← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 244 OF 267

Sashe 244

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar Maman Asad ce ta katse mata tunanin da takeyi, ta dauraye hannunta ta miqe tana mata sannu da zuwa tareda karbar ledar data shigo da ita. Seda ta rakata har dakin Mama kafin ta fito ta shiga kitchen ta debo Zobo da Kunun Aya na roba data farayi na siyarwa bisa shawarar Nuratu, itace ma ta bata Jarin Dubu biyar ta fara kuma Alhamdulillahi tana samun na kashewa tunda daman sana'ar Anty ce ta saki ta dena. Seda ta ajiye mata su ta dauka tana cewa
"Karfa mu karya Jarin"
"Haba dai, ina su Khairi kikazo ke kadai" Umaimah ta fada tana miqewa harta Juya Hajiyayyen ta tsayar da ita tana cewa
"Ni Umaimah wai baki da kaya ne se wadannan tsummokaran?"
*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 83

"Ina dasu Mana amma gaba daya sunyi mun yawa. Wadanda kika ga ina sakawa su kadaine suke zama a jikina shiyasa" Umaiman ta bata amsa hawaye na neman balle mata, abu kadan ke sakata kuka yanzu yanda kasan matar mamaci. Mama data fito daga dakinta tace
"Kema da sonbata bakinki kike daman tunda kike da ita kinga tana saka suturun arziqi ne? Ga dai kaya nan kamar su kasheta bata saka ba bata kyautar ba shekara da shekaru a haka duk zasu ratattake su mutu bata mora ba" se kuwa hawayen da take riqewa ya balle dukda Mama tace ta yafe mata abubuwan data aikata amma sauda yawa irin yanda take mu'amalantarta se taga kamar har sannan da sauran fushinta a ranta. Babu ranar banza da bazata fada mata maganar da zata sosa mata zuciya ba, idan bata goran ta mata cewar sa'anninta nacan a gidan aure suna aikin lada ba seta mata shaguben koda ace zatayi aure a gaba inta samu ma'aurin kenan abinda take gudu gidan me mata zata shiga, ta kaso auranta akan wata kuma zata auri Mijin wata me kenan tayi da sauran maganganu masu sosa rai kuma ko a jikinta zata yaba mata kuskure kadan zatayi ta rufeta da fada tasani Mama na da duk wata dama ta jin haushinta domin tayi abinda dole koma waye ya washsheta amma a kullum tana addu'a Allah yasa su yarda da nadamarta, su yarda da cewar tayi dana sanin duk abubuwan da suka faru a baya sannan a shirye take data gyara kurenta idan ta samu damar hakan.

Jiki a salube ta koma taci gaba da ayyukanta tanayi tana goge hawaye sosai zuciyarta take mata zafi, idan da ace tana da yanda zatayi ta goge baqin febtin da tayiwa kanta da tayi kota samu sauqin abubuwan data ke fuskanta a rayuwarta a yanzu. Ta tabbatar badan tasirin addu'a ba data zauce, ta kuma yarda abinda ta rasa kenan a baya rayuwarta ta ringa walagigi ta ringa ayyuka cikin rashin nutsuwa da tunani babu neman zabin Allah a cikin lamuranta abinda zuciyarta ta darsa mata kawai shine daidai a gurinta da ace tun a sannan ta karbi gyaran da masu sonta suka ringa yi mata da bata tsinci kanta cikin Halin nadama mara amfani ba. Harta gama wanke wanken ta wuce daki da tayi niyyar ta koma falon Maman suyi hira da Maman Asad amma ba zata iya ba ta lura yau Mama da uta ta tashi a ranta gara taja jiki ta koma gefe. Tana kwance Maman Asad ta shiga da jakarta alamar tafiya zatayi daman ba zama tazo yi ba, ta tashi zaune tana kallonta itama ta nemi guri ta zauna tana cewa

"Kwanciya kikayi?"
"Eh wlh so nake na dan huta kafin anjima" ta bata amsa seta gyara zama tana cewa
"Dan Allah ki ringa gyara jikinki Umaimah tsafta ai tana cikin Imani amma ki ringa yawo a gida yarkace yarkace dake duk wanda ya shigo ya fita se yayi dake meye amfanin hakan bayan kina da suturun sakawa ba baki dasu ba. Sannan wannan uban baqin da kikayi da rama bafa sune zasu nuna cewar kinyi nadama ta gaske ba, wannan tsakaninki da Allah ne da kuma ta hanyar ayyukanki za'a fuskanci hakan amma quntatawa ranki da kikayi babu abinda ze qareki dashi sedai ya haifar miki da ciwon damuwa dan haka ki saki ranki, qaddara dai kowa da kalar tasa ke kinga taki Jarabawar a rayuwa se kiyi qoqarin cinyeta amma damuwa kuka tunani duk ba zasu baki mafita ba Addu'ar dai ita zaki cigaba dayi ki nace da roqon gafarar ubangiji in sha Allahu komai ze daidaitar miki, komai ze wuce ki gani tamkar be faru ba".

Kanta na qasa har Maman Asad tayi shiru kafin ta dago fuska shabe shabe da hawaye tana cewa
" Yah Hajiyayye kenan ai wanda yake da nutsuwar zuciya shiyake kwalliya nikam a matsayin da nake in har kaya zasu suturtani sannan babu wata qazanta a jiki da zata kawowa Ibadah ta tangarda bani da matsala. Wanka ma idanta qure harda Klin inayi mai kuwa sedai ka shafa dan kar qaiqayi ya dameni amma badan wai fatata tayi kyai ko wani ba ba. Maman Asad, Allah kadai yasan halin da nake ciki irin zafin da nakeji a zuciyata baze misaltu ba. Nasan na tafka babban kuskuren da babu wanda zeyi mun uzuri amma ina fatan ubangijin daya ce idan munyi kuskure mu tuba saboda shi ze yafe mana ya dubi nadamata. Allah ya sani ina cike da nadama me tsanani da dana sanin ayyukana na baya, da ace ina da iko dana sauya rayuwata Yah Hajiyayye, da ace zan samu dama a karo na biyu danayi qoqarin wanke kaina a zukatan duk wadanda na batawa amma bana zaton zan zamu wannan damar, abu daya nake da buri a yanzu kafin na koma ga mahalicci na na samu damar neman gafarar duk wanda na zalunta a baya su yafe min shi kadai ne abinda ze samar mun da nutsuwa a rayuwata".

Hajiyayye tayi shiru, tausayin yar uwarta ya cikata ita shaidace da cewar Umaiman tayi laushi ta kuma gasgata Nadamarta ta gaske ce bawai wuya ce ta sakata saduda ba kamar yanda Mama take fada. A taurin kai irin na Umaimah ta tabbatar da ba aikin wahala ba ko kasheta za'a yi babu abinda ze canza mata ra'ayinta haka inda ace bata zubda makamanta ba bazata taba kulluwa tsayin shekara hudu da ranta da lafiya ba tareda ta fita ba koda ace hakan na nufin ta bar gidan kenan na har abada a Umaiman dasuka sani a baya zata iya zabar hakan tunda kuwa harta jure komai tsayin lokacin nan ta yarda da gaske takeyi sedai kamar yanda ta fada zeyi wahala mutane su yarda da ita har suyi mata uzuri amma yardar Allah ita Umaimah tafi buqata a yanzu domin idan harta gyara tsakaninta da Mahaliccinta komai zezo mata da sauqi sedai kamar yanda ta fada haqqin wadanda ta cutar baze barta ta samu nutsuwa ba harse ta saukeshi.

"Dan Allah Maman Asad zan roqeki Alfarma, karkice ba zaki mun ba. Banida hanyar da zan hadu da Khalil ko wani cikin Ahalinsa kinga bana fita sannan bani da waya kuma koda ma ace na gansu bani da kwarin guiwar da zan iya kallonsu. Kiyi mun wannan alfarmar koda ace shine abu na qarshe da zaki mun saboda Allah ki nema mun afuwa a gurin Khalil da Hajiyarsa a matsayinki na Jinina. Ina so na roqi Mama ko Abba suyi mun wannan alfarmar amma nauyi da kunyarsu baze barni ba, sun roqeni dana kwantar da hankalina a baya na toshe kunne na nayi abinda nayi a yanzu da komai ya rincabemun bazan iya roqarsu da su nema mun sassauci a gurin wadanda na batawa ba iyakar alfarmar da sukayi mun ta yafe mun muzgunawar da nayi musu ta isheni".

Shiru Maman Asad din tayi tana kallonta saboda abinda ta roqetan yayi mata girma ba kuma tajin ita kanta tana da qarfin guiwar da zata je nemawa Umaimah yafiya a gurin Khalil ko Hajiya. Iyakar murje idon da sukayi suke neman Yaran ya isa ba zata so ta tado da abinda ya shude ba ballantana radadin abun ya waiwayesu har a qarasa gutsire yar guntuwar alaqar da ake riritawa a tsakani. Umaimah ta kama hannunta idonta na zubda hawaye tace
"Nasan abin da wahala amma idan na mutu da haqqinsu nasan Allah baze dubeni ba Yah Hajiyayye. Na cutar da Khalil matuqa na sani kuma ba lallai ya yafemun ba amma dukda haka ina so ki gwada nema mun wannan alfarmar su yafe mun nauyin da nake ji nasu akaina ya ragu ko zan samu nutsuwar da kuke buqata ku ganni a ciki".

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kalli Umaiman tace
"Ban daukar miki alqawari ba amma zanyi bakin iyawata dukda ni kaina inajin nauyi da kunyar abubuwan da suka faru. Tun gabanin haduwarki da Khalil na zauna da Hajiya ta kuna daukeni kamar yarta irin yanda ta riqeni yasa har tayi sha'awar hada jini damu ta dage har seda ta tabbatar da qulluwar aure a tsakaninki da gudan jininta. Duk abubuwan da kika aikata Hajiya bata taba kware miki baya ba. A gabanta kin zageta amma tayi miki uzuri har Mama ta umarci Khalil ya rabu dake Hajiya bata so haka ba a yanzu da nake miki magana tunda muke turawa a daukar Mana Yayanki ko a fuska Hajiya bata taba nuna wani abu ba tayaya kike so naje gurinta Umaimah na sake tado mata da abinda ya wuce wanda na tabbatar da ba mantawa tayi ba tsabar dattako da karamci irin nata ne yasa ta mayar da komai ba komai ba.
Zanso ki bar komai a yanda yake kici gaba da addu'a da neman yardar ubangiji muma muna tayaki in sha Allahu komai ze daidaita Umaimah kinji"
Chapter 244 · 0% Book details