← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 176 OF 267

Sashe 176

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh Hajiya duk yanda kukayi ai daidai ne, ita kuma batajin dadi ne. Bakiga yanda duk ta kumbura ba kuma nayi nayi da ita muje Asibiti taqi wai lafiyarta qalau"
"Toh subhanallahi Allah ya bata lafiya amma dai ya kamata ta daure kuje din dan kumburin idan yayi yawa bashi da dadi gara a gane koma menene sikarsa tunda wuri a magance. Shi yasa nace ka ringa binta a sannu da maganar auran nan saboda yanayin da take ciki Allah dai ya raba lafiya" Hajiya ta sake fada aga nan sukayi sallama ya kashe wayar.

Zancen Hajiya Hauwa da tayi yasa ya tuna da Humairan ma dan shaf kamar an shafe masa ita daga tunaninsa gaba daya. Office dinsa ya koma ya zauna, a maimakon ya kira Humairan seya danna number Umaimah. Seda wayar ta katse ya sake kira shima kiran na dab da katsewa kafin ta daga murya can qasa kamar me bacci.
"Bacci kikeyi na tasheki ko?" Ya tambayeta a sanyaye, cike da Izza kamar wata basarakiya tace masa
"Bacci nakeyi, kuma dakyar na samu ya daukeni gashi yanzu ka tadani".
"Allah ya baki haquri ki kwanta kiyi baccinki, idan kuma yaqi sake daukanki ki kirani se nazo na lallabaki kiyi kinji" ya fada jikinsa har yana rawar daya rasa dalilinta.

Qaramin tsaji taja kafin tace
"Nidai ka katse mun baccina haka kawai me zanyi maka toh?"
"Babu komai kawai so nakeyi naji ya kike, sannan Yara sun shigo qofa a kulle idan kin tashi se ki kirawo su ko na zatama kin shiga kun gaisa da Hajiya ai" yanda yake maganar kamar wani me tsoronta ko tsoron fadar wani abu daze bata mata rai, baki ta tabe kamar yana ganinta tace
"Idan na tashi naji daidai zan shiga ai kasan bana jin dadi dai" se yayi saurin cewa
"Na sani, to kiyi kwanciyarki ki huta idan na dawo se mu shiga tare kawai ba se kinje ba".
Sallama sukayi ya ajiye wayar yana sauke numfashi, shi dakansa yasan abinda yakeji is unusual, wata muguwar shakkar Umaiman yakeji da ya rasa ta mecece. Humaira ce ta fado masa a rai seya dauki wayar ya kirata dukda yanda zuciyarsa ke qoqarin hanshi tana nuna masa ran Umaimah fa ze baci idan ta gano yayi waya da wata. Seda wayar ta kusa tsinkewa kafin ta daga wayar da sallama ya amsa se tayi shiru
"Fushi kikayi" ya fada a sanyaye, shiru tayi batace masa komai ba seya gyara zamansa yana sake yin qasa da murya yace
"Haba qanwata yanzu fushi kikeyi da yayan naki ba zakiyi mun uzuri ba bayan kinsan aiki nakeyi tuquru saboda in tara kudin auranki?"

Bata amsa shi ba dan haka ya sake cewa
"Haba mana Umaimah ta kiyimun magana naji muryarki ko zuciyata zatayi sanyi kinji Autar Mata" kamar tana jira se ji yayi ta fashe masa da kuka harda shashsheqa,a rikice ya miqe daga kujerar da yake zaune ya shiga zaga office din yana salati tareda tambayarta abinda ya faru me ya sakata kuka.
"Ni daman nasan ba sona kakeyi ba shiyasa ma tun jiya kake tayi mun wulaqanci na kiraka kaqi dauka duk message din dana tura maka babu reply sannan yanzu saboda ka nunamun ka fi son matarka bana gabanka harma manta sunana kayi kake kirana da nata" Humairan ta fada dakyar tana kuka.

Dafe bakinsa yayi jin abinda ta fada, yaushe akayi haka ya kirata da Umaimah shi wallahi be sani ba bema yarda ya fada ba amma yasan idan yace ze tsaya kare kansa rigimar ba qarewa zatayi ba dan Huamira yar daruce itama idan ta murde dan haka cikin rarrashi yace mata
"Kiyi haquri wallahi idan ma na fada banyi dan na bata miki rai ba, yanzu muka gama magana da ita a waya inaga shiyasa sunan yazo bakina ban sani ba kiyi haquri kinji Shatuna ki yafewa Yayanki kuma ni ba ina sane duk naqi daukar wayarki ba akasi aka samu amma kiyi haquri".

A maimakon tayi shiru sema qarawa kukanta amo tayi tana cewa
"Oh daman da ita kake waya nayita kiranka kanaji baka amsa ba ai dai ko second biyar ne seka dauka a gunta kace mun zaka kirani aidai zansan ka damu dani ba kayita share mun waya ba tunda dai naga nima din matarka zan zama"
"Humairah kishi, toh kiyi haquri bazan sake ba daga yau koda qa nake qaya indai ba Hajiya bace zan dauki excuse na amsa wayarki shikenan?" ya fada cikin lallashi da mamakin yanda take magana yau, rage kukan tayi nan ya shiga aikin rarrashi, besan adadin lokacin daya kwashe ba seda Anwar ya shigo office din yana gaya masa lokacin shigarsu Meeting yayi sannan ya ankare da a qalla sunfi awa daya suna waya. Sallama sukayi bayan da yayi mata Alqawarin daya tashi ze biya ya ganta saboda ya qara wanke laifinsa sannan ta haqura ya kashe wayar.

"Kai Subhanallahi" ya fada yana dafe kansa, shikenan idan wannan ta garo shi ta nan se waccen ta bugo shi ta nan kenan to Allah ya bashi wuyan dauka.

UMAIMAH
Suna gama waya da Khalil ta miqe daga kan gadon ganin daya ta gota, seda tayi sallah kafin ta fita zuwa kitchen. A Freezer taga saqon da aka siyo mata gashi nan kan guda ba'a fada ba ta ciro ta ajiye shi cikin sink tana toshe hanci saboda qarnin da ya fara hawar mata kai. Safina ta kira ta sake tambayarta yanda zata dafashi ta gaya mata seta wuce dakinda Ruqayya take ta sameta ta idar da Sallah tana lazumi.

"Idan kin gama ki sake wanke kan can ki dora ki hadashi duk yanda kikeyi idan ya kusa dafuwa se ki gaya mun amma fa kar a fasashi na gaya miki"
"Toh Hajiya sedai sun zazzage kwakwalwar a can ban sani ba ko anyi laifi?" Ruqayyan ta fada se tayi gaba tana cewa
"Babu damuwa ki hadashi yanda nace.
Haka kuwa akayi tsaf Ruqayyan ta hada Kan a qatuwar tukunya tana yi tana mitar meye dalilin da za'a dafa kai sukutum se kace na tsafi danma pressure pot din tasu nada girma ta dauke shi, seda ya dakko dafuwa kamar yanda ta buqata taje ta sanar mata.

"Ki wanke mun bandaki amma kar ki saka Hypo bana son warinsa" ta fada tana miqewa Ruqayya ta bita da kallo, ta rasa gane alqiblar uwar dakin nata. Dazu data gyara dakin ita tace ta bar bandakin karta wanke yanzu kuma tanaso a wanke kai wannan yarinya dai kamar me juju haka ta shiga aikin tana mita ita kuma ta wuce kitchen din. Tsaf ta barbade naman da garin maganin da Malam ya bata, ta debi romon ta dandana seda ta hadiye kuma ta zaro ido
"Kema zaki iya ci" kalaman malam suka dawo mata se sannan ta samu nutsuwa harta hadiye yawun data fara tattarowa dukda romon ya rigada ya shiga cikinta. Mayar da murfin tayi ta rufe ta koma palour ta zauna. Saboda ita ta saka kanta zama tayi har naman yayi laushi sosai lokacin Ruqayya ta gama tace ta farfasashi a raba a zubawa kowa nasa harda su Hajiya da Sammani. Ba sabon abu bane dan haka Ruqayyan bata kawo komai a ranta ba tayi yanda tace ta zubawa kowa. Umaiman da kanta ta dauki na Hajiya ta saka Hijabi ta fita dashi, Ruqayya kuwa Buredi ta dauka ta zauna taci abunta tana dangwalar romo, ta huta da tunanin me zataci da rana kafin a dora girkin dare dukda ba wani abu zatayi da daren bama doya kawai zata soyawa Oga yaci da Romon kan tunda an ajiye masa.

Da sallama ta shiga falon Hajiyar, seda tayi qoqari ta daidaita fuskarta babu yabo babu fallasa ta zauna akan kujera Khalifa dake aiki a Laptop dinsa ya gaidata ta amsa tana tambayarsa Hajiya yace tana kitchen sega Hajiyar ta fito Umaiman ta zame qasa ta shiga gaidata ba tareda ta bari sun hada ido da Hajiyar ba.

"Sannu Umaimah" Hajiya ta fada tana zama kafin taci gaba da cewa
"Dazu yake gayamun bakya jin dadi ai ban dauka kumburin yakai haka ba kuma kike zaune ba zakuje Asibiti ba haka ai be kamata ba gaskiya idan ya dawo kuje kiga likita asan abinda yake damunki".

"Munafuka se kace ta damu dani" Umaiman ta fada a zuciyarta a fili kuwa ta qara rausayar da kai tace
"Ai jiya naje Hajiya sun dubani sunce babu komai kawai na ringa motsa jiki sosai" seta tura mata Flask din Naman tana cewa
"Gashi Hajiya sha'awar Naman kai nayi shine na dafa daku".

Hajiya taja flask ta bude qamshi ya cika falon tace
"Madallah mun gode Allah yayi Albarka, aida baki wahalar da kanki ba kinyo waya ko Khalifa se yazo ya karba tunda Habiba basa nan sun fita da yaran wai zata kaisu Shoprite"

"Ba komai ai na motsa qafata nima" Umaimah ta fada tana dan murmushi. Hira suka shigayi jefi jefi, Hajiya naso ta kawo mata zancen auran Khalil tana tsoron abinda hakan ze iya janyowa dan haka ta kama tsufanta tayi shiru ita kuwa Umaimah jira kawai takeyi Hajiya taci naman ta kama gabanta dan ba dadin hirar takeji ba, a zuciyarta ko banda antaya mata zagi babu abinda takeyi. Me aikin Hajiya ce ta fito da Fulasan abinci data gama Hajiya tace
"Kinga zubomun farar shinkafar naci da Romon nan, kaima Khalifa idan zakaci gashi nan"
"Aa nikam Alhamdulillah" Khalifan da be saka musu baki ba tun dazu ya fada, Umaimah ta galla masa harara a fakaice ita dai Hajiya aka kawo mata shinkafarta ta zuba abunta ta fara ci tana cewa
"Ka huta ai, na ajiyewa su Auta sauran idan sun dawo suci".

Baya bar gurin Hajiya ha seda Jalilah ta shiga da sallama Sammani na biye da ita da uwayen ledoji niqi niqi kamar wadda ta siyo kasuwa gaba daya. Tana shigowa Umaimah ta miqe, kallon banza suka jefi junansu dashi ta wuce fuuu Jalilah taja tsaki tana qarasawa cikin falon Hajiya ta kalleta tace
"Meye haka Jalilah ya zaki shigo ki harari yarinya har ki bita da tsaki? Wani ni se yaushe zaki dena wannan halin da kika samu duk kinbi kin kwarzabeta na tabbata yanzu ma shigowarki ta sakata fita ba wani abu ba".
Chapter 176 · 0% Book details