← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 267

Sashe 156

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallamar Mama ce ta cece shi daga dan banzan surutun Habibu, har qasa ya durqusa ya gaidata Mama ta amsa tana tambayarsa daga ina haka da yamman nan, qeyarsa ya sosa dan besan me zece mata ya kawo shi ba. Saboda yanayin aiki be fiya samun damar leqa Maman ba sedai kamar in Mansur ya yi saqon da dole shi ze je da kansa in ba haka ba kuwa ko Alkhairi yayi niyyar yi mata kai tsaye Habibu yake kira ya bashi gashi yanzu ko sati biyu ba'ayi da zuwansa ba ya sake komawa dole Maman tayi mamaki ai.

Sallama Humairah tayi ta shiga falon, ya daga kai ya kalleta ta dena kukan amma fuskarta a daure ta wuce can kusa da Maman ta zauna
"Yawwa Habibu ka kyauta. Yanzu saboda Allah daman da nace maka da an fara Rijistar Jamb ka gaya mun ko baka gari zansa akai Humaira tayi shibe kaqi fada? Se yanzu a gidan Hajiya Asabe nake ji wai gobe za'a rufe. Ai kuwa yanzu zaka tashi ka kaita tayi" Mama ta fada se Habibu yayi saurin cewa

"Nifa Mama ban san anfara bane kuma ma wannan yarinyar nagaya miki tayi qanqanta da zuwa Jami'a wannan shekarar gata da shegen sanyi a haka zatayi karatun"

"Firinji ce qarewar sanyi. Na gama ganoka dai baqin ciki kakeyi baka shiga Jami'a da wuri ba tazo ita zata shiga da quruciyarta to koma menenr yanzu ka tashi ka kaita kar dare yayi ai ance ana samun Cafe yanzu" Mamanta sake fada tana hararar sa, Habibu ya kumbura baki yana hararar Humaira dake masa dariya daga nesa Mama ko se sababi take tana gayawa Khalil yanda Habibun baya so Humaira ta tafi Jami'a.

Kamar wanda aka fizgi maganar daga bakinsa yace
"Ta shirya ni se na kaita yanzu tayi".
Da sauri ta daga kai ta kalleshi, Mama ko ta washe baki tana cewa
"Aa daga zuwa ziyara se na hadaka da aiki shidin dai shi ze rakata ko baya so"

"Aa Mama babu komai ai daga nan gida zanje ba wani guri ba se na kaitan tunda kinga baya son zuwa kar su tafi yayi ta yi mata fada a hanya ko ya sakata cike abinda bashi take so ba tunda beyi niyya ba" Khalil ya fada se Mama tace
"Ai kuwa kamar kasan qudurinsa kenan, ina jinsu tace ita harkar zane zane take so wai bazatayi ba kamar shi zeyi mata karatun. Ni na rasa wannan hali na Habibu a inda ya dakko shi wallahi"

"To haka kawai yarinya duk kin wani fi sonta akan kowa" Habibun ya fada cikin qunquni yana miqewa jin Khalil yace ze kaita. Tashi yayi shima yana cewa
"Ta sameni a waje idan ta shirya" yabi bayan Habibun suka fita.
A jikin motarsa ya jingina a zahiri kallon Habibu dake masa hira yake amma a badini ya lula cikin tunanin abinda yayin.
Wai meya shiga kansa ne da yasa yake wasu abubuwa daya kasa gane kansu?

Hangota yayi ta fito daga gidan sanye da Dogon Jilbab kalar dark blue daya qara fito mata da hasken Fatarta haka tsahonta ya fito sosai gabansa ya fadi, saurin bude motar yayi ya shiga yana cewa Habibu
"Shigo muje"
"Aa Yaya kuje kawai, ni kallon kwallo ma zamu tafi yanzu" Habibun ya bashi amsa yana shirin juyawa. Hannu ya saka a Aljihu ya zaro kudin da besan adadinsu ba ya miqawa habibu daidai nan ta iso gurin taja ta tsaya kanta a qasa kamar me qirga duwatsun gurin.

"Se an ce ki shiga motar ko? To ki kwana a tsaye. A haka zakije kinawa mutane wanan salo salon wallahi Yah Khalil inta bara maka lokaci ka barota a can kawai kayi tafiyarka" Habibu ya fada yana harararta ita dai bata tanka masa ba ta kama murfin gidanbaya zata bude ya sake katseta da cewa
"Wato ga Driver kin samu, kefa yarinyar nan kin samu guri da yawa wallahi"

"Nifa na dauka da kai za'aje" ta fada kamar zatayi kuka, Khalil dake zaune ya kalli Habibu yace
"Ka rabu da ita haka mana, shiga mu tafi".
Gaban motar Habibu ya bude mata saboda cin zali harda ranqwashinta.

Tafiyar kurame sukayi, ita dai ta riqe Takaddunta a hannu ta sunkuyar da kai ga uban Ac daya qure da qamshin turarensa sun dameta. A bangaren Khalil kuwa yanda kasan an bame masa baki da kwado haka yaji duk tarin tambayoyin da warning din daya shirya kora mata akan ta qyale kurwarsa ta huta ji yayi sun shafe se ma wata nutsuwa da yaji ta daukar masa sanadiyyar zamanta a kusa dashi. Lokaci lokaci yake waiwayawa ya kalleta har suka Isa wani babban Cafe yayi parking motar kafin ya fita Humaira ta bishi a baya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki dan ita wannan hade fuskar tasa tsoro yake bata.

Basu bata lokaci a gurin ba akayi mata duk abinda ya dace dan suna shiga ya hadata da ma'aikatan gurin ya koma gefe ya tsaya har aka gama kafin suka gaya masa kudin ya biya. Wanda yayi mata aikin ya kawo masa takaddar da aka fitar mata ya karba yana gaya masa ranar da zata dawo dan ta san rana da lokacin da zata rubuta Jarabawar. Seda suka ci rabin hanyar komawa gida kafin ya kalleta yace
"Wane course kika cike?"

Daga kai tayi ta kalle shi ganin shima itan yake kallo yasa tayi saurin sada kanta qasa tana juya zoben hannunta muryar ta na dan rawa tace
"Fine art"
"Fine art" ya maimaita be qara ce mata komai ba yaci gaba da tuqinsa har suka kusa shiga layinsu kafin sake kallonta yace
"Ina wayarki?"
"Banida waya" ta bashi amsa. Se ya kalli hannunta itama hannun ta kalla kafin yayi magana tace
"Wayar Mama ce ni Yah Mansur yace ba yanzu za'a siya mun waya ba".

"Da layinta kikayi rijistar kenan" ya fada ba tareda ya kalleta ba seta daga masa kai kafin da sauri ganin baya kallonta tace
"Eh, shiyasa ta bani wayar ai".

Gani tayi ya dauke hanya daga komawa gida yayi wani gurin daban, ko motsi batayi ba har suka isa qofar wani shago ya kashe motar yaceata yana zuwa. Be dade a ciki ba ya fito da Leda fara qarama ya shiga motar suka juya zuwa gida. Suna isa ana kiran Sallar Magriba dan haka be shiga ba ya miqa mata Ledar daya fito da ita daga shagon dazu tareda kudi dubu goma yace ta kaiwa Mama. Ko saurar godiyar data tsaya yi masa beyi ba ya juya kan motarsa. A kan hanya ya samu masallaci yayi sallah, se a sannan ya duba wayarsa da tunda ya fito daga Office be sake dubata ba. Tarin Missed calls ya gani s sannan ya tuna da ya sakata A Silent da zeyi sallar Azahar kuma ya manta be cire ba.

Kiran Umaimah ya fara bi, tambayarsa tayi yaushe ze dawo gida dan ta fita amma tana hanyar dawowa. Sabon salon data tsiro dashi kenan se ta fita inda zata sannan zata sanar masa kuma yasan baze wuce gidan wannan qawar tata da sam yaqi Jini ba shi ya rasa ma tsakanin ita da Rufaida wacce yafi tsana a cikinsu. Gaba daya matar kalar munafukai ne da ita ga Ladabi da kana gani kasan bana Allah da Annabi bane, ya rigata komawa gidan, ta shigo da tarkacen kayan Jarirai ta baje masa su wai a gidan Safina ta siyo maqociyarta ce ta kawo shine ta diba.

Har ya kwanta saqo ya shigo wayarsa dake hannunsa. Baquwar number ce. Bude saqon yayi ya karanta abinda yake ciki
"Nagode kwarai Yaya Khalil, Allah ya saka da Alkhairi ya qara arziqi. Mama tace ayi maka godiya Allah ya raya su Mu'ayyad".
Ya maimaita karanta saqon yafi sau Goma kafin ya gane daga inda yake.
Inda ta samu number sa yake mamaki koda yake baze wuce a wayar Maman ba. Maida wayar yayi ya ajiye kamar wanda aka tsikara kuma ya janyota ya sake bude saqon. Number da ta turo yayi saving da 'Fine Art' kafinya goge text din dai dai nan Umaimah ta shigo cikin shirin kwanciya. Yana jinta tana mitar qafarta na ciwo kafin ta koma kan maganar kudin kayan data dauko. Be ko tanka taba yaja bargo ya rufe jikinsa alamar bacci zeyi. Tun bayan da sauka dawo shiri take neman yanda zata samu kudi a hannunsa shi kama ya tsuke bakin Aljihunsa tsaf ya qudurce a ransa kudi indai ba akan abinda ya zama dole ba ya dena bata. A da da yake bata dinma bega abinda ta tsinana dasu ba balle yanzu da shida kunnensa yaji tana shirya yanda zata samun kudin da besab abinda zatayi dasu ba.

Da safe yana zaune kan Dining yana jiran Umaimah da take soya masa kwai ta gama dan Ruqayya bata nan, anyi mata rasuwa ta tafi garinsu kwana uku kenan. WhatsApp ya shiga, abinda be fiya dubawa ba Status haka nan yau yaji sha'awar dubawar yana shiga kuwa da status din 'Fine Art' ya fara cin karo. Waqoqin hausa ne na soyayya ta dora a jere guda uku, se hoton wani da aka rufe fuskarsa da Emojin Zuciya ta rubuta 'Haskena' a qasan hoton. Haka kawai yaji ya qware da ruwan Tea daya kurba ya shiga tari har seda Umaimah dake kitchen ta fito ta bashi ruwa tana masa sannu. Seda tarin ya lafa masa kafin ya miqr tsaye idonsa yayi jajir saboda kwarewar da yayi ya sabi jakarsa dake kan kujerar kusa dashi Umaimah ta kalleshi da mamaki tana cewa
"Naga ka miqe, ina kuma zakaje baka karya ba?"
"Ki barshi kawai na qoshi, da akwai kudi na ajiye miki akan Dressing Mirror na zuwa Asibitin" ya bata amsa kafin ma ta sake magana ya kusa kaiwa qofa se kawai ta bishi da Adawo lafiya a ranta tana mamakin abinda ya harzuqashi haka dan fuskarsa da Muryar sa sun nuna fushin da zuciyarsa take ciki.
Chapter 156 · 0% Book details