← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 154 OF 267

Sashe 154

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nan yayi sallar Isha, be bar gidan Maman Mansur ba se gurin Tara saboda hira da suka zauna tana ta tuna masa da lokacin quruciyarsu, ya kira Mansur ya hadasu ya sake yi mata bayanin magungunan seda Umaimah ta kirashi akan sun dawo taga baya gida kafin yayiwa Mama sallama ya tashi tafiya tana ta saka masa Albarka da godiyar siyayyar daya yiwo musu.

A waje daya fita ya lura da an dawo da wuta, har ya bude motarsa ya kashe ya koma. Mama na tsakar gida ta fito shanya Hijabinta da ruwa ya zuba akai tace
"Aa, Khalil ashe baka tafi ba mantuwa kayi halan"
"Aa Mama naga an dawo da wuta ne shine nace bari na dawo na kashe muku injin, ina yarinyar take na nuna mata yanda ake kunnawa koda ace sun qara daukewa" Khalil din ya bata amsa. Seta daga murya ta kwalawa Humaira kira ta fito da sauri tana amsawa, Khalil ya bita da kallo ganin yanda ta fito itama ganin sa tsaye yasa ta juya da saurin gaske har tana shirin faduwa Mama nace mata tabi a sannu ta shige dakin.

Hijabi ta zumbulo kan Doguwar riga me hannun vest dake jikinta dan ko dan kwali bata dauko ba ta fito amsa kiran Maman san sam batayi zaton wani ya shigo gidan ba. Kanta a qasa kamar tana gaban suruki ta qarasa tana cewa Maman gata.
"Yayanki ne yace yace kizo ya nuna miki yanda ake kunna Inji da kashewa saboda wata rana, banda ma sakarcinki abinda sukace muqulli ake murdawa ina wahala a ciki" Maman ta fada tana nuna mata Khalil daya shige inda Injin yake se tabi bayansa tana tafiya a hankali. Itafa tsoron taba Injin take, tunda wani dan Unguwar yaje kunna inji yayi bindiga wuta ta kama har jikinsa ya qone sosai har yanzu be gama warkewa ba kusan fin shekara shiyasa take baya baya da sabgar Injin ko Yaya Habib yace taje ta haska masa daga baya take tsayawa.

"Ki dago qafa Malama sauri nakeyi fa" taji muryar Khalil akanta se ta daga qafar ta qarasa. Daga bakin gurin ta maqale tana leqensa, Khalil kalleta ganin yanda ta tsaya kamar wadda take tsoron wani abu ya kamata be san lokacin da ya ja tsaki ba yace
"Da Allah ki matso ko wani abun ne ze kamaki a nan din?"

Cikin sanyin murya kamar me shirin kuka har tana jan qafafunta baya tace
"Ni tsoro nakeji bana son zuwa kusa sa Gen" se kawai ya saki baki galala yana kallonta tsabar mamaki wai tsoro takeji Kura ne ko Zaki da zataji tsoronsa?
Hadiye bacin ransa yayi yace mata
"Ki matso babu abinda zeyi miki" ya fada yana kallonta. Seda ta zuba masa idanunta da suke masa wani iri idantana kallonsa kafin ta matsa kusa dashi din kadan a haka ya nuna mata inda ake Kunnawa da kashewa da inda zata danna wuta ta kawo kafin ya matsa yace tazo ta kashe Injin. Yana kallon hannunta har rawa yake ta murda muqullin ta kashe, Change over bashi da tsaho dan haka yace ta daga ta mayar dashi Nepa bata musa ba jikinta na rawa tayi abinda yace dan ya tsare fuska ganin hasken Nepa ya gauraye gidan yasa ta sauke ajiyar zuciya Khalil ya kalleta yace
"Ba gashi nan ba yanzun meya cijeki da zakice kina jin tsoro?"

Bata amsa shi ba se kanta data sunkuyar tana wasa da zoben hannunta ya wuce ya barta a gurin bata ma lura ba seda ta jiyo shi yanayi Mama sallama kafin taja qafafunta ta wuce itama.
"Seda safe" ta fada daidai ze gota ta ya fita, ya waiga ya kalleta kawai ba tareda ya amsa na ya fice daga gidan se tabi bayansa ta kulle qofar ta dawo tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tayi wani abun ta cire Hijabinta ta aje kan kujera tana kallon Mama tace
"Mama shine baban Mu'ayyad ko?"
"Oh ni Humaira gani daya kin riqe sunan yaron nan ni wallahi mantawa nakw shiyasa kawai nake ce masa ina su Alhaji amma ke caraf kin riqe, me yasa to baki tambaye shi yana ina ba?"

"Tab ni tsoronsa ma nakeji wallahi Mama ina kallonsa se naji gabana ya fadi tun lokacin da yake zuwa gidan nan gun Yah Mansur" Humairan ta fada se Mama ta girgiza kai tace
"Ai kowama tsoronsa kikeyi ke daman ki wuce ki debo abinci kici toh".
Miqewa tayi ta zubo tuwon ta dawo taba ci tana yiwa Maman zancen Mu'ayyad wai tana so taga yaron yanzu tasan ya girma sosai. Tun lokacin da Umaimah tajewa Mama yawon arba'in Yaron ya shiga ranta sosai, tayita nacin suje gidansu da Mama amma taqi sedai suje gidan Hajiya. Kwanan nan ma da sukaje yiwa Hajiyar murnat sabon gida seda ta tambayi Habiba Mu'ayyad din tace yana gidansu Umaimah a sannan basu rigada sun tare ba ita yanzun ma seda tayi noyyar tambayar Khalil din kawai yanda ya hade rai ne yasa ta kasa masa magana se wani muzurai yakeyi kamat wanda akayiwa laifi.

Khalil kuwa be qarasa gida ba kusan goma da rabi dan ya tsaya ya siyawa su Umaimah Gasashshen nama data ce ya taho musu dashi da fura. Hajiya ya fara kaiwa nasu har sun kwanta Habiba ta karba ta saka a Fridge yaran ma sunyi bacci kafin ya wuce part dinsu. A falon qasa ya tarar da Umaiman tana kallon wani hausa film a Arewa 24. Tayi masa sannu da zuwa bayan ta karbi ledojin daya shigo dasu ta wuce kitchen shi kuma ya hau sama dan yayi wanka. Sanda ya sako harta sake dumama Naman a Micro wave ta zuba a plate tana zaune tana shan fura ya zauna kusada ita ta miqa masa furar yace Aa a qoshe yake shi yaci tuwo a gidan Mama.

Hira sukeyi dukda rabin hankalinta nakan kallon da takeyi seya tashi ya shiga kitchen ya dora qaramar tukunya akan Gas bayan ya zuba Spices din Shayi ya kunna. Yana tsaye yana jiran ruwan ya tafasa, haka kawai ta fado masa a rai, a cikin kansa yake jin muryarta me sanyi tana masa yawo yaja tsaki to akan me ze wani ringa tuna yarinyar kuma.

A Mug ya juye ruwan bayan ya tasafa ya zuba sugar cubes ya koma falon, Umaimah data gama cin Namanta da fura ta hada sauran zata kai kitchen din ya fito se ya karbi farantin naman ta wuce ciki ta ajiye sauran kowanne a muhallinsa. Kadan yaci Naman ya shanye shayin gaba daya ji yake kansa yana neman yayi masa ciwo saboda wani tunanin shirme da kwakwalwarsa take kawo masa na yarinyar, meye hadin sa da ita da zata ringa fado masa a rai haka kawai saboda son ta hana shi sukuni. Har sukaje kwanciya ya rasa abinda yake masa dadi lokaci lokaci yakan saki tsaki Umaimah dake saka rigar bacci ta kalle shi tace
"Wai nikam lafiya kake ta tsaki kai kadai"?

Tsakin ya kumayi kafin ya nufi bandaki yana ce mata babu komai. Bata tsawwala ba dan yanzu kaffa kaffa take da duk abinda ze saka ya sake birkice mata. Tana kwanciya ko minti biyar batayi ba bacci ya dauke dan yanzu haka take data aje haqarqarinta a qasa bacci ze kwasheta har mamakin irin wannan bacci haka takeyi.

Khalil kuwa bayan yayi wanka ya kwanta sam barci ya gagara zuwar masa. Abin daga haushi se ya koma bashi Mamaki irin yanda haka kawai yarinya ke neman shiga rayuwarsa ta hanashi zaman lafiya.
Tsaki ya sake ja a karo na babu Adadi ya juya kwanciyarsa yana rufe ido, hotonta ya gani sanda ta fito babu Hijabi a jikinta. Doguwar qirar jikinta da babu wani abu da zece ya rudeshi da har ze saka ya ringa tunaninta tanayi masa gizo se ya miqe ya wuce bandaki ya dauro Alwala ganin ya kasa bacci.

Nafila yayi tayi har seda bacci yaci qarfinsa kafin ya kwanta. Da Asuba dakyar ya iya farkawa daga baccin da yake cike da mafarkin Humairah. Zuwa yanzu lamarinya ya fara bashi tsoro tunani yakeyi anya ba Mayya bace yarinyar take neman lashe masa kurwa? Idanba haka ba meye darin gaminsu da zata zo masa a mafarki, to koma dai yaya ne yafi qarfinta ba zata ci galaba akansa ba ze kuma sake dagewa sa Addu'a da kuma neman magani yana zaman zamansa Mansur ya ja masa ko a ina ma suka samota oho dan ya ya tabbatar duk yanda akayi suma basu san Mayyar bace shiyasa suke zaune da ita.

Haka yaje ya dawo daga masallaci yana ta ta'ajibin lamarin Humaira a ransa. Bacci ya sake komawa dan rashin kwanciya da wurin da beyi ba ya saka baccin be ishe shi ba. Da yake Asabarce ne tashi da wuri ba har gurin goma na safe. Umaimah bata dakin sanda ya farka ya dai ji qamshin turarukanta alamar anan tayi wanka ta shirya dan haka shima yayi wankan yana Jin cikinsa na qugin neman abinci. Falo ya fito, nan ya tarar da Mu'ayyad da Bibi suna cin Doya da Ketchup suka tashi da gudu suka fada jikinsa ya dagata sama ya riqe hannun Mu'ayyad din suka koma inda suka tashi.

A tare suka gaida shi ya amsa yana tambayarsu Umaimah Mu'ayyad yace masa tana gurin Hajiya. Da kansa ya sauka qasa ya debo abin karyawa ya dawo suka qarasa da yaran.
"Dady yau kacewa Anty Habiba ta kaini gidansu Humairah" Bibi data kwanta a jikinsa ta fada. Wani duka qirjinsa yayi jin sunan data ambata. Idan be manta ba haka yaji Hajiya ta kirata jiya nan take tunanin yarinyar da yayi yaqi dashi dakyar ya sake bijiro masa. Maganar da Mu'ayyad yakeyi ce ta dawo dashi daga tunanin daya tafi yana cewa

"Dady itafa Humairan bata zuwa nan gidan sw Bibi ce kullum zata ce akaita shine Anty Habiba tace itama ta dena zuwa gidansu".
Rigima Bibin ta saka akan se an kaita gidansu Humairan, sunan kadai da take ta maimaitawa faduwar gaba yake haifar masa. Umaimah ta shigo ta tarar dasu ita ta lallabata akan ta bari seda yamma akaita gidansu qawar tata yanzu basa nan da haka suka tattara suka wuce bangaren Hajiya.
Chapter 154 · 0% Book details