← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 267

Sashe 50

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"An sakawa mutane ido se sunje sun fadi"
"Ya akayi kika san ana kallonki, daman baya tana da ido ne?" Ya fada yana mintsinin mazaunanta ta fada qara ta kai masa duka sallamar daya jiyo daga masallaci alamar an idar da sallah ta saka shi miqewa da sauri yana salati.

"Kingani kin saka na rasa jam'i ko"
Baki ta tura ta sake nada rigar a jikinta tana janta qasa dan tadan qara rufe mata jiki ta shige daki tabar Khalil na mata waqar sittin saba'in, idan yana wani shaqiyancin kawai mamaki yake bata dan kafin suyi aure tsaf in aka ce zeyi zata rantse baze iya ba saboda yanda yake shiru babu ruwansa.

A dakinta tayi wanka ta gasa jikinta sosai da ruwan dumi, seda tayi sallar Ishah kafin ta shirya cikin wata Armless top da Three quater dan tun tana sallahr magriba taji fitar Khalil.

Palour ta fito ya tattare komai ya gyara kayansu da pillows din da suka watsar, kan Dining ta wuce saboda yunwar data taso mata kamar zata fadi, ita nata kalar laulayin kenan ci kamar gara se kuma wani lokacin ta rasa me yake mata dadi bayan wannan babu wani abu da yake damunta.

Abincin ta zuba soyayar shinkafa data ji niqaqqen nama ta janyo kwanon da ta zuba Salad ta tsiyaya dressing din akai ta juya kafin ta dibi wanda ze isheta ta rufe sauran dan tasan duk inda yake shima yana hanyar gida, tana kai lomar farko taji an bude Get, seta miqe ta dauki Qaramin mayafin data ajiye akan kujera ta yane kanta ta fita har ya shigo da mota ta qarasa ta kulle Get din tana masa sannu da zuwa.

"Yawwa Malama Umaimah sannunki" ya fada yana mata dariyar data rasa ta mecece,
"Yau kuma Malama na zama" ta mayar masa sanda suka shiga cikin palour, Jakar Laptop dinsa daya dakko ya miqa mata yana cewa

"Yau ai ko makaranta na kiraki kin wuce nan hajjaju, bari nayi sauri naci abinci muje a doramun sabon darasi dan ina buqatar qarin ilimi sosai nima" ya qarasa yana kashe mata ido daya, se sannan ta fuskanci inda ya dosa seta juya kawai ta wuce dakinsa a ranta tana mamakin Khalil, ahidai bashi da damuwa sabgar gabansa kawai yake ji fa ko kunyarta baya ji yake wannan magana toh Allah ya shirya.

Tare suka ci abincinsu cikin nutsuwa suna yan hiraraki, babu abinda yakai zaman lafiya dadi a rayuwa, basu ba hatta da gidan kansa yasan an samu daidaito a cikinsa saboda yanda suka koma sabgoginsu yanda suka saba. Bayan sun gama cin abincin suka buga Tv game seda Abin ya kusa zama rigima dan har ta fara kukan wai wayo yake mata yana mata Game over kafin ya kashe suka kwanta bayan an qara dora karatu sadara biyu.

Kwanakin da suka biyo baya kam se sambarka dan zaman lafiya dai ya samu guri yayi daram a gidan Khalil da Umaimah. Tattalin junansu sukeyi, idan ya fita har ya dawo suna maqale a waya. Wanka da kwalliya kuwa se wanda ta manta dan sosai take tashin kan Khalil da gayu na safe kafin ya fita daban na dare idan ya dawo daban ga karatun makarantar dare da take dora masa babu sassauci gaba daya ta rigada ta shagwaba Khalil din nata ji yake nan duniya kamar babu Namijin da ya kaishi sa'ar Mata itama kuma hakan take a bangarenta dan kuwa Khalil ya isa Namijin kere Sa'a.

Idan yayi kwalliya ze fita aiki ji takeyi kamar ta saka masa Niqab saboda kishinsa da takeyi na nan babu inda yaje a zuciyarta tana dai qoqari matuqa gurin ganin ta kawar da idonta akan duk abinda ze kawo tashin hankali a tsakaninsu.

Tsakaninta da maqotanta kuwa sedai idan sa'a ta gifta ta fita unguwa ko tayi baqi ta rakasu su hadu su gaisa dan ko barkar Rufaida bata samu ta shiga ba kuma tana da yaqinin yanzu tayi Arba'in koma fiye da haka dukda taji a bakin Khalil cewar bata nan, Mijin ze tafi wani aiki Kudu yace ta koma gida kafin ya dawo wai a Masallaci suka hadu yake gaya masa shiyasa ta bari se taji ta dawo zata shiga.

Wata safiyar Talata bayan Khalil ya gama shirinsa ze fita take ce masa tana so taje kitso.
"Wayon kije gida ne kina dai ji wancan zuwan da mukayi Mama tace kar ta sake ganin qafarki a gida se an nemeki shine ko sati ba'ayi ba zakice zaki kitso" Khalil dake daura agogo ya fada yana kallon fuskarta data fara canzawa saboda cikin daya bi jikinta. A lissafi wata na biyar yake yanzu amma sam babu alamar sa sedai qibar datayi ta ko ina har fuskar Allah ya taimaketa dai dogon hancin be kai ga bajewa ba.

"Dadin Iyaye da yawa kenan ai kaga iata Mama korata takeyi idan naje ita kuwa Hajiyata nasan bataqi kullum naje na wuni a gidan ba kai kuma saboda jelousy baka so ka kaini" ta bashi amsa tana masa fari da ido.

"Ke dince ai na rasa me kikewa Hajiya haka kullum bata da zance se naki komai ta samu tace a kawo miki shiyasa idan banyi dagaske ba kwacemun ita zakiyi"

"Toh ai kaima ka kwacemun Mamata ka shiga tsakaninmu,  ina murna Nuratu ta matsa zan kwato fada ta se ga sabon snatcher yanzu magana indai bakai ka fada ba komai na gaya mata bata yarda, kaga shikenan munyi 1-1, na kwace Hajiya ka kwace Mama" ta bashi amsa tana dariya,

"Yawwa na tuna yau irin Cream cheese maccaroni nan ta ranar zakiyi mun" Khalil ya fada, seta dan yamutsa fuska, shidai yana son shegun continental dishes din nan da ba dadi ne dasu ba, be kuma fahimci duk randa yaga ireirensu toh Maman Asad ta kawo mata ziyara ita ce gwanar girki ita takeyi mata amma dai tana ga dole ta ajiye quiya ta koya saboda ranar yar qure tunda gashi an fara da kansa yace tayi masa.

"Idan bazaki iya ba ki barshi naga kina ta bata fuska a sharrinki yanzu se kice ze saka ki Amai" ya fada yana daga hannu sama fuskarsa da murmushi dan sabon salon iyashegen data samo kenan, Allah ya yaye mata be dora mata ciki me laulayi ba amma se kalato shi takeyi. Idan batayi niyya ba shara se tace idan tayi Amai zata sakat sedai shi ya share balle girki yanzu kullum suna kan hanyar zuwa gidan Hajiya cin abincin dare dan tunda akaje Restaurant ranar nan wata classy babe ta biyo Khalil akan ya bata number sa aka kusa kwasar yan kallo Allah dai ya taqaita shikenan ya yaye wa kansa fita da ita. Yaje shikadai din ma tace bata yarda ba dan bata san me zeje yayi ba yanzu suda abincin waje sedai suyo order a musu delivery toh ya za'ayi zaman lafiya ai yafi zama dan sarki tubda outing din ba dole bane.

"Anjima zan fito na duba, akwai yaran da sukeyin ball a qofar gidan nan su Aliyu zan tambaye su koda gidan kitso kusa se naje kan ya dameni da yawa" ta sake fada sanda ta rakoshi bakin mota

"Yanda kasan wata me gashi bayan qwaiqwaido ce zaki damu mutane da wani kitso ki bari idan na dawo sena yi miki da kaina" Khalil ya tsokaneta, seta zumbura baki ya zuro kansa ta glass yayi pecking bakin nata kafin yaja mota tana daga masa hannu ya fice daga gidan. Tana qoqarin maida Get din ta hango Aliyu daya daga cikin yaran dake wasa a qofar gidan ita bata ma san dan wane gida bane tana dai aikensu wani lokacin ko idan tayi ragowar abinci ko abinda ta kasaci na kayan dadi ta fita ta raba musu.

Kiransa tayi ya tawo da saurinsa yana murna dan yasan bata kiran banza ko aikene idan ka dawo seta baka na alawa.
"Anty ina kwana" ya fada yana dan rusunawa, seta amsa masa tace

"Lafiya lau Aliyu, baka je makaranta ba ne yau na ganka da safe?"
"Ai babu makaranta yau public holiday akeyi" ya bata amsa seta daga kai tace

"Oh, yawwa ni a unguwar nan a ina ake kitso ne Ali?"
"Anayi a gidan mu Mamanmuce takeyi" ya bata amsa yana nuno mata qofar gidansu da yake kallon nata ta dayan bangaren.

"Yawwa jeka ka tambayomin naji yaushe zanje ayimun kaji" ta fada se ya juya da saurinsa ita kuma ta koma cikin gida, kayan wanke wanke ta fito dasu tsakar gidan bakin famfo ta shiga wanke wa, bata dade da farawa ba ta jiyo bugun qofa da surutunsu seta dauraye hannunta taje ta bude shida Hibban ne yaron Gidan dake jikin nata shi ta gane fuskarsa dan kamar sa daya da Mamansa da suka shigo mata tareda Rufaida.

"Wai tace ko yanzu ma kizo idan bakya komai" Aliyun ya fada mata saqon Mamansa.

"Toh shikenan, bari na qarasa wanke wanke sena zo"
"Kawo nayi miki Anty" Hibban din ya fada yana murmushi dan irin masu yawan Fara"ar nan ne, Murmushin ta mayar masa tace

"Aa nagode, gadai tsintsiya nan ku share mun tsakar gidan kafin na gama" suka Amsa da toh taci gaba da wanke wanken suna mata sharar suna yar hira har suka gama.

Ciki ta shiga ta kira Khalil a waya ta shaida masa zata shiga gidan su Aliyun ayi mata kitson yace ta duba rigar daya cire jiya da akwai kudi ta dauki dubu biyu tayi masa godiya kafin ta gyara fuskarta ta zura dogon Hijabinta ta hada kayan kitson a qaramar jaka ta fita. Seda ta daukar musu Apple daddaya da chocolate ta basu sunata godiya kafin suka rakata gidansu Aliyu.

Da sallama ta shiga wata mata baga mara jiki na zaune a tsakar gidan tana hura gawayi a Dutsen gugar charcoal ta amsa mata fuskarta da fara'a tana mata sannu da zuwa. A mutunce suka gaisa Umaimah na satar kallon gidan da a kallo daya zaka fahimci cewa mazauna cikinsa na fuskantar matsin rayuwa dan dukda cewa ginin zamani ne amma ya tsufa alamar rashin gyara a haka ma da alama dan mutanen gidan nada tsafta saboda a sannan ma tsakar gidan dukda qasace amma qal yake babu ko tsinken datti an share ko ina.
Chapter 50 · 0% Book details