← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 267

Sashe 117

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai Umaimah duk abinda ya sameki ke kika jawa kanki, kuma ke ya kamata ki fara tausaya kanki. Ai baki duba halin da kice cikin ba ki ka dauko magana da yanzu badan Allah ya taqaita ba ai qila kina can kurkuku a kulle wayasan ranar fitowarki? Kuma har yanzun babu alamar kinyi nadama dan babu wanda kika nuna wa hakan ballan tana ki nemi afuwarsu su denadaure miki fuskar, ko kuwa zaman da kike a daki da qin cin abincin ne kike zaton ze saka su dakko su shiga harkarki? To idan ma dan haka ne gara tun wuri ki chanza tunani dan a banza zaki kashe kanki qarqari mu miki Addu'a idan mun tunaki" Maman Asad ta sake fada se kuwa Umaimah ta qara ware baki tana cewa

"Daman na sani duk ba qaunata kukeyi ba, fata ma kukeyi na mutu sabida na tsare muku wani abun sannan me qaunar tawa ma an shiga an fita an raba tsakanina dashi wallahi duk abinda mutum yayi shida Allah"
Dariya wauta da rashin hankalin Umaimah ya bawa Hajiyayye tana kallonta tace
"Halinki ne ba'a qauna bake ba, kuma shi me son naki da kike magana ke kika raba tsakaninku ai. Ke yanzu bakiji ko dar ba bakiyi tunanin mutunchinsa ba yanzu ace matarsa ce tayi abinda kikayi? Yanzu haka video ku yana nan yana zaga gari kowa yasan ta'asar da kika aikata dayawa kallon Mahaukaciya ma suke miki saboda kishi kin zubarwa kanki da Mijinki mutunchi ta ina kike tsammanin ze sake bi ta kanki? Ai wallahi kin wa kanki wauta Umaimag kuma kin barar da kanki a gurin Khalil na tabbatar yanzu a kaso dari babu ko Ashirin na So da girman da yake baki dan kin nuna masa baki san darajar kanki ba.

Nidai shawarar da zan baki ki maida hankalinki jikinki ki, ki ringa fita kina motsa jiki ki samu ku rabu da cikin jikinki lafiya kafin ki fara yaqin maido da kanki a gurin Khalil dan dai a yanzu nida ke munsan bakya gabansa" tana kaiwa nan ta fice ta bar Umaimah cikin tunani da neman mafita.

Kwana hudu da zuwan Maman Asad gidan ta tashi da naquda, guraren qarfe goma sukaje Asibiti cikin ikon Allah kafin sha biyun rana ta haifo kyakykyawar yarta itama me kama da Khalil. Seda ta uku a Asibiti saboda jini daya balle mata bayan haihuwar basu dukda komai ya daidaita suka qi sallamarta a cewarsu se sun tabbatar da lafiyarta saboda gudun kar wani abu ya sake tasowa bayan sun koma gida haka yan barka da dubiya suka ringa zarya a Asibitin daga bagaren ta zuwa na Khalil da har yanzu suke cike da jin zafin Umaiman Hajiya ce kadai take rawar jiki da ita dan kullum setaje Asibitin har aka sallame ta da ita suka koma gida ga tarin kayan barka data kawo dukda Khalil dinya gaya mata wannan karon ya bawa Umaiman Kudi ta siyi abubuwan da take buqata amma seda ta hado nata.

Fitowarta kenan daga wanka ta daura Zani sannan ta lullubo jikinta qaton towel, ta zaune a bakin Gado tana jin yanda jikinta daya daddaure yake saki, tunda ta haihu bata samu wanka me kyau ba se yau da safen saboda zaman Asibiti, jiya kuma da suka dawo dare yayi dan haka suka bari se yanzu da safe Anty Laure tayi mata wanka gangariya ta zane mata jiki da darbejiya kuma taji dadinhakan. Nuratu ta shiga dakin sabe da jaririyarta Aidah me kimanin watanni biyu ta miqawa Umaiman wayar hannunta tana cewa
"Gashi za'ayi magana dake" seta karba tana kallon wayar ganin ba akan kira take ba ta ajiye a gefe ta shiga shiryawa.

Tana qoqarin zuge zip din doguwar rigar data saka wayar ta shiga qara, se sannan ma ta ankare da cewar wayar tace aka bata, ta zumburi baki ganin me kiran wallahi badaban muguwar kewarsa da tayi ba da bazata dauka ba. Ai ko babu komai taci darajar haifar masa ya da tayi ya kirata yaji lafiyarta amma ace har se yau kwana hudu sannan ze kirata taja kwafa tana hararar wayar daidai nan kiran ya katse wani ya sake shigowa.

A daqile tayi masa sallama ya amsa murya ba yabo ba fallasa ta shiga gaishe shi ya amsa tareda tambayarta qarfin jiki, seda taja tsaki qasa qasa kafin tace da sauqi sukayi shiru gaba dayansu na kusan minti daya. Jira takeyi taji ya bata uzuri na rashin kiranta sannan ya rarrasheta ya gaya mata kalamai masu dadi irin yanda ya ringa mata sanda ta haifi Mu'ayyad dan har ta fara tattare fuska tana kwabeta zata fasa masa kuka taji yace
"Abba yayi mata huduba da Aisha ya gaya miki ko?"
"Be gaya mun ba, amma ba kace idan mace na haifa ba sunan Mama za'a saka mata?" Ta mayar masa da amsa tana maimaita Aisha daya fada sunan Hajiya kenan ai ba haka sukayi dashi ba

"Munyi magana Abban yace baza'ayi taron suna ba, Khalifa ze kawo raguna da duk abinda za'a buqata sannan zan saka miki kudi yanzu ina fatan babu wata matsala" ya bata amsa a dake ba tareda ya mayar da hankali kan abinda ta fada ba. Kuka ta fasa masa tanacewa

"Yanzu Khalil kayi mun adalci kenan, ka tsallake kayi tafiyarka ka barni baka damu da halin danake ciki ba, sama da wata biyu baka kirani ba ina raye ko na mutu duk ba matsalarka bace sannan na haihu na kwanta a Asibiti tsayin kwana uku baka kira kaji ya nake ba se yanzu ne kawai zaka ce kira saboda ka gaya mun ka sakawa yata sunan da bashi mukayi dakai zaka saka mata ba wannan ai rashin Adalci ne".

"Zan koma bakin aiki, idan da wata damuwar kina iya kirana tunda kin kunna wayarki" ya sake fada kafin ta bashi amsa ya katse kiran. Sororo tabi wayar da kallo wasu hawaye masu dumi suna bin kuncinta, ta daga kai ta kalli Anty Hafsa da bata san ta shigo ba se ji tayi tana cewa
"Bakiga komai ba Umaimah idan har dai bazaki nutsu ki kuma gyara bakinki ki kuma san abinda kikeyi yanzu kika fara ganin haka" ta juya ta fice abinta bayanta kwantar mata da Babyn data shigo kawo mata.

KHALIL
Tun bayan komawarsa kacokan ya mayar da hankali kan abinda yakeyi ya cirw duk wata damuwa da zata iya distracting nasa. Daman be tsammaci zata kirashi ba shi yasa ma be saka ko a kai ba, randa ta kirashi da wayar Anty yana ganin kiran jikinsa ya bashi itace dan suna magana da Yaya Aminu a bakin sa ma yaji cewar an kwace wayarta dan haka yasa jefi jefi yakan kira Mama su gaisa ya kuma tambayeta lafiyarsu, yanda bata taba cewa zata bashi Umaiman suyi magana ba shima be tambaya ba se ranardata kirashi yana kwance a Hotel room dinda yake, farkawarsa daga bacci kenan wanda cike yake da mafarkin Umaiman suna gudanar da irin soyayyar da yayi tsammanin samu idan ya aureta ya farka kenan yaji qarar wayarsa ya janyota ya duba kamar baze dauka ba kuma wata zuciyar ta saka shiya daga ba tareda yayi magama ba yana jin muryarta kawai ya kashe shi kansa besan dalilinsa nayin hakan ba amma kawai yana so ko yaya ne ya koyawa Umaimah hankali dukda dai yasan Umaimah dai Umaimah ce.

Haka yaci gaba da lallaba rayuwa, a duk sanda tunaninta da kewarta suka bijiro masa har yaji zuciyarsa na neman karaya ta sakashi ya kirata se yayi saurin tuno abinda tayiwa Hadiza da irin tozarcin da ta saka Hadizan a ciki dan har kawo yanzu hotunanta basu dena yawo ba,wasu ma se yanzu suke sake yada shi a matsayin sabon abu, qarin baqin cikinsa na rasa Hadizan da besan yana sonta har haka ba se lokacin da yayi tozali da katin daurin auranta da Musa Kallah nan da sati biyu masu zuwa.

Baqin ciki kamar yayi me, yanzu ta qishi ta zabi wannan tsohon da duk boko ta gama tsotse shi ya tabbatar babu abinda ze iya mata, bazata wani samu wata kukawa a gurinsa ba kamar ace idan shi ta aura haka ya wuni ya kwana ranar da takaici, haushin Umaimah ya sake cikashi, duk ita ta janyo masa tasa Hadizan taqi amincewa da auransa wannan tasa ya qara tsahon zaman da zeyi a SA, ya kamata ace ya dawo Nigeria yanzu amma ya zabi yaci gaba da zama acan zuwa sanda yake ganin zuciyarsa tayi sanyi ze kuma iya sauraran Umaiman.

Sanda ya samu saqon an kaita Asibiti sosai hankalinsa ya tashi, ya tuno naqudar Mu'ayyad wadda tayita akan idonsa ya tuna irin wahalar data sha se yaji zuciyarsa ta fara tsinkewa. Ya tabbatar da tana buqatarsa a kusa da ita ya riqe hannunta yana mata sannu kamar yanda sukayi wancan tare ta yanda bazataji cewar ita kadai bace yana tare da ita a kowanne yanayi. Yana nan yana kaiwa da komowa yana mata addu'ar sauka lafiya be samu nutsuwa ba seda yaji kiran cewar ta sauka ya ringa Hamdala a fili da zuciya, ransa qal dayaga kyakykyawar yarinyar data haifa masa kuma a kallo daya ya hango kamar da takeyi da Hajiyarsa babu bata lokaci ya ayyana sunanta kenan takwarar Hajiya ce.

Tun a ranar yaso magana da ita se daga bayane ma aka sanar dashi Ballewar jinin data samu lokacin har komai ya daidaita babu wata matsala dukda haka hankalinsa be kwanta na seda ya ganta a Video call tana bacci hankali kwance aka kuma hadashi da likitan da ta dubata ta tabbatar masa da babu wata matsala sannan ya samu nutsuwa. Babu dadewa matar wani abokinsa Mannir ta haihu lafiya har suna shirin tafiya gida jini ya balle mata kafin kace me Ajali ya risketa shiyasa ya godewa Allah da basu gaya masan bama har seda komai ya daidaita dan qila da fargaba ce zata kashe shi kafin ita.
Chapter 117 · 0% Book details