← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 267

Sashe 24

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ok assume ka fasa auranta how about the life of innocent girls da zakayi puting at risk? Kace cewa fa tayi tunda ta rasa kowa ma baze samu ba zata kashe duk Macen data shiga rayuwarka, to is it not better to Marry her and save lives ko kuma ka zabi ka jazawa yaran mutane ko kuma zaka zauna ne babu aure?

Think about it Khalil ba fata ba ace qanwarka akayiwa haka in a month time to her wedding mijin yace ya fasa kai baka san zafin abin ba ni na sani because it happend to my sister kana kallo sanadin haka Lubabatu har depression ta shiga, tun farko ai Iyayenta basu rufe ka ba sun gaya maka komai amma zaqin soyayya ya kwasheka ka kasa ganin aibunta se yanzu?

Kishi kuma kaine zakayi abinda ze motsa mata shi indai ka kiyaye zaku zauna lafiya, idan kasan halin mutum kaci maganin zama dashi shikenan. In  dai shawara ta kake nema Khalil just go on with Umaimah, kayi Addu'a Allah yasa hakan ya zamar muku Alkhairi".

"Shikenan Mansur nagode zanje na cigaba da Addu'a Allah ya zaba mana mafi Alkhairi" Khalil ya fada yana miqewa tsaye, sukayi musabaha ya kama hanyar fita a ransa sam beji wata magana da Mansur din ta fada ta kama shi ba. Ta ina ma ze fara wannan gangancin? Shima Mansur din qin Allah ne yasa yake gaya masa haka yanzu bayan tun farko ma shine ya fara nuna baya son Alaqarsu a sannan ma zato kawai yake na tana da Aljanu, se yanzu daya samu babban dalilin rabuwa da ita yace masa wai Aa karyayi saboda bashi aka ce za'a kashe ba ina ba wannan maganar.

Daga Asibitin su Mansur Asibitin da Hajiyar sa take kwance ya wuce dan su biyun nan sune manyan abokan shawararsa, duk kuma abinda suka yanke masa dashi yake amfani toh yau Mansur yayi Failing yanzu saura Hajiya dukda be so ya tado mata da maganar tana Asibiti yaso ace se ansallame ta amma lokaci yana tafiya. Ko jiya da daddare seda tayi mitar me yasa ba'a kai lefe ba aka tsaya saboda jinyar da takeyi ta kuma ce a cikin satinda za'a shiga ko ba'a sallameta ba a saka rana akai.

Daga yanayin sallamar sa Hajiyan ta gane babu lafiya, yaja kujera ya zauna suka gaisa da Mama Talatu matar qanin Hajiyar ce da suke matuqar shiri tun qaninnata yana raye har yanzu kuma daya rasu suna zumunchi sosai yanzun ma ita take zaman jinyarta.

"Ango kasha qamshi, yanzu fa zancenka muke Hajiya tace na miqa mata waya ma ta kiraka ashe kana tafe" Mama Talatun ta tsokane shi, se yayi murmushin da be kai zuciya ba ya shiga gaishe su, mace ce me wayayya daga yanayin da Khalil dinya shigo ta fuskanci da magana a bakinsa dan haka ta miqe bayan ta tura masa kayan karin da su Habiba suka kawo tayi waje ta basu guri dan bata san maganar da yake so yayi kota sirri bace.

Hajiya dake qare masa Kallo tunda ya shiga dakin tace "Babana lafiya kuwa? Kaga fuskarka yanda tayi meya same ka bayan ka bar nan jiya, koda yake tun a daren na fahimci baka da walwala ko jikin Umaiman ne yaqi dadi?"

Sunan Umaimah data ambata ya qara saka zuciyarsa tsinkewa, toh Mansur ma yaqi bashi goyon baya inaga Hajiya datafi kowa son hadinsa da Umaimah bama ya zaton zata saurari duk abinda ze zo dashi amma koma yaya ne dole ya gaya mata tunda dai bashi da wadda ta fita.

Kansa ya shiga sosawa ba tareda sunhada ido ba yace
"Hajiya daman akan maganar tane, inaga Kawai a dakata da maganar kai kayan nan yanzu"

"Kamar yaya a dakatar da kai kaya Babana? Ina saura sati hudu daurin aure ya kama yau? Idanba'a kai lefe yanzu ba har se yaushe za'a kai musu bayan da tun satin daya wuce za'aje wannan tsautsayin ya faru, idan ma dan maganar kudi da akace ka bada ne baka dasu ka barshi zan gayawa Sa'adah ta ranta a qarasa komai in yaso ni daga baya se na bata" Hajiyan ta fada cikin kulawa tana kallonsa.

Tasan harkar biki da cin kudi kuma Khalil din yayi Namijin qoqari sosai tundaga kan gyaran gidansa daya dawo kamar sabo kai bakace an taba rayuwa a ciki ba har zuwa kan lefen sosai ya saki kudi akayi masa siyayya dukda Yan uwansa Mata sun saka hannu amma shi yayi rabi da kwatan kayansa.

"Hajiya ba maganar Kudi bace ta saka ita Umaiman ce kawai nake ganin kamar zamn mu baze yuwu ba saboda HALIN KISHInta" Ya sake fada kansa a qasa. Se Hajiya ta saki murmushi taredagyara zamnta dakyau tana kallonsa tace

"Se yanzu kenan yan tsurku da munafuncin suka tarar dakai, Baban yaushe ka fara saurarar qananun maganganu na mutane?
Tun sanda ka fara neman auran yarinyar nan babu kalar gulma da tsugudidin da ba'a kawo mun akan ta ba ance baqin kishi ne da ita, bata da nutsuwa, aa mutuniyar banza ce kai har akwai wadda tace ta zubar da ciki shi yasa sau uku ana saka mata ranar aure ana fasawa".

PROMO
PROMO
PROMO

BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻

08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO

SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK(UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

PAGE 12

Da sauri Khalil ya daga kai ya kalli Hajiyan jin wannan qundumemen batu, ta daga masa kai da sigar tabbatarwa kafintaci gaba da cewa
"Tabbas, magana ba irin wadda ba'a gaya mun ba amma duk naji na toshe kunnena saboda nasan da cewar qarya ce. Tun kafin naje gidan yarinyar seda yar uwarta ta zayyana mun komai akanta tun kama daga kan Kishin da mutane suke ganin tanayi yayi yawa har halin tsiwarta da komai yar uwarta bata boye mun ba.

Haka zalika da naje gidan su Mahaifiyarta ta sake tisa mun tamkar yanda yar uwarta ta fada abinda ya qara musu qima kenan a idona dukda take tasu ce basu boye aibunta ba sun bayyana wanda shine gaskiya dan aure ba'ayi masa rufa rufa, idanma an rufe shi hali baya buya dole wata rana ze bayyana kansa kuma kaima nasan ka san komai kuma kaga kaji ka gani kana sonta a hakan, se yanzu da dan lokaci ya rage sannan zaka bari hudu bar shedan da gulmar mutane tayi tasiri a zuciyarka?

Meye matsalar ta, kishi koh? Toh kaje ka tambayi Hajiyar Gaya (Mahaifiyarta) zata baka tarihin quruciyata, kuma yau da Mahaifinka yana raye da ka tambayeshi shima ya baka labarin Kishina dukda haka kana iya zuwa gurin Babanku Jibril (Babban Aminin Mahaifinsu ne) dan dashi aka sha gwagwarmayar komai.

Dan haka idanma abinda ya gigitaka kenan kazo kamar wanda aka biyo toh kama dena wani tunani akan batun kishi kowacce mace zaka aura tana da kishi sedai kawai na wata yafi na wata zafi, kuma wata tafi wata iya danne nata, in dai kuma kace zaka ringa daukar zugar mutane akan iyalinka toh kana tareda matsala kuwa. Dan wani qyashi da hassada ce zata saka ya ringa kawo maka gulmar da zata haifar da rashin zaman lafiya a gidan ka".

Shiru Khalil yayi, daga yanda hajiya take jero masa bayanin nan ya tabbatar da babu wata kalma da zeyi amfani da ita da zata saka ta ga baqin Umaimah, amma dukda haka baze sare ba dan shi harga Allah ya tsorata da auranta saboda duk wadanda zasu ce yayi basune zasu zauna da ita. Ba fata ba kuma ranar da abin qi ya faru ace shi ya jawo wa kansa dan haka tun kafin azo wannan qadamin dole ya nemar wa kansa mafita, idan Kuma Allah ya qaddara faruwar auransu shi kenan, amma dai Allah ya gani yayi iyawarsa dan ya tseratar da kansa daga wahala.

Zaman sa ya gyara yace "Hajiya wannan ba zancen zugar Mutane bane, jiya fa Hajiya saboda mun riqe hannu da Jamila shine tayi fushi ta tafi ko mota ta qin hawa tayi se Nuratu kawai na mayar gida ita ta hau Adaidaita, sannan bakiji abinda ta ringa fadamun ba har cewa tayi ta fasa auran ma gaba daya ita.
Toh Hajiya tayi haka akan Jamila da tasan babu aure a tsakanin mu inaga kuma idan ta ganni tareda wata macen? Ni dai tsoro nakeji Hajiya, kina kallo dai yarinyar nan matar Hafizu na can qasan layi da ta cakawa masa wuqa saboda zeyi aure, yanzu da yazo da qarar kwana da tuni fa an manta da babinsa".

Seda Hajiya ta gama jin sa tsaf ta kalle shi da hararar wasa tace "Nidai Babana takwaranka kafin ya mutu se da yayi mata takwas kuma hurhudu suka zauna idan wata ta rasu ya maye da wata kana kallo da dai wayon ka ya bar hudu rayayyu gashi nan kuma har yanzu suna zaune a cikin gida guda dukda baya nan, se kai kake tsoron guda daya jal Khalil? Kuma banda abinka Mijin da ake so ai shi ake kishi.

Da bata sonka idan matan duniya zaka kula ko a qasan takalminta sannan maganar Jamila ai dole tayi kishi yanda kuke abu kamar wasu qananan yara su Allah ne be taba kai idon Mazajensu sunga kuna wannan rungumar da riqe hannun ba da tuni sun taka muku burki, nasan kuma kai yanzu da ace zatayi haka da nata dan uwan se anji kanku dan kaima ai zani ce ta taradda muje zuwa kishin ne da kai.
Chapter 24 · 0% Book details