← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 227 OF 267

Sashe 227

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Ya akayi?"
"Dama tambaya zanyi me za'a dafa!" Ta fada muryarta na rawa se Maman ta nuna mata wani farin bokiti me dan girma tace
"Ga Awara nan ita za'a soya se ki damawa Abbanku Kunun gyada shikenan". Da 'toh' ta amsa ta shiga falon a darare ta Kinkimi bokitin zata fita Anty Laure tace
"Wai ni Umaimah takaba kikeyi ko qaqa? Tun dawowarki gidan nan kike fama da wadannan shegun rigunan bana jin sun kai goma Zawarci hauka ne ko kuwa Qazantar ce har yau baki dena ba duk ina uban jibgin suturunki da bazaki ringa sakawa?"

Seta rasa amsar da zata bata ta kalli Mama kawai dan dai tun dawowarta gidan kayan datayi amfani dasu zaman Asibiti ne taketa dirza basu fi goman ba ta bakin Anty Laure ita kuma ganin ba inda taken zuwa yasa bata damu da bin ba'asin kayanta ba, Mama ce ta nunawa Anty Laure Dayan dakin dake cikin Falon ta tace
"Suna ciki Akwati sun kusa Ashirin ni har Mamakin uban suturun da suka debo da sunan nata na ringayi dan da tana gidan nasa ma ba sawa takeyi ba. Tun tana Gadon Asibiti su Nuratu suka debo mata kayan katako ne Alhaji yace a barsu tunda daman shi yayi"

"Aa shi kuma Yaya wace irin magana ce haka kamar yaya shi yayi? Ai ba haka nan aka kaita babu komai ba babu abinda ba'a sai mata ba na aure canji ya mata kuma ko bataje da komai ba wadannan da ya matan sun zama nata ai kyutace saboda baqin hali shine kuma da akace ya barsu ya riqe din" Anty Laure ta fada se Mama ta muskuta tace
"Aa fa ba laifinsu bane babu yanda basuyi ba akan a diba Alhaji yace Aa yace ya tattara ya siyar ya rage Asarorin data masa dan ashe har Mota me tsada yarinyar nan ta fasa masa bamu sani ba se daga baya"
"Kuma haka ne fa ai shikenan kinga kinyi zaman shekara bakwai a banza baki tsira da komai ba randa kika tashi yin aure kina ruwa dan mun rigada mun miki na fari ke ba sana'a ba ke ba aiki ba toh Allah ya rufa Asiri".

Ita dai Umaimah tuni ta fice daga tsakar gida take jiyo sababin Anty laure, ta rafka tagumi wato duk lokacin nan an debo mata kayanta amma babu Wanda yace mata gasu ta tambaya kuma cibi ya zama qari saboda tsabar an tsaneta kayan dakin ma bar masa akayi ai shikenan. Haka ta shiga yanka Awara ta gama ta jere duk kayan da zatayi Amfani dasu cikinta se kiran ciroma yake amma ta qudurce ko zata yi me ba zata sake cin shinkafar ba, ta dazu ma yunwa ce babu yanda zatayi ga yar kwaskwarimar da Ummu-Salma tayi mata toh yanzu saboda mugunta suna dawowa Anty ta aiketa wai gidan Yayarta tasan kuma dan karta tayata aikine ai Allahya kaimu gobe da yake girkin Antyn sedai ta fito tayi abinta dan bayi zatayi ba.

Tana shirin Hura wuta Yasir ya shigo da barkono da alama aikensa Akayi ya siyo ya ajiye mata harda kayan Maggi ta kalle shi ta kalli barkonon, ko zamanin yarinta bata daka dan da tayi hannu ta zeyi kanti seta dade tana jinyarsa kafin ya warke ko tuqin tuwo tayi me yawa hala yake mata shine yanzu za'a kawo mata wani yaji kusan kwano guda ta daka me za'ayi dashi? Yasir kuwa yana aje mata ya wuce dakin Mama ya fito da ledar citta da Tafarnuwa ya ajiye mata yana cewa
"Mama tace ko raba barkonon biyu kuma kar ki saka farin Maggi iya dunqule da gishiri za'a saka". Seta wai waya ta kalli dakunan kafin tayi qasa da murya tace

"Kana ji ka dauka ka kaiwa Maman Nana kace nace ta bayar a daka yanzu ka kawo mun in ka dawo zan baka dari biyar maza ka boye kar ka bari wani ya gani" jin zata bashi cin hanci ya tattari kayan ya fice dasu Umaimah kuma ta shiga qoqarin kunna wuta a ranta tana ayyana kota kunna Gas tunda Abban baya nan sega Yasir ya dawo da barkono ya dire mata yana cewa
"Abba yace a dawo dashi". Bata iya amsashi ba saboda takaici, kenan Abban na waje. Seta miqe da sauri ganin An kawo wuta, a Blander ta hada ta warwatsa musu yajin tana kuma sane da Abban yafi son dakan hannu dan Maman Asad na siyar da su Spices da Yaji idan ta kawo niqan Inji baya ci sedai a daka masa a turmi.

Ba yanda ta iya ta shiga suyar Awara, tana cikin tsame kaskon farko Salman da Abokansa biyu suka shigo gidan da sallama. Ahmad daya daga cikinsu irin mutanen nan ne nan masu shegiyar zolaya ya kalli Umaimah harda bude baki irin na mamakin nan yace
"Kai Salman dama Yah Umaimah na siyar da Awara shine baka gaya mana munzo mun yi mata cikini ki ba? Dan Allah kalli yankan manya manya ba irin na Rabin bakin layi ba Yah Umaimah a samun ta dari a kyauta mun saboda naje majalisa nayi miki tallah" tsabar wulaqanci Salman da dayan yaron suka kalleta suka tuntsure da dariya harda duqawa qasa saboda yanda bilhaqqi tayi kama da me siyar da Awarar gasken.

Zuciya ta zowa Umaiman wuya kamar zata yi Amanta ta kalleshi tace
"Uwarka ce me suyar Awara bani ba shege dan masu..."
"Akul dinki da yi mana zagi a cikin gidannan idan ba haka ba sena gurje bakinki, aida Awarar kike soyawa ma da kin samu abinyi" Abba daya shigo ya dakatar da ita, seta fashe da kuka babu shiri tana cewa
"Haba Abba ku kumin sannan wasu su shigo sumin ku goya musu baya wannan wane irin abu ne?"
"Halinki yaja miki da ace kin zauna inda Allah ya ajiyeki da babu wanda ze ganki ya zageki amma tsarin da kika dauka kenan ai shikenan" ya fada yana wucewa ciki dan ana shirin shiga sallar Magriba ne. Salman da Abokansa kuwa jiki a sanyaye suka fice daga gidan Umaimah ta ringa kuka tana suyar Awara, wlh da Ace yaron nanya matso kusada ita seta dulmiya kansa a kaskon dan ubansa sedai duk yanda za'ayi ayi. Haka ta gama suyar wata danya danya wata ko harta qoneta ta bar musu a gaban kaskon ta shige daki tana ci gana da gursheqan kuka. Waiita me tayi data cancanci wannan qasqanci haka?
Idan laifinta suke gani ai ba ita ta kashe auranta ba su suka ce a sakota akan me kuma za'a kafa mata qahon zuqa idan ba'a dubi cin Amanar da Khalil din yayi mata ba kuma ai ba a qullaceta ba inma taqamarsu abinda ta masa ba gashi nan ya warke ba yana yawonsa ita fa illar daya mata ai harta mutu ba zata warke daga ciwon cin Amanar daya mata ba. Yayi aure a bayan idonta sannan ya bita da tukuicin saki. Haka ta sake kwanciya bata ci komai ba dan tunda ta shiga dakin bata sake fitowa ba kuma babu Wanda yabi ta kanta da safe kuwa dakyar ta ke zama saboda yanda jikinta yake rawa dalilin Yunwa. Yanda ta fito tana bin bango ga fuskarta data jeme a dare daya ya sa Mama kama aikin abin kari saboda yan makaranta da Abbazeyi fada shima daya ga Umaiman yayi shiru duk sun san yunwa ce take rarakarta, ta gama bin bango kamar qadangaruwa Mama ta daga Ruwan shayi dan tun dare an siyo biredi suka hada da ragowar Awarar kowa ya kama inda zashi ganin babu sarki se Allah yunwa na neman halakata yasa ta farwa shinkafarta da qanqararta da komai ta hau ci.

Seda taci taci se Amai kuma ta tafi bakin famfo ta ringayi gaba daya jikinta yayi laushi dakyar ta iya kuskure baki ta tashi ta koma qofar dakinta ta zauna jikinta na kaf kaf kamar zazzabi na shirin rufeta. Duk yanda Mama taso ta dauke kai seta kasa ta tafi dakin Abban ya zaune yana karyawa ta zauna a kujerar dake kusa dashi a sanyaye tace
"Alhaji kayiwa Allah ka sassautawa yarinyar nan akan batun Abinci kar yunwa ta illa tata"
"To se me? Mu illoli nawa tayi mana?" Abba ya fada ba tareda ya kalleta ba Se Maman ta shiga share hawaye tana cewa
"Na sani amma Alhaji kamata yayi mu bar komai a hannu Allah muci gaba da nema mata shiriya dan ni na fara yarda kwakwalwar Umaimah ba'a saiti take ba mutum me cikakken hankali baze ringa abubuwan da takeyi ba"
Chapter 227 · 0% Book details