Sashe 44
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta voice din ta bata amsa tace
"Hakane amma ni gani nakeyi wannan abin ai ba se an koyawa mutum ba ko kuma se kaje ka kalli haram zaka koya saboda wannan kallon daidai yake da mutum ya aikata zina bayan zunubi ga illar da kallon tsiraici yakeyiwa ido gaskiya bazan iya zama a group din ba ni, iya ilimin da nake kwasa a group Malamina ya isheni kuma da qaramar wayewar tawa haka yake gigicewa idan na masa abu" ta qarasa tana murguda baki kamar tana gaban rufaidan dan gaba daya haushinta taji ya rufeta kuma ta farayi mata kallon yar iska dan ita ko irin sakin bakin nan da mata sukeyi idan ana hira raina mace takeyi ta kuma ringayi mata kallon yar iska, to idan ba dan iska ba waye ze ringa zancen batsa ko ya kunna a waya ya kalla?
"Allah ya baki haquri ni bada wani abu nake nufi ba" Rufaida ta fada saboda jin martanin Umaiman, se itama tace
"Nima ba wani abu nake nufi ba ai ra'ayina kawai na gaya miki iya wannan ma da nake ciki ya isheni, bari nayi sallah an kira" daga haka ta kashe Datar gaba daya ta tashi jin cikinta na qugi dan yanzu tana yawan jin yunwa qila nata kalar laulayin kenan dan dai har yau ita bata ji wani abu da ze saka ta yarda dagaske tana da ciki ba.
Waya ta kira ta fadi abinda za'a kawo mata kafin ta shiga bandaki, "uhm ko nawa ya kama dakin nan se Allah" ta fada tana qarewa bandakin kallo tayi fitsari ta dauro alwala daidai nan aka buga qofar dakin, seda ta zura dogon hijabi a jikinta kafin ta leqa ta yar hudar dake Jukin qofar taga ma'aikaciyar hotel dince da Tryn abinci dan sosai Khalil yaja mata kunne akan idan an buga ta fara duba waye kafib ta bude qofa, bude mata tayi ta shigo ta gaishe ta kafin ta ajiye abincin ta fita.
Seda ta qulle qofar da muqulli kafin ta tayar da sallah dan har biyu ta gota tana can tana surutu bayan ta idar ta dauko wayar data saka a chaji ta zauna tana cin abinci tana danne dannenta, data gama goge hannunta kawai tayi da tissue ta mayar da qafafunta kan dogowar kujerar da takr kwance ta miqe da kyau yanda zata ji dadin kwanciyar ta ci gaba da gashi.
Kiran Maman Asad ne ya katse mata fafatawar da sukeyi a wani group da Halima qawarta ta sakata ana zancen kishiya.
"Ke gani qofar gidanki muna ta bugu shiru halan baccin nan naki na asara kike yi" Maman Asad din ta fada bayan data amsa kiran, se Umaimah ta harari wayar kamar tana gabanta tace
"Toh ni bana nan ai da se ki kirani kafin kizo ko idan baccin ma nake sena tashi".
"Karki ga kinyi aure kice zaki mun rashin kunya ubanki zanci wallahi, zaki bude ne ko kuwa na kama gabana dan ina da gurin zuwa ni" Maman Asad din ta fada a hasale, se Umaimah ta kwashe da dariyar shaqiyanci tace
"Nifa dagaske bana nan muna Kaduna dazu da safe muka tafi"
"Yanzu zakuyi tafiya bazaki fadawa kowa ba ko dan abubuwan gyara a baki ki dan sabunta shine kika tafi ziqau dake ko bayan ko jiya ance a gida kika wuni? ai shikenan zanga randa zakiyi hankali kedai. Me kuka jeyi kuma wadanne irin kaya kika diba?" Cewar Maman Asad.
"Woh Yah Hajiyayye sarakan gyara yanzu tafiyar ma se anyi mata wani gyara gaba daya watana nawa a gidan mijin ma bare a faramun wani garanbawul? Kawa kuma yace karna dauki komai zamu siya a nan ni nigh gowns da undies kadai na debo kuma fa aiki yazo yi ba wai hutu muka zo ba" Umaimah ta fada
"Ai shikenan ki zauna kar kiyi gyara kinji idan baki fara tun yanzu ba ya zamar miki jiki sanda jikin naki yake da buqatar gyaran bayi zakiyi ba dan baki saba ba a shegen halin son jikinki da qazanta ma ai ke kam dole a ringa miki garambawul din akai akai, saura kije ki zauna masa shabar kamar buhun masara kina sana'ar danna waya dan jiya naga last seen dinki har kusan dayan dare toh ki shiga hankalinki, idan zaki ware ki ringa masa salo da kisisi na kala-kala yaji kamar karku dawo gida, inda ba hutun yake so kuyi ba in iya aikine ai shi kadai zeyi tafiyarsa.
Idan yaji dadin tafiya dake kinga shikenan kin samu lasisi duk inda zashi kina gefensa idan ba haka ba kuwa kina kallo zeyita yawace yawacensa kina gida kina masa gadi" Maman Asad ta sake fada kafin sukayi sallama ta kashe wayar tana sake jaddadawa Umaimah da tayi kwalliya ta daukar magana kafin ya dawo, idan ma bata da kaya ta zauna da Towel shima duk cikin salon gayun ne.
Hamshaqiyar kuwa kofi ta cika da lemo tana sha ta koma WhatsApp suka ci gaba da cece kuce tana kumfar bakin babu macen data isa ta kula mata miji,
"Ai ni mijina dan ni kadai aka yi shi babu kuma macen data isa ta rabeshi a duniya idan ta wuce uwar data haifeshi se yan uwansa da suke ciki daya, duk wata mace bayan wannan tace zata tsallaka hurumin Mijina toh kuwa ta taro yaqin da ze qarar da danginta kaf bama ita kadai ba, shima ya sani ba kuma zeyi gangancin saka yar mutane a masifa ba dan na rantse da Allah zan iya halaka yarinya sedai duk abinda ze faru ya faru shi da kansa ya fada ni kadai na ishe shi" Umaimah ta tura da voice note.
Sabon cece kuce ne ya tashi, masu goyon bayanta suna yi masu nuna mata kuskurenta da cewa ta rage zafin kishi sunayi, wata me suna Rabi'atu dake da rabon karbar nata kason rashin mutunchin tabi Umaimah Pc tace mata
"Haba baiwar Allah kamar ba musulma ba ki ringa iqirarin halaka wata akan kishi ko dauki dakon rai, ba a aure ke ya aureki? Kinga ai bazaki fitar da ran wata rana ze sake gano wata yayi sha'awar auranta ba kawai dai kiyi addu'a idan Mijinki nada rabon qara aure Allah ya hada kanku ya bashi ikon yin Adalci amma irin wannan kalaman ai idan kika zamu wata yar tijarar irin ki tsaf zata iya cewa ita kuma zata nemi mijin naki taga yanda zakiyi".
Zabura Umaimah tayi daga kwancen da take ta miqe tsaye tana qara karanta saqon daga baquwar lamba kafin ta shiga mayar mata martani da cewa
"Nice yar tijara? To uwar data haifi Uban Kakarki itace Tijararriya kuma da zaki ce wata ta nemi Mijina kai tsaye ki fito kice ke zaki auri Mijina, idan baki fasa neman Mijina kin aure shi ba ke tsinanniyace kuma uwarki shegen ki tayi ta kaiwa ubanki, ni kuma ko sunan Mijina naji kin kama a bakinki ballantana ta kaiki ga neman inda yake sena nuna miki ni Umaimah na haifu kuma ina fada da cikawa idan kuma keep na ganin wasa nakeyi ki gwada".
"Allah ya shiryeki idan kina da rabo kuma in sha Allahu se an miki kishiya ko dan kiga iyakarki" Matarta sake tura mata kafinta danna mata block dan bazata iya da dingimemen tashin hankalin Umaimah ba.
Hohoho ina wuta Umaimah ta jefata? Wasu mulmulallun Ashariya masu maiqo ta shiga antaya mata amma ganin da tayi messages din basa tafiya alamar tayi blocking dinta kenan yasa ta koma group tayi tagging sunanta taci gaba da zaginta tana sake nana ta mata idan ta cika mara kunya ta fada mata inda take ita kuma zata zo ta sameta ita dai baiwar Allah yayi tsit dan taga abin yafi qarfinta yan group nata bawa Umaimah haquri masu fushi da fushin wani da basu san kan zance ba suka shiga tayata tagging matar suna zagi, a cewarsu baze wuce ta bita Pc bane zatayi mata wa'azinta na munafunci data saba ai gara haka yau ta jangwalo wadda tafita baki ita dai mata da taga babu sarki se Allah babu bata lokaci ba tayi left daga group bayan data sake cewa Umaiman
"Ko iya wannan jahilin kishin naki ya isa ya saka ayo miki kishiya kuma kina ji kina gani ze samo kamilar mace me aji ba ballagaza me zage zage a social media ba" tana turawa ta arce daga group.
Kiran layin matar Umaimah ta shigayi tana jin zuciyarta kamar zata fito saboda tsabar baqin ciki, ita zatayiwa wannan cin mutunchin? Ai kuwa duk inda matar nan take seta nemota taga ubanda ya tsaya mata se kuma ta nuna mata ita ba kanwar lasa bace.
Wayar taqi shiga ta gwada da dukka layukanta guda uku bayan wanda take chatting dashi dan daman tasan dole zatayi blocking nata amma duk a banza basu shiga ba, kwafa tayi ta jefar da wayar ta zauna tana jijjiqa qafa a zuciyarta tana ayyana ta inda zata binciko matar nan.
Da ace Yaya Aminu mutumin kirki ne shi zata bawa Lambar ya nemo mata ita tunda shi jami'in tsarone amma tasan seya tsareta da tambayoyin jin ba'asin abinda yasa take nemanta qarshe idan magana ta fashe itace a ruwa dan tasan babu me goyon bayanta dan haka dole tasan ta ina zata zaqulo matar nan dan wallahi bata zagi bulus ba.
Tana kallon Halima na kiranta a waya tayi banza da ita dan tasan baze wuce labari ya isar mata na abinda ya faru a group din ba tunda bata Online ita, tana zaune nan zaman saqa da warwara har bata san lokaci ya tafi ba sejin motsin bude qofa tayi ta zabura ta miqe tsaye tana kallon kanta da gurin da take zaune kwanukan abincin data ci na nan a bude ko murafen bata iya mayarwa kai ba bare aje ga kawar dasu gefe ga lemon da take sha ma ashe ta ture shi ya zube a garin masifa bata sani ba ya bata farin centre carpet din dake dakin seta juya ta kalli Khalil dake takowa zuwa inda take, ganinsa tayi tas sam beyi kama da wanda ya fito daga Site ba inda ake aikin Yashi da sumunti se ji kawai tayi hawaye na ziraro mata