← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 190 OF 267

Sashe 190

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A hankali yace
"Toh Kawu, nagode kwarai Allah ya qara girma Allah kuma ya dawo daku lafiya"
"Ai dole ka gode mun mana dan qusa irin wannan cin bagas da kayi koda yake cikin iyayen yarinyar akwai Abokinka MJ yace sunan daka sanshi dashi seda safe ka dai ji abinda na gaya maka idan kuma kaudi ya kaika ka gaya mata shikenan".
Mamakin MJ da Baba Abu ya kira ya kamashi tabbas MJ constructions dan Jalingo ne ashe sirikinsa nema be sani ba. Komawa yayi cikin kujera ya kwanta yana jin karadin Jalilah dake buge bugen waya lokaci daya yaji zuciyarsa ta washe wani farin ciki ya lullubeta, a fili ya yi Hamdala har sau uku seya sake daukar wayarsa daya ajiye ya shiga kiran layin Humaira amma harta katse bata dauka ba, ya sake kira karo na biyu bata dauka ba seya shiga rubuta mata saqo kamar haka
"Nayi alqawarin zama mutum na farko da zanyi miki albishir din kin zamo tawa, dukda nasan kin rigani ji saboda abun ya shammacemu duka nida ke bazan haqura ba ina farin cikin sanar dake cewa kin zama matar Khalil, tun sanda nafara ganinki naji a jikina kedin Alkhairi ce a rayuwata. Ina roqon Allah daya sanya Alkhairi da Albarka a cikin tarayyata dake ina Alfahari da kasancewarki Mata a gare ni Humairata I love you moreee" ya hada da Emojis na heart da kiss ya aika mata.

"Babana" Muryar Hajiya ta fito dashi daga shauqin daya tafi, jinsa yakeyi kamar bashi da sauran wata damuwa a duniya. Hasaso kansa kawai yake rungume da yar babyn tasa da ta zama halaliyarsa a sanda be taba zato ba duda yasan ze sha daru qarshema kacokan ta dora masa laifin cewar shiya saka a daura musu aure amma wannan duk me sauqi ne, burinsa shine auranta kuma Allah ya cika maaa sedai yayi fatan ta zamo Alkhairi a rayuwarsa.
"Babana kaji lamarin ubangiji ko? ashe auran a kurkusa yake irin wannan rabon ne fa idan kayi ja'inja dashi se ayi babu kai? Hajiya ta sake fada se ya shiga shafa kansa ya kasa ma hada ido da ita wata kunyarta taji ta kamasa yanda kasan wanda ya kwana dakin Amarya kansa na qasa yace
"Wlh Hajiya har yanzu mamaki nakeyi abin kamar wasa, Mansur ne ya fara kirana duk banma gane abinda yake cewa ba ashe ma Baba Abun ya kirani se yanzu muka sake yin waya dashi"
"Haka yace toh ubangiji ya sanya Albarka Allah kuma ya kade fitina sedai ni yanzu babban tashin hankalina yanzu Khalil matarka ce ta yaya zata fahimci wannan al'amari?" Hajiya ta qarasa maganar cikin muryar damuwa.

Kallonta Khalil yayi, tunda ya darsa qarin aure a zuciyarsa yana yawan Hasaso a yanda irin wannan rana zata riskeshi da kuma yanda Umaimah zata karbi Al'amari, kuma bisa mamaki se yaji sam hankalinsa be tashi ba farin cikin da yake ciki ya saka yake jin komai ma da zezo me sauqi ne, Allahn da ya qaddara faruwar auran shi ze wanzar da zaman lafiya ya kuma sanya mata dangana, yana fata yana kuma addu'ar Umaimah ta karbi abun da kyakykyawan tauhidi ta yarda cewar Allah ne meyi babu kuma wanda ya isa ya qetara masa iyaka. Ajiyar zuciya yayi ya kalli Hajiyar yace
"Duk ma wani abu yanzu Hajiya ai daga baya ne aure dai an rigada an daura nasan zatayi tashin zatayi rigima zatayi duk abinda zuciyarta ta ingizata tayi amma na lokaci ne dole da kanta zatayi ta gaji ta kuma haqura tunda babu yanda zamuyi da abinda Allah ya qaddaro".

"Hakane to Allah ya shiga cikin al'amarin ya kawo faruwar komai cikin sauqi, Abubakar dai yace kar a gayawa kowa to ita waccen uwar karambanin gata can ta gama gayawa yan uwanta dukda dai na tsawatar mata akanta gaya musu maganar ta tsaya iya mu cikin gidan nan, se kaje kayi tunanin ta hanyar da zaka fada mata wannan maganar amma ka bari ba yanzu ba mu jira har zuwa Allah ya rabata da cikin jikinta lafiya tukunna se ayi wacce za'ayi" Hajiyar ta sake fada. Shiru sukayi kowa da tunanin da yakeyi a zuciyarsa. Jalilah ta fito cikin shirin tafiya ta kalle shi tace
"Ango kasha qamshi irin wannan murmushi tunanin me kakeyi?"
Kallonsa Hajiya tayi yayi sauri gyara zamansa dakyau yana daure fuska tareda hararar Jalilan shi kansa besan murmushin da yakeyi a zuciyarsa ya fito fili ba ita kuma da bata gani tayi shiru shine se tayi magana
"Da dai kin wuce kin tafi gida kina gani har goma saura" Hajiya ta fada swta yafa Mayafinta tace
"Ai tafiyar zanyi Hajiya ni wlh tsabar murna ma ji nakeyi kamar nayi kwanciyata a nan nasan ko naje gidan ma ba iya bacci zanyi ba wlh Allah Allah nake gobe tayi in dawo"
"Daman karki kuskura naga qafarki a gidan gobe bama gobe ba sati biyu nan gaba bama gayyarki kuma kin daiji abinda nace nasan Jamila da Amina basuda dan banzan surutu da neman magana irin naki, Habiba da Khalifa basu sani ba dan haka in har naji maganar nan a wani guri kece kuma se ranki ya baci" Hajiya ta fada seta zumbura baki ciki ciki tayi musu sallama ta fita, Jalilah na fita Hajiya ta kalli Khalil tace
"Bi bayanta, Jalilah ba gudun magana take ba yanzu se kaji wani abun"

Ilai kuwa yana fita a qofar shiga bangarensu ya tarar da ita tana kwankwasawa dan dazu daya fita ya saki Jamlock din
"Me zakiyi a nan kuma?" Ya fada yana qarasawa seta kalleshi tana murmushi tace
"Sallama zanyiwa Uwar gida yau duk bamu hadu ba tunda nazo" ya bude baki da niyyar bata amsa aka bude qofar Umaimah ta leqo ta saka dogon Hijabi qamshin turarebta ya bigi hancinsu. Qara washe baki Jalilah tayi tana kallonta tace
"Uwargida sarautar mata ina wuni, ya jiki jiki? toh Allah raba lafiya".

Tsaki Umaiman taja ganin itace ta juya ba tareda ta amsa mata ba Khalil ya ballawa Jalilah harara yace
"Toh neman maganar taki be samu guri ba ki tafi dan Allah seda safe"
"Korata kakeyi daga gidanka ko Khalil ai shikenan nida na sake taka qofar nan se randa na kawo Amarya daga nan se naga uban daya isa yamun iyaka da shiga gidan dan uwana
"Allah ya bamu Alkhairi" ya sake fada yana jan hannunta kamar yar yarinya, seda ta shiga motarta Sammani ya bude mata Get ta leqo cikin shaqiyanci tace masa
"Amma dai zakaje kadan ji dumin yar shilarka ko tunda Allah ya ceceka kaima dai yau ka canza ka rungumi sabon jini"
"Allah ya shiga lamarinki Jalilah" ya fada yana dariyar dabe shirya ba, Jalilah shaqiyya ce ta gaske neman rigimarta kuwa besan a inda ta samo shi ba dan Babansu har yafi Hajiya sanyin Hali nesa ba kusa ba. Be koma bangaren Hajiya ba kai tsaye ya wuce nasu bangaren, be tarar da Umaimah a falo ba se Tv da take aiki ya shiga kitchen ya dakko ruwa ya fito kenan itama ta fito daga daki ta cire Hijabin, wata Bubu gown ce a jikinta pure cotton ta kwanta a cikinta sosai ya kalleta se yaga kamar cikin a karkace yake indai ba idonsa ne be gani da kyau ba.

Fuska ta sake hadewa ta zauna a qasa sgi kuma ya hau kujera duk wata nutsuwa da yake da ita ya tattaro ya aza wa kansa dan baya so yayi abinda ze tunzurota balle har ta fahimci wani abu saboda Umaimah shu'umace, kamar me aiki da Aljannu yanzun nan tana iya karanto masa abinda yake cikin zuciyarsa.
"Ka ja mata kunne wlh idan ta sake shiga sabgata ba zatayi mana da kyau ba daman bawai na haqura da abinda tayi mun bane danbata mari banza ba lokaci kawai nake jira da zan rama" Umaimah tayi magana seda ya gama sauraronta kafin cikin sanyin Murya yace
"Allah ya baki haquri ba kuma zata sake ba Mari kuma da kaina zan rama miki karki damu"
"Qaryar banza kawai, kumada take cewa zata rako Amarya duk yar abu takzan uban da tsautsayi yasa ta shigo gidan nan da ita da masu rakotan sedai a fita da gawayinsu danma mutum ya sani qonasu zanyi qurmus babu abinda ya shafeni" ta sake fada shidai shan ruwa yake kamar an sakashi dole ya sake ce mata
"Ai kinci gida naki ne kiyi yanda kike si babu wadda zata shigo miki".

Banza tayi masa ganin ta maida hankali kan Tv yasa ya miqe yana ce mata
"Babu dan wano snack a gidan ne?"
"Babu" ta bashi amsa kai tsaye ba tareda ta kalleshi ba, se yayi hanyar Bene yana cewa
"Bari na duba Sama kwadayi nakeji nasan bazan rasa ragowar Biscuit din Bibi ba oh that's reminds me yaushe zasu dawo gobe fa akwai Tahfiz"
"Na taba tambayar sanda zasu dawo idan sukaje gidan yan uwanka? Kasan dai ba cinye su za'ayi ba se ka jira goben tayi kaga ba'a dawo maka dasu ba kafin kayi magana uban yan son yaya" Umaimah ta fada a hasale tana kallonsa.
Chapter 190 · 0% Book details