← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 267

Sashe 76

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar Juma'a misalin qarfe sha daya tana zaune a palour taci kwalliya da wani Lace fari ta kashe dauri yanda kasan me zuwa wani taron biki, wayarta na hannunta ta jona sabon ringlight din da ta siyo jiya saboda daukar videon Tiktok. Tsabar zaman banza da rashin abinyi da takeyi ya saka ta fara sha'awar Matan dake video suna dorawa a Tiktok din, daman Rufaida ta dade tanayi ta na kuma tayi mata maganar itama ta fara dan ita a yanzu ta kai yawan followers da har Tiktok sun fara biyanta saboda irin badalar da takeyi da sunan comedy marasa tunanin irinta suna kalla sunayi mata like wasu su zageta, bata mutunta kanta matsayinta na musulma mace ba kuma matar aure take banzatar da kanta a Social media.

Waqa ta kunna bayan data gama saita wayar ta ajiye nan ta shiga bin waqar daga zaunen da take tana dan juya jiki wayar na dauka. Waqoqi ta ringa sakawa abinta tana yin videos wasu a zaune wasu a tsaye wani ma jikin mudubi ta tafi ta dauka seda ta gaji ta koma ta zauna bayan ta kashe Ringling din ta shiga duba videos din tana editing. Hankalinta yayi nisa a abinda takeyi sam bataji sanda aka bude Get ba se sallamar sa da taji a tsakiyar kanta.

KHALIL
Ranar Alhamis aka fitar da sunan sabon manajan bangaren da aka dorashi ruqon kwarya dan haka a ranar ya tattara ya damqa masa duk wasu abu na office din da suke hannunsa musamman daya kasance ya kammala duk wata kwangila da aka fara se sababbi wanda suka fara proposing shiyasa be sha wahala ba gurin damqa masa komai a daren kuma ya hada kayansa yayi booking jirgi zuwa kano dan ya gaji da zaman garin matuqa sati kusan bakwai ba wasa ba yayi kewar Kano kullum Hajiya cikin mitar sun tafi sunyi zamansu takeyi dan duk a lissafinta da Umaimah suka tafi, kuma da yake itama yar gaske ce tunda ta fahimci tunanin Hajiyar ko kiran ta tayi a waya suka gaisa bata taba nuna mata basa taren ba.

Tara da yan mintuna ya sauka a Kano, ya taho da wasu takaddu dole ya wuce office kai tsaye danya bayar dasu kafin ya wuce gida tunda ranar aiki ce, be bata lokaci ba yana kai takaddun inda ya dace ya kama hanyar gidan. Sanda ya isa ya rigada yasan babu kowa a gidan shiyasa be kashe motar ba ya fita ya bude Get sedai mamaki ya kamashi jin daddadan qamshin turaren wuta yana tashi a tsakar gidan, ya kalli gurin dakyau yaga ko ina fes da alama ba'a jima da wankewa bama dan gurin be qarasa bushewa ba kuma ba lokacin damuna bane ballantana yace ruwa akayi seya tabe baki ya juya ya koma mota ya shigo da ita ciki.

Jakar computer sa kadai ya dauka dan ya gaji bacci kawai yake so yayi yanzu kafin lokacin sallar juma'a yayi yana so kuma yaje gidansu Hadiza, so yake ya shammaceta dan be sanar da ita dawowarsa ba.

Muqulli ya zura a qofar yaqi shiga seya zare dan alama sun nuna akwai wani ta ciki kenan ya murda handle din ya tura qofar hancinsa na sake shaqar qamshin turaren wutar da Hauwa ta cika gidan dashi. Da mamaki yake kallonta, tana zaune gaba daya hankalinta yana kan wayar da take dannawa fuskarta a washe tayi wani sanyayyan kyau seya ga ta qara masa haske da qiba irinta wanda yake cikin kwanciyar hankali.

Dauke idonsa yayi daga kanta ganin yana neman shagala da kallonta ya ci gaba da takawa cikin palour bakinsa dauke da sallama daidai nan ta dago a dan firgice ta kalle shi, wannan murmushin nata na yaudara ta sakar kafin ta ajiye wayar hannunta ta miqe tsaye ta nufeshi cikin takun jan hankali tana qarasawa kusa dashi kafin yayi wani abu se jinta yayi a jikinsa ta ta zagaye wuyansa da hannu biyu ta sajar masa peck akan lips dinsa kafin tayi far da idonta tace
"Sannu da zuwa honey".

Sakin baki yayi kawai yana kallonta tsabar mamakin abinda tayi, babu ko digon damuwa ko tashin hankalin daya zata zatayi masa idan sun hadu dukda be saka ran ganinta a gidan kuna a yanzu ba ko dab saboda haukan data so ta farayi masa waya ranar nan hakanan babu ko digon damuwa ko nadama akan laifin da tayi masa se zallar rainin hankali da iya bariki take nuna masa lallai Umaimah ta wuce duk inda yake tsammaninta.
Hannu ya saka ya janye ta daga jikinsa saboda yanda turarukan datayi amfani dasu da yanda take goga masa jikinta suke neman yin tasiri akansa ya shige daki ba tayi fushiba ta bishi tana masa sannu da zuwa.

Sake kama rigar da yake qoqarin cirewa tayi seya dago ya kalleta ido cikin ido yace
"No thank you i can help my self" fuska a daure haka muryarsa babu wasa a cikinta, a maimakon yaga tayi fushi sema wani munafukin murmushi ta saki tana cewa
"Toh bari na hada maka ruwan wanka sena sama maka abinda zakaji dukda dawowan naka babu sanarwa aida na hada maka special" ta wuce bandakin tana kada jiki.

Binta yayi da kallo kamar wani soko, yanda take abubuwanta yanda kasan sunyi rabuwar mutunci ya dawo daga office ko wata gajeriyar tafiya, kai shi baya jin ma ya taba samun tarba irin haka a gurinta fuska a sake, gida qalqal ita kanta tsaf se an samu wani abun be cika ba.
Yana tsaye ya gagara ci gaba da cire kayan ta fito daga Toilet din, ido daya ta kashe masa tare da hura masa kiss kafin ta saka kai ta fice daga dakin seda ya saki ajiyar zuciyar dabe san sanda tazo masa ba yaci gaba da cire kayansa a ransa yana jimamin hali irin na Umaimah. Ya fuskanci ta rigada ta san lagonsa akanta shi yasa take masa iskanci yanda ranta ya bata idab kuwa hakane wannan karon shima ze zama namiji baze sake bari ta mayar dashi Soko ta qibin umarninsa sannan tazo tana masa kissa da kisisina tayi zaton ze sakko ba saboda ga Jarababbe.

Wankan ya shiga yayi, a kan bedside drawer ya tarar da Butar shayi da cup se madarar ruwa wadda yake amfani da ita se qaramin Bowl data zubo wani abu kamar cookies kamar cake. Seda ya sakawa qofar dakin key kafin ya shafa mai a jikinsa sama sama ya koma gefen gadon ya tsiyaya ruwan shayin a kofi se tashin qamshi yakeyi irin yanda yake so amma idan ba ita tayi ra'ayi ba farin ruwan fanfo zata tafasa ta zuba masa a flask ta bakinta da fada can ya gane.

Tas ya cinye cookies din ya sha shayin ya ture kayan gefe ya haye gado, se a sannan ya kunna wayarsa da tunda ze hau jirgi ya kasheta. Saqon Hadiza ne ya fara shiga na barka da Safiya sena Juma'a ya biyo bayansa, yayi murmushi yana mayar mata da amsa kafin ya danna mata kira dan yana so yaji muryarta. Seda gabansa ya fadi sanda yaji motsin Umaimah tana taba qofar, Hadiza ta daga wayar kamar wani munafuki yayi qasa da murya yace mata
"Sorry Dija zan kiraki" kafin tace wani abu ya kashe wayar.

Daga kan gadon cikin daure murya yace
"Ya akayi ne" qirjinsa na dukan saba'in saba'in saboda tsoron ko Umaimah taji maganar da yayi a waya, Umaimah dake tsaye a waje ta harari qofar cikin kissa tace
"Ban gane ya akayi ba mace zata shiga dakin Mijinta ka ringa tambayarta ya akayi wai meye ma dalilin rufe qofar da key?"
"Bacci zanyi bana son damuwa please, idan qarfe daya tayi ban tashi ba ki tasheni" ya bata amsa kafin yaja bargo ya rufe jikinsa ya juya baya kamar tana cikin dakin.

Baqinciki ya shaqe wuyan Umaimah ita Khalil ze wukaqanta dan ma yaga tana ta tasa ko, wallahi badan da abinda take nema ba ko kallo be isheta ba tunda ai ita ya kamata tayi fushi ya tafi yawonsa ya barta kusan wata biyu kamar wata gantalalliya. Kwafa tayi ta koma cikin palour ta zauna, tayi niyyar har girki tayi masa amma yayiwa qaton kansa badai yaci na rana ba sedai da dare idan taga dama tayi.

Khalil kuwa yanajin ta matsa daga qofar ya sake kiran Hadiza suka shiga hira dukda a hankali yake maganar kuma cikin takatsantsan ita kanta Hadiza seda ta tambayeshi lafiya tajishi haka yace mata babu komai, sunyi kusan minti goma kafin sukayi sallama saboda tace masa ta tashi aiki zata wuce gida ya ajiye wayar babu dadewa bacci ya dauke shi bayan ya saita alerm dan ya san indai Umaimah ce sedai ya kwana yana baccin nan ba tashinsa zatayi ba musamman da ya rufe mata qofa.

Tana nan zaune tana danne danne a waya har Azahar tayi, bataji motsin fitowar se tambayar ta da yayi ina Mu'ayyad, a firgice ta dago kamar mara gaskiya, yana tsaye akanta yayi wanka ya saka manyan kaya Light blue din shadda data karbeshi sosai ya kafa hula daman Khalil ba daga baya ba gurin iya saka hula, haka nan taji wani abu ya soketa, ba yanzu ya fara saka manyan kaya ba musamman da yake yau juma'a amma haka kawai taji kwalliyar tasa ta yau tayi yawa ga uban turare daya fesa seta tura baki tana kallonsa tace

"Gaskiya kaje ka canza kaya kayi kyau da yawa ba zaka fita a haka ba"
"Se kizo ki cire mun ai, ina tambayarko kina yi mun wani shirme" ya bata amsa yana kallonta. Gefe ta kalla ta tunzura baki tace
"Ai shikenan, amma wallahi duk wadda ta kalleka Allah ya isa".
Chapter 76 · 0% Book details