← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 267

Sashe 100

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dubasu ta farayi, a zahiri hotunane irin wadanda Yammatan yanzu harma da wasu matan auran suka daukesu a matsayin wayewa. Da yawansu ta fito daga Wanka tana daure da towel qarami daya bayyanar da irin kyan dirin da Allah yayi mata, wadansu rabin qirjinta a waje anyi wasu irin dauka dai da sam basu dace ba, wasu ita kadai wasu tareda mutane sun rungume juna ko suna kwance tare typucal hotuna dai irin na wadanda suka aro dabi'ar yahudawa suka dorawa kansu sam babu ganin rashin dacewa ko wani aibu kan abinda suke yi din sannan mafi yawancinsu a Hotel aka dauke su Wanda yake alamanta da yawa a lokutan tafiye tafiyensu na aiki take daukar su wannan a tunani irin na me hangen nesa da kyautata zato akan duk abinda ya gani kenan, banda Umaimah data rigada ta hau tayi daram akan zantukan Khausar din dan haka batareda ta bata lokaci ba ta ware wadanda take ganin sunfi muni da bayyanar da abinda take son isarwa ta aikawa da kafatanin yan gidan su Khalil din tun daga kan Hajiyarsa har zuwa kan Habiba autarsu, babu kodar a zuciyarta ta qara da saqon

"Ita ce matar da Khalil yake qoqarin aurowa a ta biyu, na kuma samu tabbacin cewar yar Lesbian ce ina kuam da shaida akan hakan".

Bayan ta gama turawa ta ajiye wayar, Agogo ta kalla qarfe biyu da minti sha biyar shi acan yanzu uku fa sha biyar kenan qila yana bacci, koda yake dole yayi bacci ya dauki farka ragowar Maza da Mata ya tafi da ita shiyasa har ya kwashi kwana biyu be kira ta ba balle yaji lafiyarta data cikindaya qaqaba mata.

Wayar ta sake dauka ta shiga WhatsApp, zuciyarta ta rigada ta bushe ba kuma ta tsoron ta mutu ko tayi rai balle abinda ze iya zuwa yazo babu tunanin komai Umaimah ta ringa aikawa da hotunan data turawa su Hajiyar Khalil zuwa duk wani WhatsApp group da take ciki tare da bayanin cewar gagarumar yar Lesbian ce sannan ta sake wucewa Tiktok ta dora hotunan da irin bayanin data tura a WhatsApp. Se bayan data gama aiwatarwa sannantaji hankalinta ya kwanta zuciyarta tayi sanyi, ko iya haka aka tsaya tasan ta gaka da rayuwarta ta tona mata Asiri a idon duniya babu me sake kallonta da idon rahama sannan ba Asiri ba ko tsafi tayiwa Khalil dan ya so ta tasan wannan magana ta rushe in dai yan uwansa suka gani.

Bacci ne ya kwasheta irin na wanda ya samu nutsuwar zuciya, ranta fes kamar an wanke shi da Hypo dan ta san ta gama da wannan maganar kuma sedai wata a gaba.
*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 42

Bata sake duba whatsapp din bama se wash gari da kusan qarfe tara bayan tayi wanka ta karya kuma se a sannan taje ta gaida Abba yayi mata yaya jiki da tambayarta Aboki kamar yanda yake kiran duka Jikokinsa Maza tace yana gidan Hajiya. Zam zama da dabinon Ajuwa ya bata yana cewa
"Gashinan musamman nayi dawafi dashi saboda ke, kisha ki shafe jikinki da niyyar Allah ya shirya ki ya shirya tunaninki ya kuma baki lafiya keda abinda yake cikinki ku rabu lafiya".
Seta tura baki gaba wai ita me takeyi da kullum ake faman cewa Allah ya shiryata koda yak shariyar Allah ai bata yawa Allah ya shiryeta din. Seda suka taba yar hira kafin ta fita Mama dai daga amsa gaisuwar da tayi mata bata ce komai ba ta bita da kallo a ranta tana mamakin walwala da annashuwar data gani a fuskar Umaiman, sannan har yanzu da dan sauran kumburi a fuskar tata ga jini daya kwanta cikin idonta bangaren da ta sha mari.

Seda taci dumamen Tuwo ta qoshi kafin ta ciro wayar daga chaji ta bude, Missed calls ta gani sunfi Ashirin, Anty Amina, Jamila duk sun kirata ga na Jalila da yafi na kowa yawa a ciki dan haka ita ta fara kira
"Umaimah saqon da kika turamun duk su Jamila sunce suma kin aika musu harda Hajiya me yasa, badan Allah yasa wayar ta na Hannun Khalifa ba shi ya gani ya goge me kike tunanin ze faru idan ta gani? Ai da kin bari mun fara magana dake kafin kowa ya sani musamman Hajiya kin san bata son damuwa musamman kuma akan abinda ya shafi Khalil" Jalilan bayan data amsa sallamar Umaimah.

Wayar ta harara a ranta tace 'aikin banza' a fili kuwa kukan qarya ta fashe dashi tana cewa
"Toh ya kike so nayi Anty Jalila so kike na zauna ina ji ina gani ya dakko mun masifa ya kawo gida? Na san baze taba fada muku gaskiya ba dan nima besan na sani ba shiyasa ban bi takansa ba kai tsaye na sanar daku dan nasan idan na fara masa magana qaryatawa zeyi sannan ya toshe duk wata hanya da gaskiya zata fito. Nidai wallahi tun wuri kuyi masa magana idan ba haka ba ni bazan zauna ba ya aurota haka kawai wani Gingimemen baka'i ya sauka a gidan mu ba iya kanta ze tsaya ba harda mu ze shafa" ta cigaba da rusa kuka kamar gaske ita dai Jalila ta kasa magana dakyar ta iya cewa
"Shikenan kiyi shiru hakan ma bazata faru ba da iznin Allah kuma na tabbaatr da shi kansa Khalil din be san haka take ba da babu abinda ze kaishi gurinta. Kuma ma ana ta neman layinsa kusan kwana biyu kenan daman bana samunsa ko a Whatsapp bana ganin sa Online in sha Allahu komai ze daidaita kinji ki dena kuka" daga haka sukayi sallama akan zata sake kiranta.

Tana kashe wayar ta sheqe da dariyar shaqiyanci dan ko a jikinta wai an mintsini kakkausa. Whatsapp ta shiga, Messages ta tarar rututu a duka  groups din nata kaitsaye kawai ta bude Group din daya fi mata dadi, kusan kaf maganar ita akayi tagging abinda ta tura jiyan, qarshe ta tafi inda taga wata tace

"Kai wannan ai Hadiza Musa ce, Lawyer ce kuma tana aiki a hukumar kare haqqin mata da qananan yara ta garin nan ko amma kuwa dai ta bata wayonta wallahi, kunsan yanda ake yabon kirkinta da kamun kanta kuwa ko kwatance za'ayi a gurin na mata masu kamun kai da ita akeyi amma ashe ashe tab abinda take aikatawa a boye kenan amma anji butur wallahi"

"Daman ai laifi bashi da kama yanzu da Allah ya tashi tona mata Asiri ai gashinan, kuma ta jira taga sakamakonta" Umaimah ta rubuta nan sukayo mata caaa kowa da tambayar a ina ta jiyo wannan magana dan daman tun cikin daren wadansa suka fara gani suke tambayarta, har PC gwanayen gulma suka bita tuni kuma da yawa suma sunyi forwarding saqon zuwa sauran group sedai Allah ya taqaita tsayuwarsa kawai.

Rufaida ce ta kirata a waya ta daga tana cewa
"Ke tun Asuba nake kiranki baki dauka ba"
"Bangani ba se yanzu na dauki wayar kuma banma lura da kiran ki a ciki ba" ta bata amsa, se Rufaidan tayi saurin cewa
Chapter 100 · 0% Book details