← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 267

Sashe 54

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa tayi ta bawa kowa ledarta suka karba suna godiya tace su jira tayiwa Khalil magana ta qarasa dakin yana zaune ya jingina da fuskar gado yana waya dan haka taja gefe ta tsaya tana harararsa, kashe wayar yayi ya kalleta ba tareda yayi magana ba tace
"Zasu tafi"
Wallet dinsa ya bude ya zaro dubu biyar ya miqa mata ta karba ta koma ta basu, seda ta raka su har qofar gida sukayi Sa'a Adaidaita ya sauke wata mata seda ta kalleta dakyau ta gane Rufaida maqociyarta ce da wata da take zaton qanwarta ce goye da baby tayi qiba tayi kyau su Habiba suka shiga ya wuce dasu ita kuma ta tsaya suna gaisawa.

"Ai baki da kirki dai Amarya" Rufaidan ta fada tana qarasowa qofar gidan Umaiman, ta saki murmushi tace
"Na yarda amma kiyi mun afuwa tunda kin dawo yanzu zan shigo ko yaushe in Allah ya yarda"

"Toh shikenan dukda dai ban dawo ba se jibi share share zamuyi yanzun" Rufaidan ta bata amsa daga haka sukayi sallama ta juya cikin gida.

Su Habiba sun rigada sun gyara mata gidan dan haka ta samu guri a palour ta zauna tana duba hannunta da yatsun suka tashi da alama dai se taje koda Chemist ne an duba dan har sannan tana jin zafi akan fatar ga kuma tashin da gurin yayi. Bude qofa Khalil yayi ya fito yana kallonta ta dauke kai, haushin sa takeji shi har yana da bakin tambayarta wata yar iska ma ko saboda kawai yaga tayi sanyi kwana biyu shine ze nemi ya taka ta to su zuba su gani.

Zama yayi a kujerar dake kallon wadda take kai yana kallonta yace
"Akan wane dalili zaki zagi Lubna kiyi mata gori kuma saboda ta rama ki rufeta da duka har kika ji mata ciwo"

"Kan babbar bala'i au abinda ta gaya masa kenan?" Umaimah ta ayyana a zuciyarta a fili kuwa gyara zama tayi irin na me shirin tarar duk abinda ze zo tace
"Saboda na isa shiyasa na daketa kuma ba Lubna ba ko uwar Lubna da ubanta ne suka zo cikin gidan nan suka gaya mun makamanciyar maganar data fada akanka tayi mun gadara sena ci ubansu ballantana ita qaramar Alhaki".
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 25

Kallonta kawai Khalil yakeyi ya kasa cewa komai saboda tsabar mamakin rashin mutunchi da tsaurin idonta dakyar ya iya bude baki yace mata
"Umaimah, uwa da uban Lubna kika zaga kin san matsayinsu a gurina?"

Zumbura baki tayi gaba tareda matsawa gefen kujerar da take kai ya zamana sun qara samun tazara a tsakaninsu kafin tace

"Oho nidan koma suwaye uban yarinya zanci idan ta sake shiga sabgata gara ma ka gaya mata wallahi"

"Lallai zaki iya zagin Hajiya koda yake ma kin zageta dan da ita da Kawu Najib da Anty Dubu abu daya ne a gurina, toh bari kiji kinyi na farko kinyi na qarshe duk ranar da da wasa kika sake kuskuren gayawa wani nawa maganar banza ma ballantana ta kai ga zagi se na baki mamaki Umaimah dan nasan darajar iyayena bakuma ayi macen da zata wulaqantasu ko ta zage a gabana ba" Khalil ya fada cikin matuqar bacin rai yana miqewa tsaye, dakinsa ya nufa se kuma ya fasa shiga ya juya da niyyar fita yana jin qunquninta tana cewa

"Oho dai kuma na daki banza, ai baka burgeni ba da baka rama mata dukan ko zagin ba"

"Ni nasan mutunchi da qimar iyaye bazan zagi naki ba, duka kuma kibi a sannu duk ranar da kika tiqeni zaki gane ba tsoronki nakeyi ba da ya saka nake raga miki" ya sake fada yana aika mata da wani irin kallo daya saka qirjinta bugawa.
Fita yayi saga gidan ya samu kan wani dakali daga can gefe ya zauna yayi shiru, shi kuma tasa qaddarar akan aure, wayar sa datayi qara ce ta katse masa tunani ya cirota daga Aljihunsa ya daga ganin Hajiya ce take kira.

Tiryan tiryan ta fada masa abinda su Habiba suka gaya mata ya faru a gidan,
"Ni daman nasan qarya takeyi Umaimah bazata aikata abinda tace tayi mata ba tareda dalili ba kuma ni tayi mun daidai data zaneta tunda bata da kunya idan ba haka ba taje har cikin gidan ta tace zata mata rashin kunya ai idan bata dubi darajar matarka ce ba ta dubi na tazarar shekarun da ta bata, Allah ya rufa asiri ka bawa Umaiman haquri dukda nima zan kirata" Hajiya ta fada se Khalil ya saki murmushin takaici a ransa yace
"Almura, duk mugun halin ta babu me yarda se wanda ya gani da idonsa" a fili kuwa yace

"Koma menene abinda Lubna tayi be kamata ace Umaimah ta daketa ba, me yasa bazata kirani ni ta gaya mun na dauki mataki ba kawai seta kama yarinya da duka" ya fada cikin bacin rai se Hajiya ta tare shi da cewa

"Akul Khalil karka kuskura ka zama cikin irin mazan da suke goyon bayan qannensu sama da matansu koda kuwa sune da gaskiya, yanda kake da damar hukunta na qasa da kai idan sunyi laifi haka matarka matsayin ku daya kaida ita a gurinsu kar kuma ka kuskura ka basu qofar da zasu rainata dan kai kanka bazaka ji dadi ba, saura kuma naji wani abu daban" daga haka ta kashe wayar tana jin haushin son kan da Khalil din yake neman nunawa, a zatonta da yaji kan labarin zece ze qarawa Lubnan wani dukan ne se taji akasin haka, maza dai Allah ya shirya su da son kai.

Khalil kuwa cikeda qarin takaici ya maida wayarsa Aljihu yanzu idanya gayawa Hajiya zagin da tayiwa yan uwanta cewa zatayi qarya ne saboda makauniyar soyayyar da takeyiwa Umaimah shidai yana fatan Allah karya kawo ranar da notin kan Umaimah ze goce a gaban Hajiya ko inda zata samu labari dan besanyanda zata kaya ba. A gurin yaci gaba da zama har aka kira sallar magriba kafin ya wuce masallacin cikin layin nasu yayi sallah, har ya zauna dan baya son kowama gidan ta qara bata masa rai se kuma ya tuna da ya taho da wani aiki da zeyi dan haka ya miqe ya tafi gidan.

Tana zaune tayi daidai akan daddumar da tayi sallah ga faranti a gabanta ta yankakken mangwaro da gani me qanqarane, kallo daya yayi mata bayan da yayi sallama ciki ciki ya dauke kai, ya ja mata kunne akan shan sanyi amma taqi ji, be kukata ba ya wuce cikin dakinsa ya kunna Laptop ganin chajinta yayi qasa ya saka shi neman chaja amma be ganta ba, daga cikin dakin ya kwalawa Umaimah kira, tana jinsa sarai amma tayi banza har seda ya gaji ya fita ya tsaya a qofar dakin yana kallonta, yasan taji shi sarai wulaqanci ne ya hanata amsawa amma bashi da lokacinta a yanzu.

A dake ya ce mata
"Ina kika saka mun Chager Laptop dina?"
Wani kallo ta watsa masa me kama da harara kafin ta tura baki gaba tace

"Ni ka bani ajiya ne ka duba a inda ka saba ajiyewa mana". Seda ya hadiye abinda ya tsaya masa a maqoshi kafin ya sake ce mata

"Idan tana gurin da nake ajiyewar ai da banzo na tambayeki ba, ki taso malama ki dakko mun ina da abunyi"
Yanda yayi maganar babu wasa ya sakata miqewa dole ta wuce shi tana qunquni, magana takeyi sarai kuma ya jita tace

"Haka kawai ayi mun laifi dan na dauki mataki kuma ya zama abin fushi toh ko kububuwa mutum ya zama ba abinda ya shafeni wallahi yarinya ta sake zuwa tayi mun hauka naci ubanta na kuma daketa na daki banza babu abinda za'a iya" ta shige ta dakko Chager data saka a cikin drawer sabanin saman drawer daya saba ajiyewa. Akan gado ta dora masa ta fice tana juya jiki Khalil ya bita da kallo ya saki murmushin zallar takaici kafin ya jona chager ya shiga aikin da zeyi

Qunquninta ne ya ringa dawo masa haka kawai yaji ransa yana qara baci wato babu abinda ya isa yayi mata koh wai wane irin raini Umaimah take dashi haka ace mace har mace amma babu ladabi harshenta babu linzami? Yaga alamar dauke kai da yakeyi yana kyaleta a maimakon tayi hankali iskancinnata qara gaba yakeyi, dole ya dauki mataki tunda shi ta rainashi ai akwai na gaba da ita da take shakka.
Chapter 54 · 0% Book details