← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 212 OF 267

Sashe 212

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fadar irin tashin hankalin da sukayi da Safina bata baki ne, ta manta da zancen wani dinki da yake a jikinta da qarfin da kowa yayi mamakin inda ta samoshi saboda ganin tunda ta farka bata iya wani motsa jikinta dakyau se gashi ta kama Safina ta sakata a kwana ta ringa kilarta aka rasa me kwatarta saboda kowa yana tsoron ya shiga ta hada dashi.
Ta zagi Safina da kafatanin danginta ta kuma tsinewa Malaman Safina da Ahalin su gaba daya ta kuma jaddada mata da ta nemo mata duk kudadenta data san ta karba ta kaiwa Malamai idan ba haka ba se tayi mata abinda harta mutu baza'a sake hada baki da ita a yaudari wani ba. Dakanta ta ringa shelanta irin abubuwan Safinan ta kaita tasa akayi mata ashe duk yaudara ce tunda gashi nan har Khalil din yayi aure bata sani ba qarshe ta karbi tukuicin Saki sanadin wannan uwar sabada da akaci seda dinkin jikinta ya bude aka sake maida mata da wani jiki ya dawo danye sati daya ya kamata a sallameta amma seda ta shafe sati biyu a Asibitin cikin wani mawuyacin hali kafin suka sallamesu gaba daya ta koma gida da Babynta Malika wadda ta karbeta bisa tirsasawar Abba da yayi rantsuwa akan in har bata karbi yarba kamar yanda take iqirari sedai ta nemi wani gidan uban badai nasa ba.

Ta karbeta dukda seda suka qulla yarjejeniya akan Idan Malikan ta cika shekara daya Khal ze karbi yarsa, kuma yace ya dauki Alhakin samar musu da duk abun buqata har zuwa wannan wa'adin, zaman Asibitin da tayi kaf shiya biya kudin sannan yan uwansa basuyi qyashin siyan duk wani abu da Jaririyar zata buqata ba sun kai gidansu Umaimah, dukda zafinta da sukeji be shafi yarsu ba. Sun yi mata ragon suna da duk wani abu da akeyi lokaci kawai suke jira shekarar da aka diba ta cika daga nansu karbi yarsu su hada da Sauran saboda koda ace Umaimah ce ta buqaci su bar mata yaran babu yanda za'ayi su yarda ballantana da har ta budi baki tace bata qaunar ganinsu, yanda Ubansu ya fitar da ita daga rayuwarsa itama ta bar masa dunda daman bada su taje ba.

Mamakin da lamarinta yake bawa mutane kadan ne, daman sunsan dacewar zata iya aikata abinda yafi haka ma amma da yawa sunyi zaton rabuwarsu da Khalil din da yanda abubuwa suka wakana zasu ladabtar da ita ta koma cikin saiti sedai ko kusa a lissafin Umaimah ba haka bane, ta qulla a ranta duk aje a dawo Khalil baze taba rayuwa babu ita ba kuma tana zaune ze dawo gareta a lokacin zata jashi aqasa ta rama duk wani wulaqanci data fuskanta a dalilinsa shi yasa sam hankalinta beyi wani qololuwar tashi ba dukda idanta tuna yana tare da wata macen ba ita ba se taji kamar ta hadiye zuciya ta mutu amma tasan na dan lokaci ne matsawar da zatayi daga kusa dashi kuma ze qara bata damar tsara ta yanda zata magance komai a lokaci daya.

KHALIL

A bangaren Khalil kuwa Sakamakon gwajin da akayi masa ya fito kuma ya tabbatar da ya samu Nakasa a al'aurarsa a gurin sa abun be zo masa a bazata ba domin ya rigada ya sakawa ransa faruwar hakan tashin hankalin da kadai ya fuskanta shine rashin iya controlling fitsari da yakeyi, daman tun bayan da aka kaishi suka saka masa robar Fitsari shika dai ne fargabarsa ace ze dawwama yana amfani dashi bayaga haka duk wani qalubale da ze bibiyeshi me sauqi ne yana kuma roqon Allah daya bashi ikon Jurewa kuma cikin ikon Allah randa ya cika sati daya suka cire masa robar kuma be fuskanci wata matsala ba, abunda kadai ya rage masa ciwon mara da yake fama dashi lokaci zuwa lokaci wanda likitan yace yaci gaba da shan magani da yardar Allah ze rabu dashi maganar samun daidaituwar lafiyarsa ce wannan ya fawwalawa Allah domin shine meyin yanda yaso, kai tsaye baze ce masa ya samu tawaya ta har Abada ba domin babu yanda Allah baya iya juya lamarinsa amma mawuyacin abune koda ace ya warke lafiyarsa bazata dawo gaba daya ba haka suka sallameshi ya koma gida sedai ya ringa zuwa check up lokaci lokaci.

Ya koma gida ya cigaba da Jinya cike da zullumi da tausayin Humaira da ko kadan bata gajiya da kulawa dashi tun ya na gadon Asibiti har zuwa sanda aka sallamo shi haka yan uwanta sun nuna masa karamci, su suke qara qarfafa mata guiwa tareda sake nuna mata dumbin ladan dake tattare da aikin jinyarsa da takeyi. Idan ya kalleta tausayinta da soyyarta suna qara nunkuwa a zuciyarsa amma ya qudurwa ransa baze taba bari son zuciyarsa ya sa ya cutar da ita ba, ze yi mata adalci ya kuma yiwa kansa Adalci shekarunta sunyi qanqantar da ze tauyeta ta zauna dashi da lalurar sa baze yarda ya zama me son zuciya ba ze sallameta taje ta auri wani tayi rayuwarta shi kuma ya rungumi qaddarar sa a yanda tazo masa. Dangane da Umaimah kuwa da abinda tayi masa ya fawwalawa Allah komai ya kuma dauki abinda ya same shi a matsayin qaddararsa yana kuma roqa mata sassauci a gurin Allah sannan yana mata fatan Alkhairi akan duk rayuwar da zata fuskanta a gaba. Baze qullace ta ba kuma yayi mata uzuri saboda yasan duk abinda ta aikata Soyayyarsa ce sila, haka ya fawwalawa Allah komai be sare ba dan haka ya shiga neman Asibitoci a qasashen qetare da suke da kwararru akan matsalarsa zeje ya gani saboda shi magani baka san inda zaka dace.

UMAIMAH

Umaimah ta sake koma gidansu amma wannan karon a Matsayin Bazawara, dakinsu na yammatanci ta gyara ta shiga kimanin watanni uku da rabuwarsu da Khalil kenan amma gani takeyi kamar ba gaskiya bane, dauka takeyi ireiren sabanin da suka saba samune ta taho gida bayan wani lokaci ze huce ya dawo ya maida ta dakinta Musamman irin yanayin da take ciki na cewar babu abinda ta nema ta rasa se kulawarsa data yan uwanta. Tunda ta dawo gidan bata qara samun wayarsa ba kai ba shikadai ba hatta Hajiya idan ta gwada kiranta wayar bata shiga harta gaji ta dena bayan dawowarta gida dai Khalilfa yaje sau daya ya kai musu saqo dukda be shiga gidan ba a waje ya tsaya ya bawa yara tulin uban siyya duk wani kayan amfani daga kan naci zuwa na tsafta seda ya siya ya aika mata dashi kamar yanda yayi alqawari sannan ya dora mata da dubu Ashirin a kan kayan.

Sanda yara suka shiga dashi Mama na zaune a tsakar gidan ta tambayesu daga ina suka ce mata wani Khalifa ne yace a kawo. Bata sake ce musu komai ba suka gama ajiyewa suka fita dan da Umaimah da duk wani abu daya shafeta ta dade da jingine su a gefe. Tsakaninta da ita ido idan sun hadu kenan tayi mata iyaka da shigar mata daki kuma bisa dukkan alamu abun be dameta ba dan bata nuna ba sabgoginta kawai takeyi wuni guda tana daki ta kwanta nan ta tashi can tunda hidimar yar ma Anty ce take yi mata ita dai a zuciyarta tana yi mata fatan shiriya idan tana da rabo dan babi wanda ze so yaga nasa ya halaka rana gobe qiyama. Haka rayuwa taci gaba da gungurawa sannu a hankali kwanaki suka ci gaba da shudewa Umaimah na nan zaune gidansu ita da me zaman kanta marabarsu qalilan ce domin kuwa babu me sakata haka babu me hanata domin kwata kwata idan ka cire Anty a gidan ma babu me shiga shirginta se Yasir da lokaci lokaci takan aikeshi ya siyo mata kayan kwadayi duk ranar da aka girka abinda beyi mata ba tunda tana da uwar kudinta gashi duk watan duniya bayan kayan abinci Khalil din zo doro mata dubu Ashirin yasa take sharafinta son ranta kuka babu wanda ya daga kai ya kalleta kamar yanda Abba yace Duniya tafi bagaruwa iya jima tayi yanda take so ba ranar kuka tana gaba.

Tunda tayi tayi ta samu Khalil a waya abin ya faskara ta haqura ta watsar dashi, abu daya ta ajiye a ranta ze dawo gareta dan baze iya rayuwa babu ita ba. Maganar Humaira ko a ranta ma gani takeyi basa tare domin ta tabbatar ba zata zauna da Khalil din da lalurar data sameshi ba ko bata nemi rabuwa dashi ba yan uwanta ba zasu barta taci gaba da zaman ba shiyasa ta kwantar da hankalinta sosai kamar babu wani abu tana jiran lokaci kawai da Khalil din ze kawo kansa a sannan zatayi masa wankin babban bargo ta qarasa tashin hankalin da batayi a baya ba.

KHALIL

Sannu a hankali rayuwarsa ta daidaita bashida wata matsala da ze iya cewa gata idan bata lalular data sameshi ba. A bangaren zamansu da Humaira kuwa babu abinda ze ce sedai ya godewa Allah kamar yanda a koda yaushe bakinsa baya gajiyawa gurin godewa ni'imar da yayi masa. A cikin watanni shida da auransu ya samu nutsuwar da besan da ita ba a tsayin shekaru Bakwai daya shafe da Umaimah. A yanzu ne ya san yayi aure ya kuma san dadin aure, irin kulawar da Humairan tak bashi tana saka ya manta da duk wata damuwar duniya idan yana tareda ita baya tuna komai da kowa se ita dashi ta shayar dashi zallar madarar soyayyar da ya dade yana mafarkin samu shi yasa be tauye kansa ba ya ware ya ajiye komai ya rungumi Matarsa suke zuba qauna domin tayi masa halacci ita da iyayenta da har ya koma ga Allah baze biyasu ba.
Chapter 212 · 0% Book details