← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 213 OF 267

Sashe 213

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun bayan fitowarsa daga Asibiti ya fito da qudurin cewar zamansa da ita bame yuwuwa bane domin ko a shari'an ce akwai cutarwa tunda har yasan bashida lafiyar da zero ci gaba da biya mata buqatarta dole ya sallamata ta auri wani tayi rayuwarta shi kuma ze rungumi qaddara ya cigaba da rayuwarsa harzuwa iyakar abinda Allah ya hukunta masa. Bayan komawarsa gida irin yanda take kula dashi take ririta shi ya karyar masa da zuciya, idan ya kalleta tausayin ta yakan narkar dashi ko kadan bata taba nuna alamar gajiyawa ko wata damuwa da abinda ya sameshi ba. A duk sanda taga yayi shiru ko yana tunani se tayi duk iya qoqarinta na ganin ta kore masa damuwa tareda qarfafa masa guiwa. Watansa biyu cikin wannan yanayin ya warke garas a zahiri tunda dama ba lalura bace da za'a gani a jikinsa har ya ci gaba da fita ayyukansa amma a cikin zuciyarsa rauninda Umaiman ta rigada tayi masa ya gaza warkewa. Duk sanda ya kalli dakinta se yaji wani abu ya dake shi ya kan zargeta da son rai da ace tayi haquri ta fawwalawa Allah lamuranta da yanzu suna zaune tare yaransu kullum cikin tambayarsa ina Momy take suke tun yana samun abin da ze gaya musu har suka haqura suka dena tambayarsa musamman saboda yanda Humairan take iya qoqarinta akan su, jansu takeyi kamar qannenta har wasan goyo da guje guje sukeyi abinda yake dauke musu kewa kenan har suka fara dena damuwa da neman uwarsu se lokaci lokaci.

Dukda irin kwanciyar hankali fa nutsuwar da yake samu tattareda ita zuciyarsa taqi nutsuwa akan yaci gaba da zama da ita a yanda yake, baya so Allah ya kama shi da haqqinta Humaira yarinya ce qarama da bata gama sanin menene auren bama tukunna. A yanzu yasanbe zama lallai ta damuda halinda yake ciki ba amma ana tafe dole za'a kai lokacin da zata fara buqatuwa da Namiji shi kuma bashi da lafiyar da ze biya mata wannan buqatar daga nan fitina zata iya bullowa wadda baya fata, domin gujewa hakan tilas ya samar musu maslaha ta hanyar rabuwa da ita koda ace hakan zeyi sanadiyyar da shi ze qare rayuwarsa cikin qunci kamar yanda Umaiman take fata.
Yanke shawara yayi akan fara samun Hajiya da maganar kafin ya aiwatar dan haka ranar bayan ya dawo daga aiki kai tsaye ya wuce gurin Hajiyar.
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 75

A falo ya tarar da Humairan da Habiba suna hira, yabita da wani malalacin kallo saboda yanda kwalliyarta ta dauke masa hankali yaji gaba daya ya rasa kwarin guiwar daya shigo da ita. Seda ta waiwaya ta kalli Bene kafin ta taso da sauri ta rungumeshi ya dagata sama dan tsahonta be kai kafadarsa ba yayi pecking lips dinta da suka sha Red lipstick kafin ya ajiyeta ya kalli inda Habiba take ya ga ta bar gurin kawai ya saki murmushi. Wannan yar babyn tana sakashi yin abin kunya a gaban Qannensa ta kama hannunsa tana murmushi tace
"Yau ka dawo da wuri, yanzu nan fa na shigo nace na rage lokaci kafin lokacin dawowarka yayi ka shiga can bana nan shiyasa ka taho nan?"

Hancinta ya dan ja yana qare mata kallo ta qara qiba da haske tayi kyau sosai ya zauna akan kujera ta zauna a gefensa yana ce mata
"Missing dinki nake tayi shiyasa na taho gida da wuri, ina Hajiya na ganku ku kadai?"
"Yanzun ta hau sama bari na gaya mata ka dawo" ta miqe sega hajiyar ta fito ta sakko qasan tana masa sannu da zuwa zame daga kan kujerar ya gaisheta ta amsa itama tana tambayarsa ya akayi yau ya dawo da wuri yace mata aikinr babu sosai. A kitchen din Hajiya ta dakko ruwa da Lemo ta kawo masa ya karba qasa qasa ya furta mata
"I love you" tayi qasa da kanta tana zuba masa ruwan Hajiya dake kallonsu tayi murmushi a ranta wani dadi yana qara mamayeta. Idan ta kalli Khalil da Humairan tana tsintar kanta cikin matsanancin farin ciki harta ce inama tun farko ita ya aura ba Umaimah ba? Ita ce irin matar data dade tana yiwa Khalil dinta addu'ar Samu a rayuwarsa se gashi al'amari mara dadi ya biyo bayan Gamuwarsu tana fatan hakanya zama wani Alkhairi a gabada basuyi tsammani ba.

Yana gama shan ruwan ya miqe yana cewa Hajiya bari yaje anjima ze shigo akwai maganar da zasuyi, suka fita tare ta daukar masa jakar sa. A bakin qofar ya fizge jakar ya ajiye ya dauketa kamar yar tsana ya haye sama da ita tana fizgewa da shagwabar ita ya sauketa be direta ba se akan Gadon dakinsa ya bita ya danneta ya sakar mata nauyi yanda yaga tana kokawa da numfashi ya sakashi saurin dagata yana cewa
"Yarinyar nan bakya motsa jikinki gashi nan qiba ta fara miki yawa har kina haki daga an dan wujijjigaki".

Baki ta tura masa tana qunquni ya kuma kama bakin nata ya shiga kissing nata passionately badan yana jin komai ba. Seda yayi sosai kafin ya cire bakinsa daga naya ya kalli fuskarta ganin ta rufe idonta yanayinta ya nuna tana jin dadin abinda yayi mata, a hankali ya saketa ya shiga qoqarin miqewa still idonta a rufe ta sake shigewa jikinsa be gama mamakin abinda tayi ba se ji yayi ta sake maida bakinta cikin nasa tana biya masa haddar abinda ya koya mata. Kasa yin komai yayi kawai ya bude ido ya kallon yanda takeyi cike da mamakinta. Har sannan idonta a kulle ta kama Hannunsa ta ta dora akan qirjinta da suka qara cika gabansa ya yanke ya fadi abinda yake gudu har yazo kenan, seda ya hadiye wani yawu kafin ya tattaro duka nutsuwarsa ya shiga yi mata abubuwan da yasan zasu bata nutsuwa dukda bayajin komai a tattare da abinda sukeyi din. Tausayinta ya kama shi ganin yanda jakinta yake rawa, yayi iya yinsa gurin ganin ya gamsar da ita ta hanyar amfani da hannayensa da kuma bakinsa har seda ta samu gamsashshiyar nutsuwa se kuma ta kife a jikinsa ta fasa masa kukan da kana jinsa kasan na zallar shagwaba ne yayi yayi ta dagashi taqi ita a dole kunyar sa takeji abinma ya bashi dariya dakyar ya rabata da jikinsa ya shige bandaki jin ana kiran sallar Magriba.

Seda yayi wanka tareda Alwala zuciyarsa cike da zullumin abinda ya faru. Qirjinsa ya ringa bugawa duk yanda yake da jaraba ace yau gashi ga mace a cikin irin yanayin da yake so amma ace beji komai a kanta ba. Hawaye ya digo masa me zafi daga ido daya ya share yana jin wata tsanar Umaimah da be taba zaton zeyi mata irinta ba ta taso masa ita ce sila ita ta janyo masa ya zama mara amfani dashi da dutse yanzu marabarsu kadance tabbas Umaimah ta zalunce shi kuma ta zalunci Humaira yanzu ta yaya zama ze yuwu a tsakaninsu bama ita ba da duk wata lafiyayyar mace da ze aura ko ita kanta Umaiman a yanzu yasan babu abinda zatayida shi tunda ta rigada ta kassara abinda takewa wasu baqin cikin samu a gurinsa.

Qofar da Humairan ta buga masa ta sakashi qarasa wankan ya fito fuska babu walwala ya wuceta ta bishi da kallo jiki a sanyaye kafin ta shiga wankan itama tana mamakin meya bata masa rai? Haka tayi wankanta ta fito tana shafa mai tana tuna abubuwan da yayi mata. Da hannu biyu ta rufe fuskarta saboda kunyar yanda ta sako jiki harda fa wani kuka ta ringayi ita wlh bata ma san meya shiga kanta ba da har ta shishshige masa.
"Amma fa akwai dadi na yau daman ya iya irin haka shine yayi mun na mugunta kwanaki?" Ta fada a fili kamar me magana da wani. Tana saka kaya tana tunanin ya warke kenan ma tunda takamaimai fa ita daman ba wai ta san meye ciwon da yake damunsa bane qarancin shekarunta be barta ta fahimci illar da ake iqirarin Umaiman tayi masa ba ita dai tasan ta buga masa abu a ciki shikenan. Tsaf ta shirya cikin qananan kaya ta kalli kanta ita kanta ta lura da qibar data yi sosai fa abin ya mata dadi tunda daman ai shi so yakeyi tayi qibar seda ta gama shiryawa kafin ta zura dogon Hijab akan kayanta tayi sallah. A gurin ta zauna har akayi isha tayi tareda shafa'i da wutri kafin ta cire Hijabin ta sake gyara jikinta ta wuce bangarenta ta dakko Baqar Abaya ta dora akan kayan jikinta kafin ta sauka qasa. Ta rigada tayi girki tun tuni, qara gyara kwanukan tayi ta ciro Jug din Zobon data hada daga Fridge da ruwa ta ajiye komai ta koma cikin falon ta zauna tana kallon Tv a ranta tana tunanin to se yaushe kenan Umaimah zata kwashe kayanta tunda an saketa gashi kusan wata nawa har yanzu kuma ba' acire komai ba.

Khalil kuwa seda yayi sallar isha'i kafinya koma bangaren Hajiya, tayi masa tayin abinci ya girgiza kai yana sosa qeya, Hajiya tayi murmushi ba tareda tace komai ba. Qara gyara zama yayi fuskarsa na qara bayyanar da damuwar da yake ciki yace
"Hajiya daman maganar da nace zamuyi akan Humaira ne"
"Toh me kuma ya sameta?" Hajiyar ta fada tana gyara zama se yayi qasa da kansa saboda nauyin maganar da ze fada din kafin ya fara magana cikin sanyin murya yace
Chapter 213 · 0% Book details