← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 267

Sashe 61

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu nisa daga Asibitin nan da nan suka isa, Umaimah ta saki baki kawai tana kallon Aljannar duniya dan gidan na Maman Nihal ya zarce duk yanda take Hasashensa. Seda suka wuce kantama kantaman palour guda biyu kafin suka isa qaramin palour Maman Nihal da haduwarsa bazata fadu ba, tana zaune akan akan kujera ta taso da fara'a ta tari Umaimah ta zaunar da ita tana tayi mata faman sannu da zuwa.

Cikin dan lokaci aka cika mata table din gabanta da kayan maqulashe iri iri tadan taba kadan Maman Nihal dai ta rasa ina zata saka Umaimah saboda murna tana ta janta da hira sauran yaranta sukazo suka gaisheta yar tsakiyar data zo ta kalli kwalbar Red wine da aka kawowa Umaimah ta tabe baki tace
"Kai harda wannan, na Dady ne fa ko Mommy bata tabawa shine kika bata" cikin tsiwa tayi maganar tana kallon Maman nata abin ya bawa Umaimah mamaki, hannu Zainab takai zata janyo ta ta kwasa da gudu tana cewa

"Se naje na gayawa Momy" Zainab din ta shiga kiranta amma bata waigo ba seta kalli Umaimah tana murmushi tace "kinga Sumy tafi duk yan uwanta rigima yarinyar nan"
"Ayya daman hakane a cikin yara se ka samu wanda yafi wani qiriniya.

Hira suka ci gaba Umaimah na ankare da agogo jira take biyar tayi ta ware kafin Khalil yasan tayi wani wajen.
Qarar takun takalmi sukaji daya sa gaba daya suka juya, wata hadaddiyar Macece ta fito fara kyakykyawar gaske da kana ganinta kasan hutu ya ratsa fatarta fuskarta babu yabo babu fallasa tayi musu kallo daya tace

"Baquwar taki ce sannu, zan dan fita zaki jirani ne ko zaki wuce".
Yanayin maganar tata kamar da Umaimah take amma kuma Zainab take kallo,
"Ina nan se kin dawo" Zainab din ta bata amsa se ta dan tabe baki ta saka kai ta fice Zainab din na mata a dawo lafiya.

Kan Umaimah ya daure ita kuma wannan wacece da zata zo cikin gidan mutum tana cika tana batsewa kamar nata, kamar kuwa Zainab tasan tunanin da Umaiman takeyi tana yar dariya tace
"Anty Maryam kenan Yayata da nake gaya miki tana aure a America, jiya tazo ta sauka a nan ni kaina bason saukar tata nakeyi ba dan gaba daya ta kura mutum takeyi"

"Allah sarki" Umaimah tace kafin ta gyara zaman mayafin kanta ta miqe,
"Aa badai tafiya ba? Zainab din ta fada itama tana miqewa se Umaimah tace
"Tafiya zanyi yamma tayi ai"
"Haba dai ki bari idan kikayi magriba kika ci Dinner se Walid ya mayar dake gida amma muna hirar mu zaki wani ce tafiya"

"Kai so kike yau Honey ya kulle mun qofa kenan, daman ai biyowa kawai nayi na wanke laifina a denayi mun gori" Umaimah ta fada tana dariya, dariyar Zainab din itama tayi tace

"Aiko da sauran laifi kin dai goge kadan se ranar da kika zo kika wunar mun sannan ze goge gaba daya amma banji dadi da zaki tafi baku gaisa da Baban Nihal ba yana gari, kinsan har na gaya masa Mijinki Architecture ne akwai filinsa a Nasarawa GRA da nake ta nacin ya gina mana mu koma toh naga alamar ze yarda idan an tashi shi za'a bawa contract din"

"Toh Allah ya tabbatar babu damuwa wata rana idan na sakw zuwa se mu gaisa". Sama ta haye ta dawo da wata leda qarama ta bawa Umaiman sannan ta shiga kitchen ta saka akayi mata packaging ragowar snacks da Dambun naman da akayi mata ta saka Wanda ya dakko ta ya mayar da ita se Umaimah tace Aa driver yana Asibiti yana jiranta irin itaka ta kankarowa kanta mutunchi dan haka suka je ya maida ita Asibitin ta kira me Adaidaitanta da daman beyi nisa ba yazo suka tafi a ranta tana ta yaba kirkin Maman Nihal. Ledar data bata ta bude, turaren wuta ne Al-Haramain  tun bata kunna shi ba tasan zeyi qamshi dan budeshi kawai tayi taji qamshi.

Allah sa a wanye lafiya Hajiya Umaimah da sabuwar qawarta

*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 28

Umaimah na isa gida ta adana Snacks din nan da dambun nama ta canza kaya ta shiga kitchen dan samarwa da Khalil abinda zeci tasan yana hanya. Soyayyar Taliya tayi an hado mata da peppered turkey seta saka shi a Microwave kafin ya dawo ta dumama dan karya kuma yin sanyi tana aikin tana santin gidan Maman Nihal gida kamar baza'a mutu ba amma kuma se taga a fili tayi mata daban, wannan fresh din da kalar hutun nata na hoto ba sosai ba gara yaran su suna nan yanda take ganinsu harma sunfi kyau a filin.

Tana tsaye tana gyara kan Dining bayan tayi sallar Magriba Matar da Maman Nihal takira da yayarta ta fado mata a rai se ta tabe baki a fili tace
"Wannan irinsu ne masu shegiyar dagawa da raina mutan dadin ta ma bata ganni a qulaqance ba ahto nima da rufin Asirina qila ma a American a qasan Gada suke (kuji fa sharrin Umai ).

"Ke kuma dawa kike faman sambatu" taji an fada daga bayanta ta zabura dan sosai taji tsoro Khalil yayi saurin tareta yana cewa
"Kee yi a hankali mana"
"Ba kaine ka tsorata ni ba, kuma banji qarar mota ko bude Get ba se jin muryar mutum kawai nayi" ta fada kamar zatayi kuka, seya kama hannunta ya sakko da ita daga steps din Dining yana cewa
"Ai bazakijini ba kina faman magana ke kadai inata sallama hankalinki yayi gaba, kedawa kike fada?"

"Hmm wata matace fa dazu a Asibiti ta ringayi wa mutane wani kallon raini se kace tafi kowa ita na tuna ta bani haushi nake mita" ta shato qarya ta fada masa, dakinsa ya wuce yana cewa
"Kedai Allah ya shirya ki Umaimah rigimarki tayi yawa" tabi bayansa tana qara nana ta masa irin kallon rainin da matar tayi mata dan dagaske abin yaci mata zuciya dan bata son wukaqanci a rayuwarta.

Qarar wayarta ce ta dakatar da ita daga taya Khalil cire kayan jikinsa, yace
"Yawwa gashi can ana kiranki a waya" dan ta dame shi da shegiyar mita shi kuma ya gaji kansa ma ciwo yake dan wunin Site sukayi. Fita tayi tana cewa
"Ni ka kora ko, zaka sake cewa na tayaka wani abune nima sena rama" ta fice kafin ta qarasa wayar ta katse ta dauka Maman Nihal ce tana shirin kiranwa wayar ta sake daukan qara seta daga tareda Zama akan kujera suka gaisa tana tambayarta ya taje gida tace lafiya lau, godiya tayi mata akan zuwan da tayi Umaimah nata bagararwa dan gudun kar Khalil na jiyota yazo ya tusata da tambaya se Maman Nihal din tace

"Kinga ban kiraki da wuri ba, order kayan gadon Hamida ne ya iso har an kawo kayan ma nan Kano shi muka tafi dubawa daman dazu can Anty Hadiya zataje ta fara yin gaba se na bita daga baya, duk ma raina ya baci wallahi dan akwai kayayyakina da nayi order babu su a ciki kuma na amfanin bikin ne yanzu ban ma san yaya zanyi ba"

"Se haquri shiyasa ni daman ban yarda da harkar order nan ba nafi gane naje shago na dauki kaya na biya kudi" Umaimah ta bata amsa, qorafi Zainab taci gaba dayi mata akan kayan nata da ba'a sako mata ba Umaimah dai ca take se haquri to me zata ce mata fitowar Khalil daga daki ta sakata yi mata sallama ta ajiye wayar suka qarasa kan Dining ta shiga zuba masa abincin,

"Ina aka samo Turkey?" Ya fada lokacin daya kai naman bakinsa, taste din da qamshin spices din basuyi kama da na gidansa ba dan bakinsa da hancinsa akwai iya tantance qanshi da dandano.
"Anty Hafsa ce ta aiko mun dasu dazu harda Dambun nama da Samosa da spring rolls da wani ko meat bag sunansa oho tasan kana sonsu shine ta bawa Salman dazu da yaje gidan ya kawo mun" Umaimah ta sake yanko wata qaryar a karo na biyu dan bata da wata Mafita seta jingina abin da Anty Hafsa, tasan dai ko haduwa sukayi baze tambayeta ba dan akwai yar kunya tsakaninsu.

Gyada kai yayi yaci gaba da cin abincinsa suka gama suka koma cikin palour harta zauna yace ta dakko masa snacks din, sosai dadinsu ya ratsa shi ya kalleta yace
"Amma yayi dadi ita takeyi?"
"Anya kuwa inaga siyowa tayi sedai na tambayeta naji" ta bashi amsa tana janyo wayarta ta dannawa Maman Nihal kira tana dagawa tace

"Honey ne yaci snacks din nan yake santi shine nace bari na tambayeki a gida akayi ko siyowa kukayi"
Chapter 61 · 0% Book details