon maganganun Ruma na dawo mata sedata gama ta tattara tukunyar da sauran kayan gurin kafin ta koma daki dan an kira sallar Isha. Tana nan zaune taji shigowar Abba ta miqe a hankali ta fita kamar munafuka ta rabe daga bakin qofa tayi masa sannu da zuwa worn nta na bugawa da tsoron meze biyo baya amma ga mamakin ta se ji tayi ya amsa fuska a sake har yana tambayarta gida kafin ya shige ciki abinsa.
Ta sauke ajiyar zuciye me nauyi ta koma ciki a ranta tana ayyana komai zezo da sauqi da yardar Allah.

Washe gari da wuri ta kama ayyukanta kamar yanda ya zame mata jiki qarfe bakwai ta gama komai saboda ranar makaranta ce ta shirya abin Karin Abba a Try yanda akeyi ta ajiye a bakin qofarsa dan kullum haka takeyi idan ya gama ma a nan za'a aje kwanukan ta dauko. Daki ta koma ganin Mama bata fito ba tayi wanka ta zura rigarta ba tareda ta shafa mai ba dan ya qare kuma wata beyi qarshe ba balle ta samu ta siya a pocket money ta. Seda taji motsin Mama suna gaisawa da Anty kafin ta fita, ta gaida Antyn da take mata wani gani gani yanzu a tata fahimtar tunda ta aurar da Ummu-Salma ta samu gidan daula ta ke wani buda hanci itama ta aurar da ya a ganin Umaimah fa. Seda ta jira Mama ta shiga falonta kafin ta bita jiki babu kwari a bakin qofa ta dakatar da ita ganin tana shirin shiga tace
"Lafiya?" Seta diririce, dakyar ta iya cewa
"Aa daman gaisheki zanyi" se maganar tata ma ta bawa Maman dariya ta murmusa tace
"Toh yau kuma ina a tsakar gida muka saba gaisawa yau ta musamman ce da se kin biyoni har daki?" Raurau tayi da ido hawaye na shirin kwace mata daman tasan fushin Abba me sauqi ne na Maman tafi tsoro, durqusawa tayi daga bakin qofar da take murya na rawa tace
"Dan girman Allah Mama kiyafe mun ki barni na ringa shigowa dakinki ina gaisheki" ta qarasa kuka na kwace mata Mama ta juya ciki abinta tana cewa
Chapter 235 · 0% Book details