← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 267

Sashe 148

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sanda Abba ke labarta mata abinda Umaiman ta sake aikatawa kuwa kasa motsi tayi a gurin banda binsa da kallo ba abinda takeyi dan ko tunani ta kasayi a kwakwalwarta.
"Wallahi Malika saboda kunya kasa cewa komai nayi se su Badaru ne sukayita fadace fadacensu. Yanzu ace Umaimah bazata bar rayukan mu su huta ba kullum ta Allah da sabuwar rigimar da zata janyo mana?
Nidai na yanke shawara zan kira yaron nan daga baya, ya fadi gaskiya karya ji kunyar mu idan har yana ganin da cutarwa a cikin zamansu ya sawwaqe mata kawai kowa ya huta tunda dai ita bata san inda yake mata ciwo a rayuwarta ba, gara ta dawo ta zauna kawai kafin wata rana ta dakko abinda zata saka a hada harda mu a kulle".

Hannu Mama ta saka ta share hawayen dake mata tsere akan fuska amma suka qi tsayawa, cikin sheshsheqa tace
"Alhaji na gaji da Halin Umaimah na gaji ban san wace irin yarinya bace ba, Allah ya gani iyakar iyawa babu ta inda na banbantata da yan uwanta a gurin tarbiyya, raino daya nayi musu harma nafi lura da saka ido akan al'amuranta. A kullum na daga hannu kafin na roqawa kaina komai sena roqawa Umaimah amma na sani Allah ba mantawa yayi dani ba yana sane kuma in sha Allahu jarabawar da yayi mana akanta zata zamo mana kaffara" ta qarasa tana sakin wani kukan me nuna zallar zafin da zuciyarta takeyi. Cigaba tayi da magana tana cewa

"Yanzu Abdullahi seda ya qare min tanadi tas akanta kafin ya fita, a gaban Saratu yake fadar cusa maka ni akayi saboda na rasa ma'auri baka sona ka aureni a bazawara ya gama fadar maganganunsa ya fita duk saboda Umaimah, shikenan saboda na haifeta bazan samu nutsuwar zuciya ba? Kullum tazo gidan nan cikin fargaba nake se naga ta tafi salin alin sannan hankalina yake kwancita har se yaushe? Se yaushe zamu huta da matsalolin Umaimah?".

Kuka take sosai Abba ko ya rafka tagumi ya kasa rarrashinta, seda tayi me isarta kafin ta miqe tayi masa saida safe, kai kawai ya iya daga mata danshi kansa zuciyarsa a dagule take da zeyi kukan ma daya ji dadi.

Koda ta koma dakin inda ta bar Umaimah nan ta tarar da ita. Kallo daya tayi mata ta wuce cikin dakinta kai tsaye Alwala ta daura ta shinfida Sallaya ta fara jera nafiloli. Kwana tayi tana sallah ko kadan bacci be ziyarci idonta ba, toh ta ina zatayi bacci bayan Allah ya hada ta da yarinya irin Umaimah?

Da Asuba Umaimah da tayi kwanan zaune ita ba sallah ba ba salati ba tana ta faman sharar hawayen da bazasu magance mata komai ba, dakyar ta iya miqewa saboda yanda qafafunta suka haye saboda zaman da tayi ta ringa dafa bango harta shiga dakin Maman. Alwala ta dauro, Mama data idar da Raka'atanul fajr tabita da kallo harta fito daga bandaki ta nemi gefe kusada Maman ta zauna dan ba zata iya sallar a tsaye ba. Seda suka idar da Asuba kafin ta kalli Maman cikin muryarta da bata fita saboda kukan data sha ta gaisheta.

Da "Lafiya" ta amsata batareda ta kalleta ba taci gaba da lazumin da takeyi, Umaimah ta sunkuyar da kai hawaye suka kawo a idonta cikin muryar kuka tace
"Dan Allah Mama kiyi haquri wallahi...."
"Dan Allah karki dameni bakiga abinda nakeyi bane? Tunda ke daman sallar kadai kikeyi bakya addu'a se ki tashi ki bani guri nikam inada buqatu da yawa gurin Allah karki dameni" Maman ta katseta ba tareda ta bari ta fadi abinda take so tace ba. Se kuwa ta saki kukan da take qoqarin hana fitowarsa, a fusace Maman ta juya tace mata

"Tashi ki bar nan kafin na saba miki"
"Dan Allah Mama ki tsaya kiji, wallahi Allah bayin kaina bane, Safina ca ta bani shawara kuma tace mun ta tabayin hakan itama shi yasa nayi amma ban zata abin zeyi zafi da yawa haka ba" Umaimah ta fada cikin kuka tana matsawa gaban Maman.

Carbin da take ja ta kai mata duka dashi ta goce dukda haka ta sameta a hannayenta data saka ta rufe fuska dukan ya shigeta kuwa sosai
"Badai ke kince bakya jin magana ba? Bazaki bar zukatan mutane su huta daga tashin hankalinki ba ko? Ai shikenan kici gaba da daukar hudubar mutane suna ingizaki kina rashin hankali, Qawaye ko? gaki gasu Umaimah wata rana se sun kaiki kurkuku sun ja miki daurin rai da rai sannan zaki dawo shikin hayyacin ki shashasha kawai" cikeda takaici Maman tayi maganar tana miqewa dan barin mata dakin tunda ita taqi fita. Palour ta koma, tana jiyo Umaiman na kuka daga ciki.
[8/18, 9:52 PM] KYAUTA: *TASTED & TRUSTED*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE, MASU JEGO DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*AN GWADA ANGA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGE WA DA WANNAN SAIWOWIN ZAKI YI AMFANI DA SU SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL PACKAGE, AKWAI RABI, TA YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*.
*KAYANA NATURAL NE DOMIN SAIWOWI NE DA AKE HAKOSU A DAJIKAN CHADI. BAYAN SAUKAR DA GAMSUWA HAR YAQI SUKE YI DA DRYNESS DA KUMA INFECTIONS.*
*AKWAI NA TSUGGUNO DA YAKE HA'DE MACE TA MATSE.*
*AKWAI HADADDUN DAKA NA SHA DA MADARA KO NONO WANDA BABU ALGUS*.
*SANNAN AKWIA GADALIN MATA NA ASALI, WANDA SHA YANZU NE MAGANIN YANZU DA IKON ALLAH*
*AKWAI MAGANIN SANYI SADIDAN*.
*DUKKANSU TESTED & TRUSTED NE*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*.
*NATION WIDE DELIVERY* .

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 56

Abba yayi sallama ya shiga falon ta amsa ya nemi guri ya zauna kusada ita. Bayan sun gaisa yake ce mata
"Malika kinga idonki kuwa a dare daya har kin zabge dan Allah ki cire damuwa daga zuciyarki, ita rayuwar mumini bata cika dole se ana jarabtarsa dan gwada imaninsa dan haka mu mayar da komai ga Allah kuma mu ci gaba da neman taimakonsa shi kadaine ze iya mana".

Hawaye ne suka fara sakko mata cikin tsananin tausayinta ya kama hannyenta biyu yana cewa
"Ki dena kuka, wadannan hawayen suna daga abinda yake qara dagula rayuwarta kiyi shiru kici gaba dayi mata addu'ar da kikeyi kullum in sha Allahu wata rana se labari kiyi haquri". Haka ya ringa lallashinta yana gaya mata kalamai masu dade harta samu ta tsayar da hawayen wanda sosai nauyin da qirjinta yayi mata ya ragu, a kullum Addu'arta Ubangiji yaci gaba da bata juriya akan al'amuran Umaimah karta kaita bango tayi mata baki.

Seda Abban yaga ta samu nutsuwa kafin ya miqe yace zeje ya duba Saratu, Mama ta rakashi da ido, shikansa tasan qarfin hali kawai yakeyi. Yana fita ta mayar dakai taci gaba da jan carbinta.

A tsaye ya tarar da Anty Saratu tana cire Hijabi alamar lokacin ta idar da sallah. Ya nemi gefen gadonta ya zauna, seda ta ninke hijabin kafin itama ta zauna tana gaishe shi.
"Jiya har nayi bacci shiru baki shigo ba" ya fada kasancewar ita ce da girki, seta yi murmushi kadan tace
"Ina nan jiran baqinka su tafi bansani ba bacci ya kwashe ni".

Kallonta yayi shima yayi murmushin, Saratu kenan bata san Mama ta gaya masa a gabanta Abdullahi yayi mata tijara ba. Yasan zancen ne bata so a tayar dashi shiyasa tayi masa alaye da cewar bacci tayi se ya miqe yana cewa
"Idan da akwai dumame ki kawo mun yanzu zan sha magani, jiya ban samu naci abinci da daddaren ba" ya juya ya fice daga dakin. Kallon tausayi ta rakashi dashi, tun jiya Salman ya labarta mata abinda ya faru ta dade tana ta''jibin taqadaranci irin na Umaimah tana kuma tausayawa Mama dan itace babbar abar tausayi ma sama da Abban. Dan ma shidin ya kasance me shiga lamuran iyalansa shinr sauqin da take samu, da ace tayi katari da irin iyaye Mazan nan da sanda yaro yayi abin kirki yake nasu, duk wata rigima ko damuwa ta yaro uwarsa ta shafa qila da yanzu qasa ta dade da rufe idon Maman dan ba zata iya da baqin cikin Umaimah ita kadai ba.

A iya zamansu sama da shekaru Ashirin idan ka cire sabani na yau da kullum da dole a same shi tsakanin mutane idan aka zauna bazata ce yau ga wani mugun abu da Maman ta tabayi mata a matsayinta na kishiyarta ko wani ba a zahiri, haka har badininta zata iya shaidarta da babu komai a zuciyarta se Alkhairi ba kuma ta nufin kowa da sharri ballantana ace ko wani mugun abu da take aikatawa ne take ganin sakayya akan Umaiman, kawai ta qaddara kalar tata jarabawar rayuwar kenan tunda kowa da akwai ta inda Allah ya rage shi ko yake jarabtarsa sedai suyi fatan Allah ya shirya Umaimah in tana da rabon shiriyar su kuma ya qara musu juriya.

Bayan La'asar bisa Umarnin Abba badan Maman taso ba ta shirya suka tafi mayar da Umaiman kamar yanda sukayiwa Waliyyan Khalil din alqawari. Daya kira Baba Abdullahi shi daya ce ta zauna goben ze mayar da ita cewa yayi in yaje Allah tsine masa, daman dan ya samu ya sauke fushinsa yasa ya hana tafiya da ita yanzu kuwa ko banza zata koma da tabon marinsa gidan Khalil. Dariya abin nasa ma ya bawa Abba, haka suka kama hanyar gidan qarfe biyar suka isa, a qofar gidan suka tarar da Khalil tareda abokinsa Nasir Tsohon Malamin su Umaiman ya kawo masa ziyara ze tafi ya fito rakashi.
Chapter 148 · 0% Book details