← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 267

Sashe 51

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kitso nazo, Aliyu ya gaya miki ko" Umaimah ta sakw fada ganin matar tayi shiru bayan da suka gama gaisawa, se matar ta nuna mata dakin dake fuskantar su tace
"Tana ciki Maman Aliyun ki qarasa" daidai nan matar dakin tayi fit ta fito tana gyara daurin zaninta dake neman faduwa.

Wata harara ta makawa Abokiyar zaman nata se kuma ta saki murmushi ganin idon Umaimah akanta ta fara cewa

"Au Amarya ashe kece bismillah qaraso ai dangidan naki yace zakizo da fita zanyi ma na fasa"

Murmushin yaqe Umaiman ta sakar mata itama dan sam matar bata mata ba, ta tuna fuskarta itace Maman Hauwa wadda suka shiga tareda budurwar yarta da tana Amarya.
Cikin palour suka shiga Maman Hauwa nata faman jera mata sannu da zuwa Umaimah ta tsaya tana kallon kujerun palour tunanin inda zata zauna takeyi dan sunci uwarsu da datti ga wani zarni zarni na tashi kamar anyi fitsari a palour a haka har turaren tsinke taga an kunna.

"Zauna mana Amarya, kin tsaya" Maman Hauwa ta sake fada baki a washe, Umaimah ta dosana mazaunanta akan kujerar data ga nada dan dama dama a ranta tunanin yanda zasuyi kitso a wannan dakin takeyi dan tuni cikinta ma ya fara hautsina mata.

"Ina kwana?" Maman Hauwa ta fada, seta dawo daga kalle kallen da take ta amsa mata suka gaisa.
"Ai muna ta ganin abin arziqi komai Aliyu ya shigo dashi yace Anty ce ta bashi ko mijin Anty, nace ita Antyn taka ce bame son mutane ba aida mun shiga munyi godiya" Maman Hauwan ta sake sako magana, se Umaimah ta saki murmushi bata ce komai ba Maman Hauwa taci gaba da cewa

"Eh mana, tunda muka shigo muna ta zuba ido ko zaki shishshigar mana shiru. Lokacin haihuwar Rufaida ma matan layi duk an hadu ana ta tambayar ina Amarya a sannan yara sukace kamar bakya nan kai har ma aka gaji da tambaya kowa yace baki shigar masa ba dake mun saba nan idan aka kawo sabon zuwa zakiga duk za'a ringa haduwa ana gaggaisawa"

"Allah sarki" kadai Umaimah tace seta dakko wayarta ta shiga dannanwa dolen Maman Hauwa tayi shiru. Kusan minti uku a tsakani tana qarewa Umaimah data hade fuska tana danna waya kallo se tace

"Bismillah toh kinzo da kibiya ko na dakko?"
"Aa nazo da ita" Umaimah ta fada ta bude jakar ta dakko Comb, kibiya da Mai. Tana shirin zame Hijabinta aka dauke wuta, Maman Hauwa tace
"Oh sunyi halin nasu sedai mu koma tsakar gida dan yanzu zakiji dakin ya gume da zafi ga shi daman yara sunyi fitsari a gun"

Hamdala Umaimah tayi a zuciyarta ta tattara kayan tayi waje, ita badaban bama gudu zatayi amma yata iya tubda tazo zata daure amma dan ba qara.

A tsakar gidan suka zauna kitson sunayi dayar matar nata gugar kaya ta gama ta shiga hidimar girki Maman Hauwa nayiwa Umaimah hira ita dai sedai ta amsa da Eh ko Aa dan sam ba dadin hirar takeji ba gashi ta debar mata kitson qanana dan ma tana da sauri nan da nan zuwa sha biyu se gashi sun gama zuwa sannan gidan ya fara cika da Mata wasu yan kitso wasu kuma kawai hirarsu ce ta shigar dasu harda masu kai zubin Adashi dan taga duk wadda ta shiga zata bawa Maman Hauwa dubu daya ko dari biyar ita kuma tasa yara su rubuta a littafi duk wadda ta shigo kuna se an mata bayanin Amaryar can gidan ce.

Dubu daya ta bata kudin kitson dan yayi kyau sosai ta kuwa ringa godiya kamar zata durqusa mata. Tana shirin fita daya matar ta fito daga kitchen tana murmushi tace

"Har kun gama kenan sannunku" Umaimah ta amsa mata da murmushi itama dan jininta yafi haduwa da ita sama dana me kitson, bata damu da hararar da Maman Hauwa da sauran dake zaune ba ta sake cewa Umaiman

"Ga Abinci ya kusa sauka bazaki tsaya kici ba Alalen gwangwani ne abin marmari"

"Toh uwar kinibibi gurinki tazo ko yaya da zaki tsareta da surutun banza ko tace miki mayunwaciyace ita duj inda taje se taci Abinci" Maman Hauwa ta hayayyaqowa matar sauran matan dake zaune suka hau qunqunin wai ta fiya cusa kai daga ganin mace zata fara mata shishshigi, baze wuce wanki da guga zata ce ta ringa kawo mata ba kuma ba samu zatayi ba dan duk dan dakin Maman Hauwa bazeyi hulda da Ramatu ba.

"Idan kin gama a bawa Aliyu ya kawo mun toh" Umaimah ta fada kafin tayi musu sallama tayi ficewarta a ranta tana mamakin wadannan mata da suka taru, a haka dai gasu kamar wayayyu ashe duk taron marasa sanin ciwon kai ne. To in banda rashin sanin ciwon kai qarfe sha biyun rana ki kullo gidan ki lokacin da kowacce Mace take qoqarin dora abincin rana ki tafi yawon daukar magana wani gidan toh Allah ya kyauta.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 24

Umaimah na zuwa qofar gida wayarta dake cikin jaka ta hau qara, seda ta zarota sannan ta bude qofar ta shiga, Khalil ne ya ke kira ta daga da sallama tana narke masa muryar shagwaba.

"Me kuma ya faru?" Ya tambayeta cikin rarrashi, seta narke fuska kamar tana gabansa tace
"Na gaji da zama kitson me yawa tayi mun duk yanzu bayana ciwo yakeyi".

"Ayya sorry Babe idan na dawo zan miki Massaging bayan kinji, na kiraki da zu Hajiya ma tace ta kira baki amsa ba"

"Lah wayar tana jaka se yanzu na dawo banma duba taba kiranka ya sake shigowa bari toh na kira Hajiyan sena sake kiranka" ta fada tana shirin kashe kiran ya dakatar da ita da cewa

"Base kin kirata ba daman su Habiba ne zasu zo da yaran Kawu Najib shine zata sanar miki"

"Ohk to shikenan se sunzo"  ta bashi Amsa daga nan suka yi sallama ta kashe wayar. Azahar tayi dan haka ta daura Alwala tayi sallah a ranta tana tunanin me zata dafawa baqin nata dukda bata san manya ne ko yara ba dab Kawu Najib din kansa sunansa kadai ta sani, tunanin ta dora musu dafa dukan shinkafa da pepper chicken tayi, seta miqe ta shiga kitchen ta dakko kaza a Freezer ta gyarata tsaf ta hada kayan qamshi dasu maggi tayi marinating nata ta mayar cikin fridge dan ta tsumu dan ba tafasata zatayi ba.
Bazata dora abincin ba se sunzo dan kwanaki kusan sau biyu ta shiryi yin baqi se ta gama girki tsaf suqi zuwa sedai ta bayar kota aika dashi gidansu kona Hajiya shiyasa ta yanke shawarar dena yin girki idan zatayi baqi se sunzo, sedai ta tanadar musu qananan abubuwa da zasu dan taba kafin ta gama.

Daki ta koma ta miqe akan doguwar kujera kafin kace me bacci yayi awan gaba da ita can cikin baccin qarar wayarta data ajiye saman kanta ta fara qara, a firgice ta farka tana zare ido, ta daga wayar daga dayan bangaren Khalil yace

"Babe ina kika shiga ko wanka kikeyi? Gasu can a waje sunata bugu baki jiba". Cikin muryarta da tayi qasa saboda baccin da yazo mata me nauyi tace

"Waifa dan kwanciya nayi na huta shine bacci ya kwasheni"
"Ai ke dai yanzu kin zama kasa is a sace ki ma kina bacci baki sani ba" Khalil ya tsokaneta seta mayar masa sa cewa
"Naji din, idan zaka dawo ka taho mun da rake"
"An gama, jeki bude musu kinga ana rana suna tsaye a ciki" sukayi sallama ta miqe.

Seda ta wanke fuskarta ta gyara daurin dankwalinta dan bata san su waye ba karsu rainata kafin ta yafa mayafinta ta fita, tana budewa Habiba qanwar Khalil na tsaye da dutse a hannunta se wasu guda biyu da bata san fuskarsu ba Habiban ta saki murmushu tace

"Yawwa Anty Umaimahtundazu muke bugu seda muka kira Yaya yace qila bakya nan ba bari ya kiraki" Habiban ta fada da murmushi se Umaimah ta mayar mata da martanin murmushin ta qarasa ta bude musu qofar tana cewa

"Kitso na shiga can gidan ai ba nisa nayi bama dana dawo kuma bacci ya daukeni shiyasa banji bugun naku ba bismillah ku shigo" tayi ciki suka rufa mata baya. A mutunce suka gaisa tana binsu sauran biyun da kallo qasa qasa musamman farar ciki da se wani yatsina take tana qarewa Palour kallo seta tashi ta kawo musu ruwa da lemo, tana da sauran Samosa danya a Freezer ta soya ta hado musu da ita ta zauna tana cewa

Solar taje ta kunno saboda an dauke wuta ta kunna Musu Tv ta miqawa Habiba remote tana cewa
"Bari na dora abinci Habiba ku fara da wannan, sedai baki gaya mun su waye baqin nawa ba"
Chapter 51 · 0% Book details