← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 219 OF 267

Sashe 219

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amin Mama babu komai in sha Allahu Da ai na kowa ne in sha Allah zanyi iyakar iya wata kuma ina fatan idan da rabon daidaito Allah ya shiga tsakani Mamansu ta dawo muci gaba da zaman mu" Humairan ta fada se Maman ta kasa amsa mata haka ta rakota har inda Khalil din yake jiranta da sauran yaran.
50k ya bawa Mama da Antyn yabi sauran yaran gida da 2k kowanne suka ringa saka masa Albarka suna tsaye tsakar gidan Anty na sake jaddadamasa zancen kawo yaran har ya hada kan iyalansa suka fice sauran yaran suka rakasu. A baya Mu'ayyad da Bibi suka zauna kafin ya zaunar da Iman itama dan se hanqoron shiga takeyi ganin su a ciki kamar ta sansu, da kansa ya budewa Humaira qofar gaba ta shiga ta zauna sannan ya karbi Aryaan daga hannun Salman suka sakeyin Musabaha ya miqa mata shi sannan ya sunkuya yana gyara mata mayafinta daya fito waje yana tsokanarta da cewa
"Qannenki sun qara yawa daga hudu kun zama ku biyar" ita kuma ta mayar masa da cewa
"Eh naji dai qannen nawa ne kai kuma Babanmu" ya saki murmushi saboda yanda tayi maganar, seda ya kulle mata qofar kafin ya juya zuwa bangarensa kamar ance ya kalli gefe karaf idonsa suka shiga cikin na Umaimah data qame a bakin qofar wani gida tana zare ido kamar wadda ta taka jelar Maciji.

Kallonta yayi na second biyu kafin ya dauke idonsa ya shiga motar zuciyarsa na bugawa, Tabbas So ba qarya ba, seda ya kwashi minti biyu yana qoqarin daidaita nutsuwarsa kafin ya iya kunna motar shima dalilin tambayarsa da Humaira takeyi lafiya taga yanayinsa ya canza lokaci daya seya dafa kansa ya kalleta yana yamutsa fuska yace
"Kaina ne ya sara"
"Sannu kona karbi Driving din?" Ta fada cikin nuna damuwa seya taka motar yana cewa
"Dadai ni dake ne kadai amma yanzu na debo gaba dayan Ahalina kice zaki jamu a Babban Titi Nooo" yayi maganar cikin zolaya seta zumburi baki tana cewa
"Allah yasa wata rana ka sake cewa ka gaji bazan kuma tuqaka ba" shidai yaci gaba da tuqinsa amma hoton ganin da yayiwa Umaimah ya gaza barin kwakwalwarsa.

Kenan bata damu da rabuwarsu ba dan babu alamar hakan a tattare da ita gani yayi ta qara kyau tayi qiba dukda Hijabi ne a jikinta ya tantance hakan koda yake me yasa zeyi tunanin zata damu dan ta rabu dashi ita da taso ta rabashi da duniyar ma gaba daya? Haka suka qarasa gida yayi qoqarin ganin ya kawar da komai daga ransa gudun kar wani ya zargi wani Abu, Humaira kuwa kallonsa kawai takeyi dan taga fitowar Umaiman kuma taga sanda Khalil din ya tsaya yana kallonta dan haka tasan damuwar daya shiga nada nasaba da ganin ta da yayi kuma bata ga laifinsa ha Matarsa ce da suka rayu tsahon shekara bakwai kuma yana sonta Qaddara ta rabasu dole zeji wani abu idan ya sake ganinta.
Da suka isa gida ma ganin yana buqatar fili yasa ta barshi ta shiga hidimar yaranta a Daren ta ware kayan Iman din tsaf ta shirya mata su a dakinsu na nan bangaren ta ware wasu ta kaiwa Hajiya aka saka mata a dakinsu na can tunda suma sauran haka kayansu suke, Ruqayya ta dawo dan haka bata samu wani qalubale ba ita take taimaka mata da hidimar Iman din ta bata abinci tayi mata wanka da shirin bacci ta goyata babu bata lokaci kuwa tayi bacci abinta daman Anty ta gaya mata bata farkawar dare indai taci ta qoshi haka kuwa sukayi baccinsu lafiya lau dan a dakinta ta kwana da ita da Aryaan ganin Khalil ya dage akan kan sa na ciwo yasa ta tafi dakinsa ta barshi yayi jinyar famin ciwon da ganin Umaimah yayi masa, washe gari kuwa da kansa ya bita ya lallabata bata ja magana ba dan daman ba fushi tayi ba suka ci gaba da rayuwarsu, Duk yanda ta tsara zata kula da yaran data haifa a cikinta haka take tafiyar da yaran a kullum kuma tana addu'ar ubangiji ya taya mata ya bata ikon kulawa dasu tsakani da Allah ba tareda ta cutar dasu cikin sani ko akasin haka ba.

UMAIMAH

Seda motar Khalil ta qurewa ganinta kafin ta farka daga suman tsayen da tayi, dakyar take jan numfashi saboda yanda zuciyarta tayi mata nauyi a hankali ta ringa tafiya tana dafa bango gudun karta fadi dan bata gani da kyau harta shiga gida, Mama da Anty na zaune tsakar gidan suna bude ledojin tsarabar da Khalil ya kai musu ta shigo Anty ta miqe ganin tana shirin fadowa kansu ta tareta tana tambayar lafiya? Cikin muryarta data shaqe saboda abinda take ji tace mata
"Khalil na gani shida wata mata ya bude mata mota har ya sun kunya yana mata dariya"
"Eh Matarsa ce daga nan suka fita ai yazo ya dauki yarsa" Mama ta fada cikin yanayin ko a jikinta se Umaimah ta bita da kallo kamar bata gane meta fada ba aranta tana maimaita kalmar Mataraa data fada, kenan tana Nufin Humaira ce wannan data gansu tare? Kuma ai itace ta gani da Anty se yanzu ta fahimci kallon sanin da tayi mata ashe ita ce.

Wasu hawaye masu tsananin zafi suka shiga tsere a fuskarta se kawai ta juya ta shige daki Anty ta saki baki ta bita da kallo tana cewa
"Toh kukan me takeyi kuma?"
"Na jin dadi mana" Mama ta bata amsa tana miqewa ta shige dakinta.

Umaimah kuwa zama tayi kan Gadon dakin tana hawayen da bata san dalilin yinsu ba. Wani radadi zuciyarta take mata kamar ana gasata idonta ya kasa dena ganin Khalil yanayiwa Humaira tsadadden murmushin da ita kadai take samunsa yanda yake kallonta kadai ya isa ya tabbatar maka da cewar soyayyarta ta huda Qashi da tsokarsa babu wata alama a tattare dashi da take nuna damuwa ko wani abu kenan ya manta da ita sannan yana nufin yayanta ma ya rabata dasu kenan duka ya mallakawa Matarsa ya dena sonta ya haqura da ita zeci gaba da rayuwa batareda ba? Tambayoyi ta jefawa kanta da bata da amsarsu haka bata da me bata amsar a kusa da ita

A sannu a hankali kwakwalwarta ta fara yarda da tabbacin cewar Khalil yana raye tareda wata Mace bayan ita ta kuma gasgata cewar a yanzun babu igiyar aure a tsakaninsu mafi munin abun ta haihu iddarta ta kammala tuntuni koda ace zasu sake komawa qarqashin inuwar aure dashi se bayan an sake daura musu aure wanda bata zaton iyayenta da a yanzu basu da abinda suka tsana sama da ita zasu yarda da hakan balle aje ga nasa yan uwan da bata matsayinta a gurinsu ba. Dagaske ta rasa Khalil ya zama mallakin wata daban ba ita ba. Zamewa tayi ta kwanta akan Gadon saboda ji da tayi dakin yana juya mata gaba daya a maimakon ta nemi taimakon Allah ya sauqaqa mata abinda take ji a ruhi da gangar jikinta se kawai ta bude baki ta ringa zunduma ihu tamkar ba diyar musulmi ba babu kiran Allah se maimaita Kalmar ta shiga uku ta lalace takeyi.

Anty dake tsakar gida tana cigada ayyukanta dan ita ce da girki tana shirin dora abincin dare ta zabura tayi dakin dan ganin abinda ya saka Umaiman irin wannan ihun. Abba ya shigo gidan da Sallama dawowarsa kenan daga Kasuwa yaci burki a bakin qofa yana jiyo ihun Umaiman da muryar Anty dake qoqarin kwantar mata da hankali da nuna mata cewar Addu'a ya kamata ta ringayi ba iface iface ba.

Zuciyarsa tayi baqi ta kawo masa wuya, tun bayan Dawowarta gida be yarda sun hadu ido da ido ba saboda gujewa baqin cikin da yake tsintar kansa a ciki duk sanda ya tunata balle ace ya ganta a cikin gidansa. Tun sanda ya fahimci Anty da Maman ne suke hidimar Malika ransa ya qara baci wato Umaimah bataji maganarsa ba amma ya qyaleta kawai domin lokaci yake jira da duniya da kanta zatayi mata karatun da tilas ta fahimceshi yayi niyyar ya zuba mata ido ne yaga iyakar Hankalinta amma Ihun da take masa yanzu a cikin gida ya bata masa rai matuqa ya tunzura zuciyarsa, kasa dauke kai yayi dole ya koma waje, wani saurayi dan maqotansu ya kira yasa ya tsinko masa Bishiyar Dogon Yaro dake qofar gidan ya zuge masa guda uku Saurayin yanata mamakin abinda Abban zeyi dasu ya diba ya koma cikin gidan har sannan Umaimah bata bar ihun da takeyi ba abin baqin ciki daya shiga dakin a qasa ya tarar da ita tana birgima da ihu kamar wadda ta gamu da ciwon hauka, ba tareda bata lokaci ba ya shiga dukanta tamkar an aikoshi Anty batayi gigin shiga tsakani ba tayi gefe da sauri gudun kar ya hada da ita dan irin bacin ran data gani a idonsa tasan ya kai maqura yau kam. Jikinta ya dauki rawa saboda ganin irin dukan da yakeyiwa Umaiman da gushewar tunanin dan lokaci ta sameta saboda yanda dukan ya zo mata a bazata ta dena birgimar ta tsaya kawai kwakwalwarta na qoqarin gane abinda yake faruwa.

Wani gigitaccen ihu na gaske ta fasa sanda zafin dukan ya ratsa kwakwalwarta ta shiga neman ceto Abban kuwa be bata dama ba, a kwana ya sakata ya ringayi dukanta iya qarfinsa tamkar ya samu Jaka, tun tana ihu da guje gujen neman taimako harta haqura ta zauna guri daya ya ringa lafta mata bulalu seda duka ukun suka karye a jikinta kafin ya jefar da sauran yana haki ya kalli Anty da ta gama tsurewa a gefe ta gagara ko motsawa agurin da take saboda firgici yace
"Ki kawo mun ruwan zafi" ya fice fuu har yana shirin hardewa da babbar rigarsa.
Chapter 219 · 0% Book details