← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 267

Sashe 127

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kan Dan gadonta da ya gani a gefen kijera ya kwantar da ita tareda pecking goshinta. Kai tsaye kan Dining din ya wuce ya kalli wasu Luxury warmer data zuzuzuba abincin a ciki su kadai kyan su ya isa ya saka ka cin abinda yake ciki ko bakayi niyya ba. Zama yayi ya bude babbar ciki, Tuwon shinkafa ne fari so a ciki, ya waiwaya ya kalli Umaimah data biyo bayansa kamar mara gaskiya, da yar mutunchi suke tashi zeyi ya dagata yayi juyi da ita dan kamar ta shiga zuciyarsa, abinda yake muradi kenan yaci har mafarki yake ya samu tuwo dan tunda ya tafi ko a ido be ganshi ba, zuwan da yayi kwanaki ma zaman hotel ya qare harya tafi be ci ba.

Qaramin murmushi ya sakar mata, Umaimah ta sauke ajiyar zuciya har yana ganin yanda maqogaronta yayi sama da qasa kafin ta taho kamar wahainiya ta shiga bude masa sauran warmers din. Miya kala biyu tayi masa, Miyar Egusi dataji duk wani kalar Wasali da ake sakawa miya ga hadaddiyar Kuka wadda tayi digiri a London tasha zabi da suka dagargaje saboda yanda ta bata lokaci ta dafu.
Dayan kwanon Jellop din shinkafa ce itama dai se wanda ya gani ga wani Musulmin peppe meat tsabar qyallin da yake kamar zaka ga fuskarka a jiki. Se casserole data zuba hadin potatoe Salad dayan kuma ganyan lattece yasha garnishing se wani bowl me kyau data zuba Samosa da spring roll ga kuma Jug din Coconut drink dana Zobo se Jarkokin ruwa me sanyi har diga yakeyi

Duk yanda yaso ya daure seda ya kama hannunta na dama ya sumbata, qarshen abincin sa kenan ta hada masa su, ga Tuwo ga shinkafa ga nama.ga kayan fulawa. Kadan ta zuba masa kowanne a plate yayi bismilla ya shiga ci yana kallon fuskarta data marairaice kamar marainiyar Mage, tuwo ya gutsira ya nufi bakinta dashi, Allah sarki yanda take abu se yaji kamar zata bashi tausayi amma ya kanne haka suka shiga cin abincin yana ci yana bata har suka gama ba tareda wani yace qala ba.

Ita ta kwashe kayan ta kai kitchen ta dawo ta goge gurin harda fesa freshner, a ransa yace
"Ikon Allah, su Umaimah course din tsafta aka yo kenan yana kallo ta ta shige daki babu dadewa ta fito ta zauna akan kujerar gefensa.
"Na same ku lafiya?" Ya fada yana chanza channel, da sauri ta amsa masa ya daga kai ya kalleta, yanda take muimui da baki alamar tana son yin magana se juya yatsunta take kamar me jin tsoron yayi bala'in sake kunna shi.

"Kaak...kayi haquri dan Allah" ta fada dakyar hawaye na kawowa idonta, banza ya mata yaci gaba da chanza channel din da yakeyi
"Dan Allah Khalil ka yafe mun, wallahi sharrin shaidan ne bazan sake ba" ta sake fada cikin muryar kuka"
juyowa yayi ya kalleta, a cikin idonta ya karanci laushin da tayi na gaske ne ya kuma tabbatar da wannan ladabin bana qarya bane da gaske takeyi amma dukda haka baze saki da sauri ba, haka nan baze fasa qudurinsa akanta ba.

Hannu ya miqa mata fuskarsa dauke da wani murmushi da kai tsaye bazata iya fassara ma'anarsa ba yace mata
"Zo nan, haka ake bawa Miji haquri a garinku" ya qarasa yana dorata a cinyarsa ya zura kansa cikin wuyanta yana shaqar qamshin turarenta da tun gamuwarsu ta dazu ya hautsina masa kwakwalwa. Baki ta buse da niyyar sake magana yayi saurin rufe mata da nashi, daga nan labari ya canza, da farko cikin nutsuwa da soyayya ya ringa tafiyar da ita, seda tafiya tayi nisa ya birkice mata. Cikin wani irin fushi da sauri yake saraffata, tayi kuka tayi magiya Bibi kanta dake bacci seda ta farka ta shiga taya Mamanta kukan neman ceto amma be saurare su ba, seda dan kanshi yaji ya samu nutsuwar da yake da buqata kafin ta qyaleta, be ko bi takanta ba ya tsallake ta ya shiga dakinsa ya yiwo wanka ya dawo ya dauki yarinyar dake faman tsala kuka.

Ki tashi kiyi wanka ki karbeta" ya fada yana kallonta cikin sigar bada Umarni dole ta tattara jikinta da take ji kamar Buldozer tabi ta kanta, dakyar take iya daga qafarta ta kuma tabbatar da yaji mata ciwo ba kadan ba. Haka ta ringa gas jikinta tana kuka taredajera masa Allah ya isa a zuciya. Da tasan muguntar daya shirya mata kenan da bata shige masa ba. Ta gaya masa da wannan salon muguntar tasa gara ya saka bulala ya zane ta idan tayi masa laifi amma Allah yana kallo kuma seya saka mata.

Tsawar daya bugo mata akan tayi sauri ta fito ta karbeta ce ta sakata qarasa wankanba shiri ta fito, an kira sallar La'asar dan haka tana karbarta ya fice daga gidan yana sakin wani mugun murmushi na jin dadi, riba biyu, ya kwashi dadin da yaji kamar ze manta sannan ya horata yanda zataji a jikinta, Allah ya kaimu dare zata sake gane kurenta, tunda ita bata ji ta haka ze ladabtar da ita har se kunnenta ya ringa jin abinda yake gaya mata.

Da daddare daya kirata dakinsa kuka kawai ta saka masa dan ta tabbata ranta kuma yake nema, tun dazu da yammar zazzabi ya saukar mata, wani irin azaba takeji a qasanta dukda yanda ta shiga ruwan zafi ta gasa kanta dakyau amma kamar batayi ba ta tabbata hakan nada alaqa da uban maganin matsin da tayi amfani dashi bayan dinki da akayi mata na haihuwa. Daman seda Nuratu taja mata kunne sanda tace ta bata dan ita Allah ya taimake ta duk haihuwar da tayi bata samu qari ba shiyasa take yan gyare gyarenta amma Umaimah ga dinki ciki da waje ta nace seta bata,
"Jiki magayi" abinda ta fada kenan gashi kuwa tana gani. A daren nan haka Khalil ya sake moreta seda yayi bidirinsa tsaf ya gama kafin kuma ya fara jin tausayinta, haqoranta har haduwa suke saboda zafin zazzabi ya taimaka mata ya gasata sosai kukan ma ta denayi se ajiyar zuciya kafin ya hada mata tea me kauri tasha da maganin rage zugi daya siyo bayan daya fita sallar Magriba dan yasan zata buqace shi dole sannanta samu bacci ya dauke ta.

Da safe seda ya tsokaneta tana kwance yazo kamar ze shiga jikinta yanda ta zabura idonta ya fito seda ta bashi tausayi da dariya. Yanayin zafin jikin dayaqi sauka yasa dole sukaje Asibiti, dinki dai ya farke tas oho shi bema ji ba haka aka saka Umaimah a Theatre aka sake sabon dinki, bala'i dai ta ganshi muraran dan suna hanyar dawowa daga Asibitin kuka ta ringayi tana roqonsa ya maida ita gidansu. Da wannan Azabar data sha daga jiya zuwa yau ai gara zaman Cell din da tayi Aradun Allah shidai Khalil dariya kawai yakeyi a zuciyarsa dan ba wai iya hukuncinta kenan ba, ta gama wannan jinyar yana nan ze jijjigo mata gagarumar jinya ta gaske.

Seda Umaimah ta kwashe kusan sati hudu tana jinyar jikinta, Ummu-Salma ce ta dawo gidan tana taya ta da ayyuka saboda suna hutu sannan, a bangaren Khalil kuwa wani mugun tsoronsa ne ya darsu a ranta, duk abinda takeyi idan taji muryarsa se gabanta ya fadi ta fara tsuma musamman da ya samu sarar daure mata fuska a yanzu tun bayan daya gama dagargazarta ya dinke fuskarsa tsaf baya mata dariya, idan kaji muryarsa yana wasa to da Salma yake magana ko kuma ya dauki Bibi yana mata wasa ita kuwa tsakaninta dashi gaisuwa ce daman itama bata so din wata doguwar magana ta hadasu ballantana har a sake maimaita abinda ya faru.

Se a yanzu tayi nadama ta gaske ta kuma tsinewa shegiyar Khausar data ja mata, da bata shigo rayuwarta na da duk wadannan abubuwan basu faru ba. A haka aka ci gaba da gungura rayuwa, Umaimah ta canza lokaci daya tayi wani irin sanyi qalau. Gidansu me cike da soyayya da kwanciyar hankali ya dawo kamar wani gidan Makoko, babu wani karsashi a cikinsa idan kaji magana me qarfi Tv aka kunna ko Bibi ce take rigimarta, a bangaren Khalil kuwa be ma cika zaman gidan ba yanzu se dare. Daga office idan ya tashi ze wuce sabgoginsa dan yanzu Yana taba abubuaa da yawa ga kuma sabgar ginin gidansa da bayan dawowarsa seda yasa aka canza abubuwa da yawa saboda ba'ayi su yanda ya tsara ba, idanya koma gidan ma tsakanin su gaisuwa ce idan tayi abinci in yayi niyya yaci idanbega dama ba ya ciyo a gidan Hajiya haka suka kwashi kusan wata biyu a wannan yanayi.

Babu inda take zuwa gashi maqotan da suke gaisawar ma gaba daya Rufaida ta rabata dasu yanzu babu me shigowa gidanta se Kishiyar Maman Hauwa da ita kadai suka ci gaba da zumunchi se wata Amarya da aka kawo ita kuma ba mazauna bane Mijin a kudu yake aiki kuma tare suke tafiya haka zata wuni a gida sedai tayi ayyukanta dan yanzu tsafta kam babu kama qafar yaro, Khalil har gulmarta yake a zuciya daman ita tun Asali idan suna fada ko suka samu sabani tafi nutsuwa ta ringa abinda ya kamata yanzun ma haka ta kasance gidan nan ko yaushe qal ta saka turare wannan karon jego take na masu hankali daga ita har Bibi bazaka gansu da qazanta ba musamman da tayi sa'a yarinyar bata da rigima sam idanta qoshi zatayi wasanta daga nan tayi bacci gashi har sannan ba'a dawo da Mu'ayyad ba, tsabar tunani da zaman Kadaici ya saka depression ya nemi kamata.

Wani mugun ciwon kai tayi ranar Allah ya saka yana gida Weekend ne, tana cikin daki daman tun dare take fama da ciwon kan zuwa safiya ko motsin kirki bata iyayi saboda yanda takeji tamkar ana kwada mata guduma idan akan.
Chapter 127 · 0% Book details