← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 267

Sashe 111

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin kuka tace masa
"Sunanta Hadiza kuma budurwar Mijina ce"
"Budurwar Mijinki?" Ya maimaita ta daga masa kai ba tareda tayi magana ba se ya sake bude wani envelope dinya zaro hotunan da take yadawa ya ajiye mata yana cewa
"Me kika sani akan wadannan hotunan?"

Kallonsu tayi ta kalleshi kafin ta juyar da kai gefe tace
"Wata ce ta turamun dasu, tace ita Aminiyar Hadiza ce sannan itace ta gaya mun abinda yake tsakaninta da Mijina da duk irin Badalar da suke aikatawa a bayan idona ta turamun da shaidar hotuna da videos ta kuma hado mun da wannan tace mun daman Hadizan yar Leabian ce, kuma Mijina ya sani yace a hakan ze aureta, shine ni kuma na turawa da yan uwansa dan su gani su san irin matar da yake so ya auro kuma na watsa a media saboda na tona mata Asiri kowa yasan abinda take aikatawa".

Kallonta ya ringayi yana nadar abinda take fada har ta kai aya, a ransa ya jinjina mata wannan ita Gaba gadin ai babu Tsoro ko shakkar komai a ranta kuma da alama iyakar gaskiyar abinda ya faru ta fada. Jin tayi shiru ya sakashi ya sake tamke fuska ya kalleta yace
"Kecw kika yada hotunanta a Media kenan kikayi mata qazafi saboda kawai Mijinki yana nemanta koh?"

"Ni ba qazafi nayi mata ba, na ma santa ne ballantana nayi mata qazafi? Na gaya maka Aminiyarta ce ina zaman zamana ta kirani a waya ni badan ta gaya mun ba babu ta yanda za'ayi nasan tana tare da Mijina kuma ita ta gaya mun Halinta ni kuma na tonata a duniya saboda wanda basu sani ba su sani ni meye nawa a ciki?" Umaimah tayi saurin katse shi seya miqe tsaye yana zaro mata ido yace

"Bazaji gyara bakinki ba ko? Naga alamar se jikinki ya gaya miki sannan zaki fahimci a inda kike, wato ke ga Fitsararriya kin aikata laifi sannan har kinada bakin kare kanki. To ki adana duk wasu surutanki zasuyi miki amfani a gaban Alqali, idan kinje can se kiyi muau bayanin dalilin daya saka kika Lalata Rayuwar Baiwar Allah ta hanyar yi mata mugun qazafi" ya shiga tattara takaddun daya barbaza a gurin. Kotun da taji ya ambata ta saka ta qarasa shigewa cikin nutsuwarta murya na rawar Kuka tace
"Yanzu kuma me nayi dan girman Allah, kai fa kace na fadi gaskiyar abinda na sani kuma na fada. Wallahi banida laifi nima fada mun akayi ba Sharri nayi mata ba. Idan ma kuma baka yarda ba aje a duba wayata lambar qawartata tana nan da duk maganar da mukayi da ita zaku gani wallahi bani na qirqiri maganar ba".

Banza yayi mata ya juya ya fice daga dakin, hankalin Umaimah ya dugunzuma, ita bata ma san ina suka kawota ba tadai san office din Jami'an tsaro ne amma bata san wadanne iri ba shikenan daga zuwa se yace ze kaita Kotu? In ma kullewar Za'ayi ai qawar Hadiza zasu nemo su kulle tunda ita ta fada mata ai.
Sake bude qofar akayi mutumin ya dawo yana kallonta yace

"Wacece wadda kika ce ta tura miki kuma ina wayar taki take?"
"Nima bansanta ba kawai a waya muke magana, amma ka bani aron wayarka na kira gida se su kawo wayar tawa daga nan ma seka fada musu inda nake dan nasan yanzu suna can hankalinsu a tashe yake basu san inda nake ba" Umaimah tayi caraf ta fada se ya tsaya yana kallonta wannan yarinya lamarinta da ban mamaki yake, da alama ta dauka shirin film sukeyi ko amma zata gane kurenta. Fita ya sakeyi daga dakin babu jimawa wata mace ta shigo itama fuskar dai kamar Hadiri tace mata ta taso. A gaba ta tasata a zatonta gida zasu maida ita se gani tayi sun sake shigewa can cikin gurin, birki taci ta shiga zare idanu ganin inda ta kawota, Cell ne Matan dake ciki suka zuro musu ido kamat Kura taga Nama Umaimah ta hadiye yawu dakyar ta kalli mayar tace

"Dan girman kuyi haquri ku maidani gida wallahi iyakar gaskiyata na gaya muku, in baku yarda ba muje tare na baku wayata se ku nemota nidai ku qyaleni" bata kulata ba ta iza qeyarta har zuwa gaban wani Cell da babu kowa Se Rufaida tana can qurya ta hade kai da Guiwa itama Umaiman saboda kayan jikinta ta gane ta.
"Shiga ciki Malama idan ba so kike jikinki ya yagaya miki ba" Matar ta fada tana turata, Umaimah ta maqale a bakin qofar tana cewa
"Fitsari nake ji toh" banza ta mata taja qofa ta mayar ta kulle ta juya kan sauran Matan dakw cikin dakunan tace

"Saura naji wani surutu" ta fice daga gurin tana fita kuwa wata me suffar Yan daba ta matsi jikin qofar su Umaiman harda zura hannu ta jikin qarfe zata tabata tayi saurin yin baya suka kwashe da dariya kamar wasu mahaukata matar tace
"Daga yanayinki dai nasan qaramar kwaruwa ce baze wuce ashe Kishiya kima yiwa wani abun ba aka kawoki nan ko?"

Murguda mata baki Umaimah tayi tana hararta tace
"Aa Uwar kishiya ba kishiya ba, dallah malama kiyi takanki ina ruwanki da ni da abinda ya kawo ni? Naji ni kalar qananan qwari ke ai ana ganinki anga anga Tsohuwar yar ta'addah".

"Gyara kintsi yarinya idan ba haka yanzun nan nayi miki balli balli, naga alamar kanki yana hayaqi to kibi a sannu baki san inda kika shigo ba. Ni in fardeki in miki tiyata a nan gurin qaramin abu ne a gurina nan da kike ganinmu mun ci dubu se ceto" Daya daga cikin Matan ta zaburowa Umaimah ganin tana neman ta zagi shugabarsu. Umaimah tayi ciki can kusada Rufaida a tsorace jin za'ayi mata Tiyata da alama wadannan manyan yan tasha ne.

"Rufaidah ya akayi kika zo nan kema?" Umaimah ta fada tana dafata kamar tana jira kuwa ta dago cikin bacin tace
"Tambayata ma kikeyi ya akayi nazo bayan kece sila haka nan ina zaman zaman kin jefani a masifa daga taimako to wallahi idan Allah yasa muka fita daga nan kowa yayi takansa babu ni babu ke ballantana ki ringa janyo magana kina sako ni a ciki a ringa kulleni a Cell"

"Lallaima to daman gayyatar ki nayi ko kuwa ni bace kije ki dora a Facebook ni bance kin jawo mun ba tunda nasan ai ta silarki har aka bincikoni se kece zaki ce wani waye waye aikin banza kawai duk kinbi kin wani rikice kamar wadda akace tayi kisan kai" Umaiman ta hayayyaqo mata itama se kuwa Rufaida ta miqe tana cewa

"Ai da banyi kisan kai ba gashi nan an sakani cikin Yan ta'addah, wallahi Allah ya isa tsakanina dake Umaimah idan har naje Prison ta dalilinki bazan taba yafe miki ba" ta qarasa tana sake fashewa da kuka wiwi kamar yarinya. Hasko kanta kawai takeyi a prison yanda take jin labarin irin gwale gwalen da ake sha ina zata iya, da ace tasan yarinyar nada daurin gindi da bata saka kanta a sabgar Umaimah ba, yanzu gashinan daga solidarityn qawance se ta zurme da gidan yari gaskiya Umaimah ta cuceta.

A can waje kuwa bayan dogon cuku cuku da Yaya Aminu yayi dakyar ya samu jin bayanin tuhumar da akeyiwa su Umaiman, kansa ya dafe yana kallon Detective Adnan dake kora masa jawabi ya qarasa yana cewa
"Yanzu abinda ya rage mu samu ita wadda tace ta tura mata hotunan a farko daga nan zamu tattara dukka shaidun da muke dasu mu turasu koto ta yanke musu hukuncin daya kamata dan haka muna buqatar wayarta tace komai yana ciki".
Jiki a sabule ya koma ya shaidawa su Mama abinda aka gaya masa daidai lokacin Khalil ya dawo daga Sallar Azahar din da beyi ba, ya kalli Mama dake hawaye tana cewa
"Yanzu daman Umaimah ce? Itace ta tozarta yarinyar nan haka duniya gaba daya take mata tofin ala tsine amma shine a gabanta muke maida zancan yarinyar nan tayi funfurus bata ce komai ba yanzu ina zata kai haqqin wannan baiwar Allah? Me yake damun Umaimah anya Umaimah naso ta gama da duniya lafiya kuwa?"

"Aa Mama ki dena fadar haka, addu'a dai zaki ci gaba dayi mata kina nema mata shiriya a gurin Allah shine kadai mafita" Anty da gaba daya itama jikinta yayi sanyi ta fada. Mama ta goge hawaye da gefen Hijabinta tace
"Tunda na haifi Umaimah ban huta ba Saratu ke shaida ce babu ta inda na banbanta tarbiyyarta data sauran yan uwanta amma ta fita zakka a cikinsu. A kullum abinda yake faranta mata rai shine ta dakko mana magana, duk wani abin tsiya Umaimah ce daga yari tarta har girmanta bata barmu mun huta ba se yaushe zamu rabu da Jidalin Umaimah?
Wallahi da nasan fitinar da zata zamar mun kenan dana zubar da cikinta na huta tun tuni qila da Rayukan kowa ya zauna qalaubarshi ya shiga" ta qarasa tana rushewa da sabon Kuka wani Dattijo dake tsaye gefensu shima tasa ta kawo shi yace

"Ashsha Ashsha kiyi gaggawar yin istigfari ki nemi yafiyar ubangiji. Duk abinda kikaga Allah ya jarabci bawansa dashi yasan ze iya ne kuma Duk mumini baya rayuwa haka ba tareda jarabawa a rayuwarsa ba, idan rai ya baci ya kamata asan abinda baki ya furtawa dan a lokaci da yawa Dan Adam yana warware Ayyukansa da kansa ba tareda ya sani ba. Yanzu da kanki kin fadi kina yi mata Addu'a kina nema mata shiriya a gurin Allah sannan idan ranki ya baci kina jifanta da Kalamai masu muni wanda sune suke dada tasirantar rayuwarta.
Kinsan kaifin bakin uwa kuwa? Ko fushi kikayi da ita a zuciyarki abin seya shafeta ballantana kin bude baki kin jefeta da mummunar kalma ya za'ayi ki ambaci Yar da kika haifa a cikinki da Fitina kuma kiyi tunanin Ubangiji baze jarabceki da ita ba?
Kin zubar mata da hawaye, kin aibatata kin butulcewa Allah bisa kyautar da yayi miki ta samunta kinga kuwa bazaki taba ganin daidai akanta ba.
Chapter 111 · 0% Book details