← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 267

Sashe 147

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umaimah hankalinta idan yayi cikin tirela ya tashi da jin wai zatabi Baba Badaru, ita kuwa wane tsautsayi nr ze ritsa da ita haka? Ai wallahi gara ta koma Khalil idan gunduwa gunduwa zeyi da ita yafi mata sauqi. Tun suna yara bata taba sha'awar ko zuwa hutu gidansa ba duk kuwa yanda su Nuratu ke doki da rizgillin son zuwq Abuja sedai su dawo suyi ta bata labari amma koda wasa bata taba zuwa ba. Bata jin magana Baba Badaru kuma baya daukar nonsense dan ko gidansu yazo daga gaisuwa gudu takeyi karma ta tsaya tayi shirme a gabansa yaci ubanta shiyasa ko yaransa babu wata shaquwa tsakaninta dasu bama zata iya cewa ga Adadinsu ba dan ba shiga abinda ya shafesu take ba tana gudun masifar Babansu shine yanzu zece ta bishi salon ya kasheta acan sedai ya aikowa yan uwanta jana'iza tab.

"Yanzu dai ayi haquri gaba daya dan laifi Umaimah bata kyauta ba amma shima Khalil yayi laifi. Me yasa ze saka yaidara a cikin lamarin ai ba ga Umaimah ba ko a gurin ubangiji beyi daidai ba hakan ma da yayi yasa Allan ya nuna masa wayonsa baze bashi kwangilar ba sannan dan ta zama sila hakan bashi ze bashi damar ya taba lafiyarta ba, ko dan gaba karka sake, idan tayi maka abu da bazaka iya jurewa ba ka kawota gaban magabatanta su tsawatar mata amma koda wasa karka sake cewa zaka taba lafiyar jikinta" Alhaji Abubakar kawun Khalil ya fada kafin ya dora da cewa
"Yanzu dai magana ta wuce Alhaji muna sakw baku haquri komai ya wuce ke ki bawa mijinki haquri sannan ki shiga ki hado kayanki mu tafi dare yanayi"

"Ai Yaya Badaru ya gama magana Alhaji, kuyi haquri kuje kawai, idan aka kwana biyu zuciyoyi suka qarayin sanyi seta dawo amma yanzu idan akayi haka tamkar an shiga haqqin yaron ne, kowa yasan abinda akayi masa babu dadi kuma yana da buqatar a bashi lokaci ya samu nutsuwa" Baba Liman ya fada nan su Alhaji Garban suka dage akan lallai fa se an basu bikon Umaimah sun tafi da ita.

"Kayi haquri Khalil dan girman Allah wallahi sharrin zuciya ne amma nayi alqawari bazan sake ba" Umaimah dataga Lamari yana qara rikicewa ta fada cikin matsanancin kuka, fata take yace ya yarda ta bisun dan abinda Baba Liman ya fada kenan se anji ta bakinsa amma yayi mirsisi ya zubawa qasa ido yaqi ce musu komai,

"Babu shakka, Khalil ma kike kiransa kai tsaye saboda kin rainashi ko" Baba Munzali ya katseta se tayi saurin cewa
"Abban Mu'ayyad na tuba bazan sake ba, na yarda daga yanzu in na kuma duk hukuncin daka ga dama ka yanke akaina amma yanzu ka yafe mun dan Allah". Cikin tashin hankali take dan idan yace baze tafi da ita ba bata san inda zata tsoma ranta ba. Zancen tabi Baba Badaru ma baze yuwu ba dan ko duniya zata taru bazata gidansa ba wallahi kuma idan ta zauna a cikin gidan nasu ma tamkar ta fito daga rana ne ta fada wuta dan Shirun da Abba yayi yana kallonta kawia ta tabbata idan be hada mata jikinta da duka ba to qila wuqa ze saka ya yankata balle labari ya isa kunnen Mama kai ita bata shirya fuk wani tashin hankali ba gara ta bishi suje can zata jure duk abinda zeyi mata har ya haqura ya sakko daga fushin.

"Ya isa haka, ina ganin magana tana hannun Khalil yanzu, idan ya yarda ya dauketa su tafi idam kuwa ba haka ba babu me tilasta masa akan ta koma. Zata cigaba da zama anan har zuwa sanda shi dakansa ya gamsu ya nemi ta koma din" Abbada tunda aka zauna bece komai ba yayi maganar ganin takaddamar taqi qarewa. Khalil ya daga kansa ya kalli Abban wanda shima shidin yake kallo. Iyayen Umaimah na daga abinda yasa yake daga mata qafa a lokuta da yawa dan mutanen kirki ne, a yanzun ma ta sake cin darajarsa dukda hakan ba yana nufin ya yafe mata bane Aa ze haqura ta koma ne saboda ya ragewa Abban radadin da abinda take aikatawar yake haifar masa wanda kwayar idonsa take gaza boyewa. Ya tabbatar idan aka auna jininsa a yanzu ya hau.

Rintse idonsa yayi cikin wata murya yace
"Na yarda ta koma amma..."
"Karma ka bata bakinka Yi shiru Halilu kaidai Allah yayi maka albarka ya qara maka hasken zuciyar musulunci, yanda ka iya shanye wannan baqin ciki Allah ya saka maka a mizani dan abinda kadai zan iya cewa kenan, Amma Alhaji sefa kunyi haquri dan ba zata biku yanzu ba saboda dole zamu sake yi mata fada a matsayin mu na iyayenta, idan Allah ya kaimu gobe da kaina zan rakota har gidan mun gode Allah qara Arziqi, ke tashi muje" Baba Abdullah daya miqe yana nade babbar riga ya fada.

Umaimah tayi wuri wuri da ido take murna ta koma mata ciki, jin Khalil ya yarda ta koma ga kuma wani sabon zance a gun baba Audun seta bare baki zata kuma rusa wani kukan ya daka mata tsawa yana cewa
"Na rantse da Allah ko ki tashi ko yanzu nayi ball dake a gurin nan, qarqari akai mi gidan yari na shekara na fito dan ba dauruwa zanyi ba" yanda yayi maganar kuma taga a gun babu wanda ya ce komai ya saka ta miqe jiki na rawa tana waiwayen Khalil da taqi kallon sashin da take.

Gabaya tasata, tun daga qofar falon yake antaya mata maruka a fuska da qeya har suka isa falon Mama, Mama da Anty na zaune kowa ta rafka tagumi dan Umaiman ta fado tana ihu.

Cikin rashin Jin dadi kawunan Khalil sukayi sallama da kowa suka tafi, Alhaji Abubakar ya ringa sababi wai ya wulaqanta su ya nuna basu isa ba, sun bashi umarni yaqiyi shidai Khalil ransa fes ya biya ya sauke kowanne a gidansa kafinya wuce gida yana zuwa ya tarar da Hajiya na jiransa, a taqaice yace mata kawai gobe Umaiman zata dawo, taja doguwar Hamdala ya tsaya yana kallonta kawai kafinya girgiza kai ya yi mata seda safe ya fita. Kwana yayi yana ayyana ta yanda ze iya manta abinda ya faru yaci gabada rayuwa da Umaiman.

Har ga Allah ba rasa kwangilarda yayi ne yafi damunsa ba, tunanin irin rainin da Umaiman tayi masa da harbata shayin tayi masa duk abinda taga dama. Idan har zata iya aikata haka bayan tasan cewa ze taba rayuwarsa ya taba aikinsa gababe san me zatayiba, dole ya dauki mataki kafin ranar nadama mara amfanita riskeshi. Tunanin hukuncin da zeyi mata ya huce kawai yakeyi amma har bacci ya kwashe shi be samu ba.

UMAIMAH
Seda Baba Abdullahi ya kumbura mata fuska da marukan daya ringa zabga mata tamkar Allah ya aiko shi kafin ya kalli su Mama da sukayi cirko cirko suna kallonsu aka rasa wadda zata kai mata taimako yace
"Ki gayawa wannan mahaukaciyar yar taki ta yanda kika hadu da ubanta".

Kallon rashin fahimta Mama tabi shi dashi, Baba Abdullahi da seka rantse shine ma Khalil din saboda yanda ya ara ya yafa a masifance yace
"Eh Malika, ki sanar mata da yanda akai kika auri Ubanta, koda yake bazata fahimta ba idan ke kika gaya mata, bari ni nayi mata gwari gwari ta yanda zefi shiga kwakwalwarta" ya juya kan Umaimah data dafe kunnuwanta da takeji kamar sun toshe yace

"To bari kiji, Hajiya Lawisa ta qaraye ai kinsanta Uwar Mijin Naziyya yayan maza muke da ita kuma itace Asali wadda suke soyayya da ubanki Sabo, sanda ya baro qaraye ya shigo birni Alhaji Madaki Mahaifin Malika gatanan data haifeki shine ya zamar masa ubangida, ya koya masa neman kudi har ya dorashi akan harkokin dukiyarsa da sharadin ze auri yarsa, bazawara ce ma a sannan baya sonta amma ya yarda kuma haka akayin ya koma gida ya fadawa iyayenmu ya fasa auran Lawisa duk da dadewar da sukayi suna soyayya haka kowa ya dauki qaddara aka barshi ya auri yar ubangidan nasa itama Lawisan kuma a cikin Abokanansa da sukaje daurin aure daga Birni Allah ya fitar mata da Miji tayi auran.

Sanadin auran uwarki duk muka baro qauye muka dawo nan masu boko suka kama masu kasuwanci suka kama da ba'a aure dan wata biyan buqata da yanzu ba a haifeki ba shegiya me kalar ibilisai kinzo kin gallabi kowa se kece zaki hana saboda baqin ciki da kyashi ya cika miki zuciya to ai kin kyauta, kuma yanda kika rusa kwangilar nan kikayi masa baqin cikin samun wasu a gaba in sha Allahu seya janye miki tallafi" Baba Abdullahi ya fada yana kai mata wani marin ta goce kafin ya gallawa Anty da Mama da suka zama hoto harara yaja tsaki ya fice daga gidan.

Muryoyin ragowar sukaji da suka fito suna musanyar sallama, suna tsaye kamar mutum mutumi Abba daya raka yan uwansa ya dawo jiki a sabule ya leqa falon Maman.
"Ki sameni a daki ina son magana dake" ya fada mata kafin ya juya Anty taja numfashi ta fesar kafin tace
"Bari naje na kwanta Allah ya tashe mu lafiya" ta fice daga dakin tana tariyo maganganun Baba Abdullahi da bata tabajinsu ba. Iya saninta Abban ya sanar mata da auran soyaya sukayi da Malika daman dai tasan yar ubangidansa yanzu kuma taji wata cakwakiya ashe shine dalilin da ya saka Sam Hajiya Lawisan basa wani shiri da Mama dukda bata nunawa Naziyya komai amma fa idan suka hadu ko a taro ne tafi yi da Anty akan Maman da suke matsayin surukai.

Mama ko tamkar wadda aka watsawa ruwan sanyi haka taja qafafunta da sukayi sanyi tabi Abban ba tareda ta bi takan Umaimah dake nan tsugunne tana kuka ba. Wannan cin mutunchi na Abdullahi har ina? A gaban kishiya yayi mata tijara, wai ma me Umaiman tayi daya juye kanta ake mata wannan tonon sililin?
Chapter 147 · 0% Book details