← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 267

Sashe 8

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa Hajiya tayi da mamaki jin ya kama sunanta, "ka santa ne daman?" Ta tambaye shi tana tsare shi da ido. Seya duburburce, ya manta shaf da halin Hajiyar tasa, yanzu abinda be faru bama tunda akayi haka seta qullo shi wai wa ma ya aike shi nuna ya santa ne? Koda yake yarinyarce, ta shige masa yanda beyi zato ba.

"Magana nake maka ka tsareni da ido kayi shiru, ko baka ji me nace bane?" Ta fada ganin gaba dayama hankalinsa baya gurin, se yayi firgigit yana shafa kai yace

"Aa fa Hajiya ni ban san ta ba, sau daya na taba ganinta dalibar Nasir ce ranar dana je makaranta gurinsa na ganta a office din shine fa naji ya fadi sunanta se kuma dazun na ganta a compound wai an aikota amma ba wani abu daban bane da kike tunani"

"Toh ni me kaji nace Babana, yarinyar ma ai ta gidace qanwar Hajiyayye ce kuma dai kai shaidane akan nagartar Hajiyayyen tunda Mijinta kusan abokinka ne kaima kana yabonta, babu komai Allah ya tabbatar mana da Alkairi" Hajiyan ta fada tana murmushi me kama da dariya saboda murnar wannan al'amari, ita daman tunda taga yarinyar tayi mata, harta fara saqa yuwur hadi ta da Khalil din nata se gashi ma ashe tuni Allah ya hada abinsa, to Allah yasa abokiyar arziqi ce.

Khalil da gaba daya ya rikice jin Hajiya na neman kwanto masa ruwa ya miqe yana cewa
"Nifa Hajiya ba wani abu tsakanina da ita idan baki yarda bama ki aika a kirawota kiji idan ko sunana ta sani karma ki kawo wannan maganar" ya fice da sauri kafin ta kwanto masa wata kurar.

"Ja'iri, ai har na fara tunanin kodai baka da lafiya ne ace mutum shekara Talatin da dori amma babu wanda zece ya taba ganinka a qofar wani gidan da sunan kaje zance, to yanzu hankalina ya kwanta, bari na kirawo yan uwanka na shaida musu abin arziqi sannan na kirawo kawunka ma na fada masa dan da zafi zafi ake duka qarfe" Hajiya ta fada, nan ta shiga kiran Habiba akan ta kawo mata wayarta, Habiban na cewa

"Oh Hajiya kina jin fa abinda yace shine zaki fara yayatawa se yazo ya baki kunya daga baya"

"Ke dallah tafi can kece baki gane borin kunya yake ba, amma daman ina kallonsa dazu nasan da wata a qasa itama baki ga duk a takure take ta kasa sakewa ba? Ga yarinyar kuwa tabarakallah kyakykyawa da ita ga nutsuwa Allah yasa ta dore da haka"

Ita dai Habiba dariya ta ringayi tana kallon ikon Allah dan dagaske Hajiya take, waya ta ringa kiran yayanta kaitsaye gaya musu take Khalil ya samu mata su fara shirin biki kowacce aka fadawa kuwa nan zata hau murna a fara lissafin abinda zaayi da auran nasa.

Tana komawa gidan wanka ta fada dan saurin da take tayi daman su Fauziyya ne zasu zo wa Yaya Hajiyayyen barka, ta gama shirin ta tsaf ta shirya cikin wasu riga da skirt na Atamfa da suka matuqar yi mata kyau. Bata daura dankwali ba se hula ta zura akanta ta fesa turare ta fito palor inda Yaya Hajiyayye da Anty Larai dake taya ta da wasu aikace aikacen suke zaune suna hira.

"Dan Allah Umaimah goya yarinyar nan bacci zatayi take ta rigima" Hajiyayyen ta fada tana miqa mata Ummu-Salma seta ja da baya tana cewa
"Tabdi haka kawai daga fitowata kice wani in goyata in bacci zatayi a kwantar da ita mana tayi kawai tun jiya nake goyata da daddare kusan kwana tayi a bayana gashi yanzu tasa mun ciwon baya".

" yanzu Umaimah wannan abar da bata fi nauyin pure water ba ce ta saka miki ciwon baya kedai kiji tsoron Allah, koda yake kamar yaune kema kin kusa ki haifi naki se naga uban da ze goya miki ba ciwon baya ba wannan ko ciwon qunquru duk ya hada ya saka miki" Anty Larai ta fada tana miqewa ta karbi yarinyar tace

"Kema neman magana yasa kika ce ta goyata ai, tun dazu da kin bani ita da yanzu ta dade da yin baccin ai" ta saba yar a baya ta daure da zani.

"Gani nayi kin sha aiki da yawa ai Anty ita kuwa babu abi da tayi, ina jinta dan iskanci cewa tayi inta taba danyan nama kanta ciwo yake amma kin iyaci idan an soya ko?" Hajiyayye ta fada tana Hararar Umaimah, ko a jikinta ta zauna kusa da ita tana latsa waya, ba jimawa suka jiyo sallamar su Fauziyya Umaimah ta fita da dan gudunta ta taro su.

Seda suka gaisa da Maman Asad kafin suka qule a dakin da Umaiman take, se yaba haduwar gidan suke dan sabon gini ne suka yi ko shekara basuyi a cikinsa ba.

Basu tashi tafiya ba se dab da magriba suka fito bayan da suka sake kwalliya kowa ta baza turare aka kashe daurin dankwali.

"Bazaku bari ayi sallah ba zaku tari goshin magriba ku fita" Maman Asad ta fada tana qare musu kallo,
"Bari kawai muje Anty, Allah ya raya a gaida su Asad da Mimi" suka hada baki gurin fada

"Zasuji suna gidan qanwar Babansu hutu, ki duba kitchen ki daukar musu kullin nama" ta fada kafin ta shige daki ta barsu tsaye suna jiran Umaimah data tafi kitchen.

"Ke ai irin unguwar nan dab da magriba ne kake ganin mutanen ciki ta, kinsan yan gayun nan basa yawo a rana yanzu ne daidai masu fita sallah sun fito masu dawowa daga aiki suna shigowa da qafa zamu taka har titi ko Allah ze sa mu dace da rabo" Nabila ta fada tana rarraba ido tana qarewa qerarrun gidajen unguwar kallo, unguwa ce ta yan gayu me kyau da tsari,

"Kedai Allah ya shiga lamarin ki Nabila naga alama kina neman zaucewa akan neman Miji, koda yake tsarin da kika dakko ne bame bullewa ba kin tsaya ke se hamshaqin me kudi bayan su kuma ba irin ki suke so ba" Fauziyya ta fada tana qunshe dariyar dake son kufce mata saboda yanda Nabilan ke faman rangwada da karairaya se jefa dogayen qafafunta take ala dole tana yanga.

"Wallahi Fauza zan miki rashin mutunchi, idan Allah ya kawo munme kudin dan Allah ki hana shi aure na banza yar baqin ciki" ta fada a fusace tana kallonta, har Fauziyyan ta bude baki zata bata amsa Umaimah ta dakatar dasu tana cewa

"Malamai ya ishe ku zaku fara halin naku kamar kaji, ke kuma sauka daga titi kafin ya rage miki farashi" ta qarasa tana kamo Nabila gefe saboda hango Khalil daya fafaro mashin dinsa kamar ze tashi sama.

"Wannan kamar guy din nan na office din Sir Nasir" Nabila ta fada tana binsa da kallo se Umaimah ta gyada kai tace
"Tabbas shine, daman ina ta tunanin ina na san fuskar sa ashe saurayin Nabila ne" ta fada da sigar wasa.
Baki Nabilan ta tabe tace

"Wallahi ya hadu kawai dai matsakar sa rashin chanji, kome yazoyi nan oho qila gidan su wani abokin nasa yazo" tayi tambaya ta bawa kanta amsa duk ita kadai se Umaimah ta nuna mata gidan su tana cewa

"Kinga gidan su can, ko zaki shiga ki gaida surukarki"

"Aa kakan surukata banason wulaqanci" daga haka suka ci gaba da tafiya har ta raka su bakin get din layin kuwa babu wanda yace musu tafi ku mutu dukda ga Maza nan samari da magidanta suna ta qoqarin Shiga masallaci dan an kira sallah kota kansu basu bi ba. A bakin Get din tayi musu sallama ta juya.

A qofar masallacin taga Khalil yana alwala ya bita da kallo ta galla masa harara se ya sakar mata murmushi ba shiri ta dafe qirji jin zuciyarta ta buga da qarfi kamar wadda ta tsorata. A haka ta shiga gidan faran faran kamar wadda aka biyo saboda yanda taji gaba daya zuciyarta na tsere kanta har wani sarawa yakeyi.

"Ke lafiyar kuwa kika fadowa mutane babu ko sallama" Maman Asad ta fada tana qare mata kallo, se Umaimah ta kalleta tace

"Inaga Gamo nayi, wani mutum na gani, kai ba mutum bane Aljanine" ta fada kamar me tantamar abin

"Idan ma rauhanine zaki gani ai, saboda baku da hankali da magribar nan haka kuka kwashi qafa kuka fita, ni sam bana son wadannan qawayen naki gaba daya basu da nutsuwa har gara gara Halima a cikin su daman amma wadannan biyun bansan wadda tafi wata rashin hankali a cikin su ba"

"daga abin arziqi kuma shine zaki zagesu yan gidan mu nawa suka haihu basuje musu barka ba seke, daman mantawa nayi baa miki abun kirki dama basu zo ba" Umaimah ta fada tana zumbura baki,

"Da suka zo din uwar me na qaru da zuwan nasu fitsararriya? Ki shiga hankalinki idan ba haka ba kuma sena hadaki da Abba ina daman an raba ki dasu kinqi ji ko? Shikenan" Hajiyayye ta fada tana wuceta, Umaimah ta rakata da harara, wallahi badan tafi samun yanci anan ba da gidan su zata tafi haka kawai mata ta sakata a gaba ta ringa mata masifa daga an mata abin kirki anzo mata barka? Ai shikenan maganin ta itama gobe ta qara.

Haka rayuwa taci gaba da mirginawa da dadi babu dadi Umaimah na zaune gidan Hajiyayye har Sukayi arba'in ranar kuwa bata qara kwana a gidan ba ta tattara ta wuce dan daman tuni taso tafiya Mama ce ta hana saboda Anty Larai ta tafi qauyensu yarinyarta bata da lafiya gashi su Asad sun dawo daga hutu dan haka hidimomin sunwa Hajiyayyen yawa.

A dan zaman da sukayi ko fada anyi shi yafi sau cikin kwando, Umaimah rashin jiz Hajiyayye rashin haquri, haka zata biye mata suyita hayaniya musamman da Mijinta ba mazauni bane shiyasa Umaiman ke samun yanda take so.
Chapter 8 · 0% Book details