← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 189 OF 267

Sashe 189

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 68

JALINGO
Ana kiran Sallar Magriba su Baba Abu suka isa gidan Alhaji Muhammad Jibril wanda yake matsayin yaya ga Mahaifin Humaira Marigayi Malam Nura Jibril kuma qani ga Mama Hauwa. Sun rigada sun san da zuwansu dan haka sun tanadesu, a matuqar gajiye dattijan suka zauna a katafaren falonsa inda aka ajiye musu kayan abinci nau'ika kala kala, ruwa kadai suka sha suka fita zuwa Masallacin dake qofar gidan a can sukayi sallah kuma a sannan suka fahimci Ahalin gaba daya suna zaune a unguwa daya ne dan tun a Masallin Alhaji Muhammad ya fara gabatar musu da yan uwansa wanda kamannin da suke kadai ya isa ya gaya maka alaqarsu mutane masu karamci.

Cikin gidan suka koma bayan sunyi Sallah, Basa tare da yunwa sedai gajiya dan haka suka zauna a falon aka shiga sake gaggaisawa. Bayan gabatar da juna Alhaji Musa wanda shine babba a gidansu Maman gaba daya ya fara magana da cewa
"Hauwa ta rigada tayi mana bayani akan shi manemin Aisha da kuma zuwanku, bamu da buqatar sake yin wani bincike akansa saboda a duniya mu zamu fara bada shaidar irin tarin qaunar da Hauwa takeyiwa Aisha tun mun kuma san ba zata taba yi mata zabin Mijin da bana gari ba, amma dukda haka domin mu sauke haqqin da Allah dora mana mun sake bincika wanene Ibrahim is aka sake yin wani katari ashe na gida ne domin Abokin aikin dan uwan mune gashi nan" ya Nuna Alhaji Muhammad se Alhaji Muhammad din yaci gaba da magana yana murmushi yace

"Tabbas Khalil Abokina ne kuma qanina nafi shekaru biyar da saninsa mun hadu a qasar Africa ta Kudu lokacin da wani aiki ya kaimu daga nan alaqa me qarfi ta qullu tsakaninmu saboda kasantuwar harkar neman abincinmu daya, munyi kwangiloli da yawa tare kuma ya kasance mutum me Amana da kyakykyawar mu'amala shi yasa nayi matuqar farin ciki a lokacin dana fahimci shine manemin auran Yar dan uwana".

"Toh masha Allah haqiqa munji dadi kwarai da wannan shaida da kuka bayar akan Dan mu ina kuma me qara baku tabbacin yarku ba zatayi dana sanin auran Khalil ba domin mutumin kirki ne ku da kanku da sanin nesa kukayi masa kun shaida hakan, sedai muyi fatan Allah yasa su zama abokan arziqi na har abada Allah kuma ya hada kawunansu" Alhaji Garba ya fada kafin yaci gaba da cewa
"Ina ganin idan har babu damuwa zamu iya gabatar da abinda ya kawo mu saboda yanayin jiki da akwai gajiya tattare damu mu samu mu tafi masauki mu huta saboda Asubanci muke so gobe mu qarayi mu juya Kano, Alhaji Abubakar Bismillah".

Baba Abu ya zura hannu a Aljihu ya ciro kudi badir yan dubu guda uku ya ajiye gaban Alhaji Musa yana cewa
"A matsayina na waliyyin Ibrahim Khalil ina nema masa auran yarku Aisha wannan kudi Dubu Dari biyu kudin gaisuwar Iyayene dana na gani ina so, se wannan dubu dari kuma Sadaki ce kamar yanda waliyyinta Alhaji Muhammad ya yanka mana"
"Amma Alhaji mun rigada munyi magana da kai cewar mu a qa'idar gidan mu bama karban wani dukiyar aure Sadaki ne kawai kuma mun yanka muku" Alhaji Muhammad ya katse Baba Abu se Baba Imrana yayi saurin cewa

"Mun sani Alhaji amma muna neman alfarma tunda mun kawo ayi haquri a karba, Ya fa zaku bamu ina ganin ko Duk abinda muka mallaka muka kawo be kai mu biyaku karamcin da kukayi mana ba".

Bayan Alhaji Muhammad ya karbi kudin ne Alhaji Musa ya sakeyin gyaran murya yace
"Ba karambani ba duba da yanayin tazara dake tsakanin garuruwanmu da rashin tsaro da ake fama dashi ga kuma damar da tazo a kan gaba yasa nake tunanin tunda har mun samu daidaito kuma yarjejeniyar aure ta qullu a tsakani, me ze hana mu taqaita komai domin mu hutashshe ku dawainiya da sake dawowa harma da yin gayyar mutane zuwa daurin aure. Yanzu da yardar Allah idan an idar da Sallar Isha'i da akwai auren yar dan uwanmu da za'a maida a nan masallacin, ina ganin idan har babu damuwa daga gurinku dan mu a shirye muke in kun Amince a hada gaba daya ina nufin a daura auran ita Aisha da Ibrahim kaga mun sallameku Yarinya ta zama taku se ku koma can Kano ku yi shirinku duk sanda kuka so ku dauki Amaryarku a hannun Hauwa, muma daga nan sabga ta mata idan an tashi tariya suje suga mazauninta shi kenan ba se munyi rakiyar Kura ba kunzo kun koma ku sake dawowa sannan muma mu biku, zamu baku guri ku tattauna a tsakaninku yanda kukayi se muji".

Shiru sukayi ganin waliyyan Humairan na shirin miqewa Alhaji Garba ya numfasa yace
"Idan akayi hakan Alhaji zamu fi kowa murna to sedai wani hanzari ba gudu ba, bamu san shirin ma'aurin ba ina nufin ta bangaren gurin zaman ita yarinyar da sauran abubuwan buqata bamu da tabbacin ya tanade su amma hakan baze zama wata damuwa ba da yardar Allah, Abubakar seka kirashi ka sanar dashi halin da ake ciki Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi" gaba daya suka Amsa da Amin.
"Ai maganar muhallima nasan wannan ba matsala bace Lefe kuwa ya gama danma sunce kar azo dashi ne kaga babu wani abu da yayi masa saura inaga se zuwan Amarya kawai" Baba Abu ya fada cikin raha kafin ya shiga kira wayar Khalil sau biyu be dauka ba, jin fara kiran Sallah yasa suka fita. Masallacin ya cika danqam ciki da waje ba kamar yanda sukayi sallar Magriba ba Baba Abu ya kalli Angon da za'a maidawa aure da zugar abokansa ya cewa Baba Imrana
"Kaga shirin Allah, qila da munzo dashi yayi mana taurin kai shiyasa can qafarsa ta riqe muka zo babu shi, Allah ya sanya Alkhairi yasa mutuwa zata raba.

Bayan an daura auren suka niyyatu wucewa Hotel inda zasu kwana amma iyayen Humairan suka hanasu dan tuni an tanadar musu makwanci Abincin da basu ci bama can aka kai musu, duk wani abu da zasu buqata an tanada bayan sun dan sake taba hira suka barsu saboda su huta se a sannan Baba Abu ya kira Hajiya ya shaida mata, kasa magana tayi seda ya sake cewa
"Hajiya ko bakya Ji nane" kafin ta aje numfashi saboda kaduwar da tayi da zancen daurin auran tace
"Ina jinka Abubakar labarin ne yazo mun a bazata har na rasa abinda zance akai"
"Me kuwa zakice muma duk haka abinya shammace mu kuma su da zasu bamu suka yanke haka kinga babu damar muce Aa se ya zama kamar ba dagaske muke neman ba fatanmu dai Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi kawai amma yanzu kuyi shiru da maganar karta fasu a Dangi tukunna har se mun dawo"
"Toh ubangiji yasa hakan ya zama Alkhairi Allah ya basu zaman lafiya kuma yasa matarsa ce har gidan Aljanna" Hajiya ta fada daga nan sukayi sallama.

Gaba daya rasa ta inda zata fara tunani ma tayi, an daura auran Khalil daga zuwa tambaya ta ina zasu fara fitar da wannan Labari har ya isa kunnen Matarsa a wane matsayi zata karbi abun?
Jalilah ta kwalawa kira dan tanada buqatar wanda zasu shawarta tunda wuri, seda ta sauke tagumin data rafka saboda Jimami Umaimah kawai take tunowa a duk cikin al'amarin dalilin daya hanata yin murna da daurin auran gaba daya kenan. Bude baki tayi da kyar ta gayawa Jalilan yanda sukayi da Baba Abu, sak tayi da farko kamar bata gane abinda Hajiyar take fada ba kafin ta saki Kabbara ta waiwaya gabas ta tsugunna tareda kai goshinta qasa tayi Sujudushshukur seta miqe tana kallon Hajiyar bakinta kamar ze tsage tace
"Kin gani ko Hajiya Allah kadai yasan sirrin daya boye cikin wannan auran Allah yasa silar fitar Khalil daga qangin rayuwar da yake ciki kenan" seta juya da sauri ta koma falo, a kan Khalil ta tsaya ta rangada masa guda tayi ta qarayi yanda kasan wadda ta kawo Amarya.

KHALIL
Kallon bakin Jalilah kawai yakeyi yana so ya tantance abinda take fada, wai shi Khalil take nufi an daura masa aure kowa? Maganar da sukayi da Mansur ta fado masa take ya hadasu da maganganun Jalilar lissafin ya bashi daidai da gaske kenan aurensa aka daura amma ya akayi hakan ta faru?
Wayarsa ce ta sake daukar qara ya daga ganin Baba Abu ne kafinma yayi magana yace masa
"Kai ina ka shige ina ta kiranka baka dauki waya ba ina fatan da kaji abinda ya faru ko? Toh daman kira nayi in ja kunnenka ko zaka fadawa matarka ka bari seda safe dan wlh babu ruwana ga Hajiya nan ka tambayeta sanda Nayiwa Zinatu Kishiya lokacin kana Ingila seda nayi sati daya a gidanku Hajiya ta bani Maboya kafin su Alhajin Gabas Allah yajiqan rai suka shiga suka sasantamu dan haka kabi a hankali"
Chapter 189 · 0% Book details