← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 267

Sashe 93

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waigawa Khausar tayi iya hangenta bata ga Khalil ba babu kuma ma wanda hankalinsa yake kanta, Muryar wanda ya kawo musu abinci taji daga sama yana cewa
"Hajiya kin gama ne zamu gyara gurin wasu zasu zauna" bata iya magana ba ta daga masa kai kawai, ka garindaukar kwanukan ya ture mata wayarta data ajiye kan Table din cikin sauri ya dauko ya miqa mata yana bata haquri ta harareshi kafin ta karba ta jefa a jaka, jiki babu kwari ta fice daga gurin, Adaidaita ta tare ta hau, bata samu nutsuwar baza'a tareta a sace ta ko a kwace mata waya ba seda ta ganta a Office dinsu. Tana zuwa ta tararda Mata biyu da suka zo shigar da qara, Ogarsu tace taji dasu dan haka suka shiga ciki ta ajiye jakarta ta dauko wayar da suke recording ta kuna ta fara tambayar matar.

Mijinta ne yake dukanta shine data gaji yau da yazo dukan nata ta kwada masa Tabarya ta gudo, dayar da sukazo tare qawarta ce kuma daman ita ta bata shawarar ta nemi madoki a kusa dik randa ya sake yunqurin dukanta ta rama toh kuma an samu kuskure tana rafka masa tada ya fadi a gun bata da tabbacin yana da rai ko ya mutu shine ta gudu qawar tace suje Human right ta shigar da qarar yanda koma menene ya faru abin ze zo da sauqi.

Seda ta gama nadar komai taje ta kaiwa Ogar tayi mata bayani se tace ta tura mata Matan. Kujerar Hadiza da  babu kowa a kai ta kalla tayi murmushi a fili tace
"Tukunnama, se kin rasa komai da kike taqama dashi a duniya ai duk wanda yaci tuwo dani miya yasha".
Tunawa da barnar da tayi kuma ya sakata miqewa da sauri ta suri jakarta da sauran tarkacenta ta fice ba tareda tayiwa kowa sallama ba kaitsaye gidan su Shema ta wuce dan tana so su tattauna.

Khalil
Seda ya tabbatar da Khausar tabar gurin dan akan idonsa ta hau Napep kafin ya fito daga gurin daya boye ya koma ciki, kiran Hafiz ne ya shigo masa ya daga daga can bangaren Hafiz yace
"Yaya, an dace kuwa?"
"Yanzu nake komawa bata dade da barin gurin ba" Khalil ya bashi Amsa.

Gurin yaron daya kai musu Abinci ya qarasa yana zuwa ya dauko masa waya ya miqa masa ya karba yana murmushi tareda yi masa godiya. Kudin da shi kansa be san nawa bane ya zaro daga Aljihunsa ya bashi kafin ya juya ya hau motarsa ya bar gurin a zuciyarsa yana fatan Allah yasa qarshen matsalar kenan. Jin kansa yakeyi kamar an dora masa dutse saboda Nauyi da ciwon da yakeyi masa, haka kawai yarinya na neman ta dora Masa Hawan jini babu gaira babu dalili.

Daga gurin kai tsaye office dinsu Hafiz ya koma, ya miqa masa wayar yana cewa
"Gata, amma Ya akayi kayi wannan tunanin?"
Hafiz ya karbi wayar yana murmushi yace
"Na gaya maka wannan ai qaramin aiki ne, da nayi niyar na tura ne a karba a hannunta se kuma kawai naga ma ga hanya me sauqi kuma gashi an dace, kaga qarin Sa'a wayar tata ma babu Security akai amma dai wannan wawiyar yarinya ce ma ita haka ake Blackmailing din babu wani shiru babu matakan tsaro"

Bincike ya shigayi a wayar bayan ya saka Sim din a flight mood yanda kira baze shigo ba. Messages ya shiga, chat din dake sama ya bude ganin message din da aka turo mata
'Bani dasu kuma karki kuskura ki sake nemana idan ba so kike ranki ya baci ba' lokacin da aka turo ya duba yaga suna tareda Khalil ma se ya bude Saqon ya fara bin sauran saqonnin da sukayi musaya da me Number shine wanda yayi mata aikin hada hoton kuma a nan ciki ya samu tabbacin ita kadai ya turawa kamar yanda ya fada shima ya goge saboda haka ne qa'idar aikinsa baya ajiye hoto ko video bayanya hada maka saboda tsaro.

Seda suka bincike wayar tas daga suka samu tabbacin mutum biyu ta turawa da Hoton daga Khalil se Hadiza se kuma mutum daya da tayi saving da 'Best' ita kuma da ita suka shirya komai dan ita ta bata shawarar aikata hakan ma ita a son ta Akan Nude Video za'a dora fuskokinsu Khausar din tace Aa.

Bayan sun gama binciken nan take Hafiz yayi formating memoryn wayar gaba daya ya kuma bi duk inda yasan za'a iyayin back up ya goge shima. Miqawa Khalil wayar yayi yana cewa
"Case close hankalinka ya kwanta ka maida qibarka kaga yanda fuskarka ta zabge kuwa kamar wanda ya shekara yana jinya ni gaba daya ma ka bani kunya se kace na Namiji ba haba mana"

"Kai bazaka gane ba, yanzu dai tunda Allahya taqaita shikenan amma idanda ace Umaimah ta kai ga ganin hotunan nan, inaga sedai na dawo nan office din ku bani mafaka" dariya sukayi gabadaya Hafiz yace
"Mata mata wato na ko ina dai haka suke da kishinnan, ni fa ina ganin babu Wanda yakai tawa yar darun" Khalil yayi saurin tare shi da cewa
"Na tabbata ko yatsanta gidanabata kama ba kawai Allah yaci gaba da rufa mana Asiri"

"Amin, yanzu ya za'ayi da wannan wayar" Hafiz ya fada, Khalil ya daga kafada yace
"May be idanna samu wandaze kai mata a mayar mata da abarta ko"
"Haba dai taci banza ma kenan ai an musanya maya wayarta, wannan 12 pro ce ma aka bata pro max ai kaje da ita kawai ka rage kudinka" Hafiz ya fada, Khalil ya girgiza kai yace

"Ko nawa na kashe bazanji komai ba tunda na samu biyan buqata" cewar Khalil se Hafiz ya maida wayar kan Table dinsa yana cewa
"Kaga Allah yaci dani daga sama na samu waya"
"Shikenan kuwa ka samu ka riqe kawai" Khalil ya fada yana miqewa, kiran La'asar da akayi ya saka dole ya jira yayi sallah a gurin kafin ya tafi. Seda ya hau hanya ya tuna da Umaimah daya kai gida tun  safiya kuma ko shiga ciki beyi ba yace seya dawo lallai wani tashin hankalin ya girmi wani yanzu kuma se yazo yaji da nata tunda ya gama da wannan.

Hadiza ya kira ya shaida mata halin da ake ciki, Hamdala ta ringayi tana qarawa tace
"Nagodewa Allah nagode maka Khalil shiyasa bazan taba dena kukan rasa jajirtaccen Namiji irinka ba, ina kuma Addu'a idan da rabo a tsakanin mu Allah ya gaggauto dashi kusa"
Da 'Amin' ya amsa mata kafin sukayi sallama ya kashe wayar tausayinta yana tsarga masa. Gidan hajiya ya tafi ta sa shi gaba da tambayar meya same shi taga ya rame haka yace mata babu komai aiki ne, a can yaci Abincin rana dabe iya ci a waje ba. Seda yayi sallar Isha sannanya tafi dauko su Umaimah yana tunanin yanda zasu qare da ita kuma.

Khausar
Tana isa gidan su Shema a tsaitsaye ta gaida Mamansu ta shige dakin Sheman tana cewa
"Qawata Na shiga uku, yanzu ya za'ayi?"
"Kiyi dagaske har Mama tajiyo ta san me kika qulla zaki wani shigo tun daga waje kina wa mutane terere" Shema dake kan gado ta fada, se Khausar ta rufe baki da hannunta tace

"Au wlh kaina ne ya dauki zafi na manta" ta zauna kusada ita tana sake cewa
"Ki bani mafita me ya kamata nayi yanzu kafin abubuwa su cakude mun?"

"Mafita daya ce da zata saka ya shiga taitayinsa kawai ki turawa Matarsa" Shema tta fada ba tareda ta kalleta ba Khausar tace
"Matarsa? Kina ganin hakan dabara ce nafa gaya miki yanda yake son matar nan tasa da kuma irin haukan kishinta da na samu labari idan na tura mata baza'a samu matsala ba?"

A hasale Shema ta kalleta tace
"Toh ke ina ruwanki kece a cikin hoton ko kuma ke zatayiwa haukan da kike jin tsoro? Kinga ni idan ba zaki ringayin abinda na gaya miki ba kije can ki qarata da yawarki karki kuma nemana"

"Haba Qawata abin be kai haka ba ai kawai dai ina jin tsoron kar wani abu ya faru nice sila yaqi aurena a qarshe kuma dai kinga abinda nake yiwa fafutuka kenan" Khausar din ta fada jiki a sanyaye se Shema ta sake galla mata harara tace
"Toh ai seki zauna kinga kinyi asarar kudinki da lokacinki a banza da wofi, kuma ki tashi ki fita karki sake kirana wallahi duk abinda ya faru"

"Aa baza'ayi haka ba yanzu nan zan tura mata bari kiga" ta fada tana zaro wayarta daga jaka. Budewa tayi sabanin hotonta dake kan wallpaper se taga babu daman tun sanda Waiter dazu ya miqo mata ta lura amma saurin da takeyi ya saka bata mayar da hankali ba.

WhatsApp ta shiga nema bata gani ba, se a sannan hankalinta ya dawo jikinta ta lura da wannan wayar kamar babu komai ma a cikinta. Miqawa Shema wayar tayi tana cewa
"Ke tayani dubawa, daidai nake gani ko duk rudewar ce"

Shema ta karba ta duba seta kalleta tana cewa
"Ya haka wayar babu komai akai? Allah yada ba a garin rawar jiki kika yi Restoring nata ba, ke kamar ma fa babu Sim akai" ta sake fada ganinbabu alamar Network. Wurin kira ta shiga ta loda number ta ta danna yaqi tafiya seta miqa mata tana dariya tace

"Tab lallai mutumin nan a shirye yake, ni daman nayi mamakin da ace wai zaku hadu keda bakya aiki da kwakwalwarki kika kwashi jiki kikaje, gashi nan ya nuna miki ya fiki iya wasa chanza miki wayar yayi".

Hannu biyu Khausar ta dora akai tana zare ido, se kuma ta tuna da Khalil ya rigata tafiya,
"Anya, bashi bane saboda ya rigani tafiya kuma se bayan ya tafin na kiraki"
"Toh a ina aka canza miki? Daga gurin se ina kika tsaya?" Shema ta sake tambayarta. Khausar da hankalinta idan yayi miliyan ya tashi tace

"Ban tsaya ko ina ba se office kuma ko a can ban fito da wayar ba sannan idan Khalil ne dole zan sani dan tunda muka zauna har ya tafi wayar tana gabana ko tabata beyi ba sedai idan..."
Chapter 93 · 0% Book details