← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 267

Sashe 59

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Hakane Maman Hibban in sha Allah zan kiyaye" Umaimah ta fada sukayi sallama kowata shiga gidanta.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 27

Bayan tayi sallar Magriba ta miqe a gurin ta bude WhatsApp din dan taga ko an sakata dan daman duk a takure take tsahon lokacin nan na rashin groups din dan taji dadin su wancan karon. Halima dai tayi rantsuwar bazata qara sakata a WhatsApp group ba tunda bata da mutunchi dan kona class dinsu ma na secondary s zuwan da tayi Dutse Ruma ta saka aka maida ita dana Poly.

Cikin sa'a tana shiga WhatsApp din ta ga an sakata a groups hudu harda na girki, tsaki tayi ganin na girkin da sauran biyun a rufe suke iya Admin ne suke magana ta tsani irin groups din nan da ba'a sharing idea to ko meye amfanin hakan oho sedai ayi ta turo muku abu ku bazakuyi magana ba gara gara ma na girkin tunda shi Recipes ne ake turowa amma in kana da tambaya sedai ka bi Admin pc kenan ta tabe baki shiga wanda yake a bude daga sakata zuwa lokacin ta tararda messages sama da dari.

Info din group din ta fara dubawa taga mata sun kusa dubu a ciki a fili tace
"Tab kace a kwai gwarama dan nasan nan ba mutane kadai ba harda Aljanu se an samu" ta rubuta sallama ta tura ba a dauki lokaci ba aka shiga amsa mata wata azakwai tace

"Ban taba ganin wannan sunan ba a gidan nan da gani sabuwar zuwa ce se ki gabatar da kanki ki turo hoto da voice note".
"wani sabuwar dokar groups ce haka da za'ace dole seka tura hoto da voice" ta fada a ranta, a taqaice tayi bayanin kanta da voice message ta tura kafin ta shiga laluben hoton da zata tura, daga cikin hotunan datayi ranar da sukaje Yinin cousin din Khalil ta zabi wani da tayi a gaban Mudubi yayi kyau sosai ta tura aka ringa mata sannu da zuwa anata yaba hoton ta da zuzu tawa suna cikin haka Adminta rufe group akan za'a fara gudanar da Program na ranar,a tsarinsu kullum suna da abinda suke gabatarwa na qaruwa na dan wasu mintina idan an gama se abude group aci gaba da sharholiya.

Fita tayi ta ci gaba da bude status da duba massages din mutane kafin a gama program din da akace za'ayi ranar zasuyi ne akan Ado da kwalliya. Wata number taga tayi mata magana kamar ta share se kuma ta bude

"Assalamu alaikum Asiya dama rai kanga rai" aka rubuta, seta bude info din number, Zee Ladan sunan me lambar ga hotonta nan akan Dp tayi zooming ita dai ko a irin fuskokin da bata gama tantancewa babu wannan sannan sunan data kirata Asiya ba sunanta bane kuma gashi suna cikin group daya sabon da aka sakata dazu dan haka ta rubuta mata
"Wrong number" kawai ta tura.

"Lallai Asy, daman ance kin zama big girl yanzu kin yada duka yan GGC amma ban zata nima zaki ce kin manta dani ba duk irin zaman mutu chin da mukayi daga yin Candy kikayi batan dabo akace kun koma garinku Zamfara se yau Allah yasa naganki a group ina ganin hotonki na gane ki" matar ta sake turo mata da dogon rubutu, se Umainah taja tsaki a fili tace

"Baiwar Allah inaga kinyi kuskuren lamba dan ni ba Asiya sunana ba Umaimah nake kuma ni ba yar Zamfara bace a Kano nake"
Se matar ta turo mata sticker irin ta mamakin nan tareda voice note tace
"Kai amma wannan kama da yawa take, dan Allah bakuda yan uwa a Zamfara? Kamar ku daya da wata qawata da mukayi Secondary Asiya Sani ina ganin hotonki bakiji yanda nayi murna ba dan nafi shekara goma ina nemanta"

Umaimah na shirin bata amsa tajiyo horn din Khalil dan haka ta kashe datar ta ajiye wayar ta miqe dakyar dan cikinta yayi nauyi, daga bakin qofa ta jirashi ya shigo da mota ya kulke gidan, hannunsa dauke da manyan ledoji ya ajiye su aqofar kitchen seta qarasa tana masa sannu da zuwa ya amsa yana cewa

"Zabi ne Kawu Labaran ya saka aka yanka mana an gyara su se ki saka a Frizeer" ta amsa ta toh ta shiga kitchen din dasu shi kuma ya shige daki.
Seda ta kai masa ruwan sanyi da Lemon Tamarin da tayi tun da rana ta barshi ya shiga wanka ta koma kitchen din ta kunna Gas ta shiga dumama miyar zogale da yake tuwo tayi ta cire zabin ta sake wanke su dakyau ta saka a Freezer sannan ta shiga hada kayan abincin tana kaiwa kan Dining tana gamawa Khalil ya fito da shirin fita masallaci.

Sannu yayi mata yace bari yaje yayi salla tunda an kira se itama ta wuce ciki ta sake Alwala ta dawo palour tayi sallar ta, tana idarwa ta sake zarar waya, Khalil ya shigo ta tashi ta koma kan Dining din ta zuba masa abinci ya fara ci yana kallonta ganin ta maida hankali tana kallon waya tana zuba murmushi,

"Me kike kallo a wayar haka da kike murmushi" ya fada yana kallonta, seta dago tace
"Babu komai nida Maman Asad ne wai jiya ashe Nuratu tayi naqudar qarya har Asibiti aka kaita sun zata haihuwa ce akace da saura bakaga yanda ta gigice ba wai tana ta sambatu"

"Uhm daman ana naqudar qarya ne qila dai ita tasan abinda take ji a jikinta" ya bata amsa yana ci gaba da aikawa cikinsa tuwo Umaimah ko ta maida kai taci gaba da danna wayarta.
"Ke bazaki ci ba?" Ya sake jefa mata wata tambayar ta daga masa kai kawai alamar eh se ya saka hannu ba tareda ta ankare ba ya zare wayar daga hannunta ta dago tana marairaice fuska yace

"Uhm kice kin koma sana'ar taki ta chatting ko" ya fada yana bin chats din group din dan tana ciki lokacin.
"Wato abinda kukeyi kaiwa daren kenan ku zauna kuna qare mana zagi da sharri kala kala ko?" Ya fada yana yamutsa fuska saboda ganin wata mata data ke cewa 'ai duk maza tsinannune, idan ba ana cin kutumar ubansu ba ba'a daidaitawa dasu' ya miqa mata wayar yana cewa

"Ita wannan harda uban ta a ciki kenan ko? Allahya rufa asiri"
"Bafa kasan me akayi mata da take fadar haka ba" Umaimah tayi saurin katse shi seya tareta shima yace
"Duk ma me akayi mata ya kamata tayi jam'u ta tsinewa mazan duniya duka? Daga jin kalamanta kinsan ba matar arziqi bace bana so ki fita daga wannan group din idan ba haka ba ranki ze baci Umaimah, na fuskanci a nan kike kwasu duk baqin halayen da kike zuwa dasu toh ki fita idan ba haka ba zan karbe wayar gaba daya ki rasa" ya qarasa yana miqewa tsaye dan gaba daya abincin ya fita a ransa.

Cikin palour ya koma ya kunna labarai Umaimah ta bishi da kallo kafinta miqe itama ta koma kusa dashi tana cewa
"Honey bafa wani abu bane ba kuma ni banma san wacece ba kawai magana akeyi ta sako baki kagani ma Admin seda tayi mata magana tace be kamata ba abinda ta fada"

"Nidai na gaya miki ki fita, ba kijw kin shiga cikin marasa hankali bama ya aka qare" ya fada ba tareda ya kalleta ba, seta zumbura baki tace
"Me kake nufi"
"Duk abinda kike tunani shi nake nufi" ya bata amsa kamar me jiranta seta tabe baki tace
"Toh Allah ya naka haquri da alama dai a waje aka bato maka rai to kayi haquri".

Be tanka ta ba, maganar matar ce take ta sukarsa a rai wato shi yasa kenan Umaimah kullum cikin tayar masa da hankali take saboda tanajin karatun irin wadannan matan da suka kwashe kayansu daga gaban ma'aiki suna tunzura mata su kai su wuta ko?

Umaimah ko gefe ta koma ta zauna akan carpet ta ci gaba da danna wayarta, matar dazu ta sakeyi mata magana se sannanta tuna dazu batayi mata reply ba ta bude

"Naji kince a Kano kike dan Allah toh ina so mu qulla qawance ki zamar mun makwafin qawata da nake ta nema ban samu ba dan wallahi har yanzu ban gama yarda baku hada jini da ita ba, a ina kike kuma yaya sunanki?"
Mayar mata amsa tayi da cewa
"Ni sunana Umaimah, ina Kano Unguwar Tudun-yola get 4 kefa?"

"Nice name Umaimah ni kuma sunana Zainab Ladan zaki iya kirana da Maman Nihal bamu da Nisa ina Janbulo Third Gate, ina da aure yarana Uku" ta tura mata tareda hotonta da wasu kyawawan yara mata guda a wani tamfatsetsen palour.
Chapter 59 · 0% Book details