← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 267

Sashe 82

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ke baki san idan miji ya qauracewa matarsa shine qololuwar horon da zeyi mata ba ko Aa se shirme da hauka kika saka a gaba a wautar ki idan jarabarsa ta tashi dole ze kawo kansa to kici gaba tsinuwar Mala'iku kadai ta isheki ai.
Yadai kamatu zuwa yanzu ace kinyi hankali kuma kema kin isa ki gayawa wani yanda yavkamata yayi ba ace kullum ke ake yiwa fada ba. Zaman auran nan fa ibadah ne Umaimah yana kuma da dokoki da sharudda ba kara zube ake yinsa ba, idan baki nutsu kinbi Allah ba wuta zaki kai kanki a banza babu ruwan Khalil dan yana shiru baya ce miki komai akan abinda kikeyi Shi Allah babu ruwansa zeyi miki hukunci daidai da abubuwan da kika aikata"

Haka suka ringa yi mata fada da Nasiha tare da bata shawarwari tayi laqwas kamar ta dauka harda yar kwallarta ta kuma Alqawarin zata gyara idan Khalil ya dawo zata bashi haquri in sha Allahu ba za bashi haquri basu bar gidan ba seda sukayi sallar Azahar ta dafa musu Indomie sukaci sannan sukayi Haramar tafiya zasu biya gidan Anty Hafsa. Bayan tafiyarsu ta tashi yin tuwon shinkafa da Miyar Yakuwa saboda Khalil yana sonsa. Hauwa ta kira ta daukar mata Mu'ayyad dukda jan kunnen da suka gama shi mata akan hakan amma bataji ba.

Ta tuqa tuwanta ta malmale ta hada miyar gaba daya gidan ya dauki qamshin girki dan Umaimah gwana ce gurin iya sarrafa abinci musamman na gargajiya qyuyace take hanatayi. Seda ta sake gyara gidan ta turare ko ina kafin qarfe shida ta gama komai har Mu'ayyad an dawo mata dashi ta masa wanka ta shirya shi tsaf suka zauna jiran Khalil

Tunda ya shaqi qamshin turare daya cakude dana girkin da yayi ya saki murmushi, har ga Allah yayi missing komai nata, dole ta saka yake nesanta kansa da ita dan yana so ta fahimci girman laifinta tayi nadama amma abin ya gagara.
Da sallama ya shiga, fuska babu yabo babu fallasa daidai nan ta shafa Addu'ar da takeyi ta miqe tana cire Hijabin da tayi sallah tayi masa sannu da zuwa. A sama ya amsa yana nufar dakinsa yana kallon yanda take kallonsa se yaga kamar jikinta a sanyaye yake ba kamar yanda ya saba ganinta ba, tabe baki yayi ya shige daki yasan wani wasan kwaikwayon ta shirya kuma.

Wanka ya farayi, yana bandakin wayarsa daya ajiye akan gado ta dauki qara, a jikinsa yaji cewar Hadiza ce dan ta kirashi yana tuqi yace idan ya tsaya ze kirata yasan taji shiru ne ta sake kiransa dan ita kuma haka take da nacin tsiya bata da Jan Aji irin na Umaimansa. Tunawa da yayi Umaimah zata iya shigowa dakin a ko wanne lokaci ya sakashi watsa ruwa babu shiri ya fito, wayar ta katse dan haka ya sakata a Silent, hakan be masa ba ya jefata a Aljihun rigar daya cire kafin ya koma yaci gaba da wankansa.

Tana zaune a kan kujera ya fito tana ganinsa ta miqe tana ce masa
"Ga abinci nan tuwo nayi naga kwana biyu baka cin abinci sosai"
"Sannunki" ya bata amsa yana nufar Dining din ta bishi a baya, ita ta zuba masa ta tura masa komai gabansa kafin ta nemi kujera ta zauna kamar me gadinsa yau ko danne dannen wayar da takeyi babu shidai cin abincinsa yakeyi lokaci lokaci yana kallonta tareda karantar yanayinta harya qarasa ya dauki bowl din data zuba fruit salad ya koma cikin palour ya chanza channel zuwa tashar labarai.

Sake binsa tayi ta zauna a kujerar kusada wadda yake kai ya zuba masa ido ba tare datace komai ba. Yanda kasan an daure mata harshe, so take ta bashi haqurin amma shedanna nan yana zugata akan kartayi zata bada kanta daga qarshe dai ta yakice shi ganin ya mayar da Hankali kan Tv tamkar ma besan da zamanta ba ta bude baki dakyar tace
"Khalil kayi haquri ka yafe mun laifin da nayi maka wallahi sharrin shaidan ne".

Shiru yayi kamar beji taba, ta sake maimaitawa kafin ya dago fuskarsa da dan murmushi yace
"Wane laifi kikayi mun kuma?"
"Qin binka da nayi Lagos, kayi haquri wallahi...."
"Wannan ai ba laifi kikayi ba, ra'ayinki ne bakya son zuwa ni ya kamata na baki haquri da nake neman tilasta miki ki ringa bina wani waje alhalin bakya son zuwa, kiyi haquri kinji in sha Allahu bazan sake cewa kiyi mun rakiya wani guri ba duk inda zanje zan tafi ni kadai" Khalil ya tareta, yanda yayi maganar babu damuwa sam a fuskarsa amma tasan magana ce kawai ya gaya mata ta yaya ma zece beji haushi ba seta sake marairaicewa tace

"Toh idan bakayi fushi ba me yasa tunda ka dawo kaqi kulani?"
"Ni kuma naqi kulaki yanzu ma ba gashi magana mukeyi dake ba?" Ya fada yana kallonta seta tura baki wato so yake ma ya raina mata wayo be gane me take magana akai ba kenan dan haka tace

"Ba irin wannan ba, nasan baka iya daukan lokaci ba taredani ba amma ka iya zama kusan wata biyu a can kai kadan sannan yanzu ma daka dawo kai kadai kake kwana ko nazo korata kakeyi".
Dariya yayi a ransa yana jinjinawa Umaimah da wautarta wato Maye ta dauke shi ko,ta aza ze jure duk wukaqancinta saboda jikinta to shima ya koyi yanda ze hadiye zalamar tasa seta qarata can da abinta kafin ya samo wata. Kallonta yayi yace

"Toh yazanyi? Daman saboda ina ganinki ne na saka rai da zan samu shiyasa nake damuwa amma tunda babu kinga dole nayi haquri kuma koda na dawo daman ai akansa ne kike mun wukaqanci shine na barki ki huta ko, ban nema bama ballantana raina ya baci idan kin hanani".

Shiru sukayi gaba daya, shi ya maida hankalinsa kan TV ita kuma tana ta jan yatsun hannunta tana auna abinda zata gaya masa, ganin tayi shiru taqi magana ya sakashi miqewa yana cewa
"Karfa ki sakawa ranki damuwar ko ina fushi dake ne Aa, kawai ina baki space ne kamar yanda kika zaba"

"Dan Allah kayi haquri" ta fada kamar zatayi kuka har idonta sun kawo kwalla, qoqarin wuceta ya shigayi yana cewa
"Bakiyi mun komai ba" seta riqr qafarsa ta sakar masa kukan shagwaba hade da kissa tana cewa
"Kayi haquri ka yafe mun wallahi na horu bazan sake yi maka gardama ba ko China kace na bika zanje amma dan Allah ka yafe mun bazan iya ci gaba da jure rashin ka ba"

"Ikon Allah" ya fada a zuciyarsa a fili kuma ya saka hannu biyu ya dagota ganin tana neman kayar dashi tana miqewa kuwa ta fada jikinsa gaba daya ta kanainayeshi tana sake sakar masa wani kukan tana nanata yayi haquri"

"Ya isa Umaimah kinga karki tashi Mu'ayyad na haqura shikenan?" Ya fada yana qoqarin janyeta daga jikinsa, noqe wuya tayi tace
"Ba shikenan ba, baka haqura ba"
"To me kike so nayi da zaki yarda na haqura" ya sake fada yana jan numfashi saboda kusancinsu yayi yawa tana qoqarin tayar masa da abinda yake dannewa. Kanta ta kwantar a wuyansa tana cewa

"Nima ban sani ba amma baka haqura ba na sani"
"Toh sakeni se naji me kike so nayi" ya fada yana dago kanta daga wuyansa saboda yanda dumin numfashinta yake shigarsa, kamar wata kaska haka ta maqale masa yayi yayi ta sake shi amma taqi qoqari takeyi ta hade bakinsu yaqi bata dama dan yasan inhar ta samu dama zancen fushi kuma dole ya qare dan baze iya tsalkakewa tarkonta ba shi kuma be yarda da nadamarta ba yanzu, ko ze sakko se ta sake horuwa tukunna wannan tuban nata beyi kama dana gaskiya ba.

Wayarta da aka kira ce ta cece shi, babu bata lokaci ya shige dakinsa ya barta tsaye tana hawayen baqin ciki a ransa yace
"Kema kiji irin yanda nakeji idan da dadi" dan ya karanci a buqace take sosai.
Da safe yayi zaton tayi fushi se yaga akasin haka dan kafin ya fito harta hada musu breakfast, jikinta a sanyaye sosai fuskarta ta kode kamar wadda take jinya se yaji tausayinta ya tsirga masa amma daya tuna tasa jinyar daya sha se ya danne tausayin nata yaci abincin ya kama hanyar office.

Seda suka sake cin sati a wannan yanayin zuwa sannan ya tabbatar da ko badan Allah ba Umaimah ta biyu, ranar daya shammaceta ya amsa gayyatar ta har kuka seda tayi masa se ya rasa tsakanin shida ita wayafi kewar dan uwansa daga nan komai ya daidaita sukaci gaba da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali da jin dadi ko sanda ya fahimci Hauwa keyi mata ayyukan gida bece komai ba tunda daman ya dade yana mata maganar ta nemi me aiki dan baya son qazanta tunda bazata ringayi na ta nemo wadda zata tayata, kawai yaja mata kunne akan karta kuskura ta bata gyaran dakinsa haka girki tayi da kanta se rainon Mu'ayyad da take tafiya dashi ya hana, yace duk abinda zata tayata dashi tayi a nan a gabanta karta qara bayar masa da Yaro a tafi dashi wani gida tadai kiyaye wasu daga sharuddan amma wasu kam ta take kamar maganar Raino kam daya fita idan Hauwan tazo tayi mata aikin da zatayi zata bata shi su tafi, se yamma lis kafin lokacin dawowarsa zata kawo mata shi girkin ma wata rana bata takeyi sedai ta tsaya tana dubawa ko gurin saka maggi da sauran kayan hadi ta saka da kanta ta barta ta qarasa toh ina zata iya ita tunda tasan dadin me aiki ai kuma shikenan.

A bangaren Khalil da Hadiza kuwa tun daidaiton sa da Umaimah ta kasa gane kansa, gaba daya yanzu shareta yakeyi dan harga Allah yana mantawa da ita wani lokacin tunda me guri ta dawo dole yar haya ta kama gabanta. Lokutan da yake samu ya kira daman irin lokacin da suke waya da Umaimah ne idan yana office dan haka yanzu ma sun dinke abinsu sau da yawa idan Hadizan ta kira sedai taji call waiting in taci sa'a ya daga yace mata yana aiki ze kira shi kenan sedai idan ita ta sake kiransa kuma.
Chapter 82 · 0% Book details