← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 267

Sashe 27

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"In banda sharri Naziyya a ina aka taba cewa biyayyar mace tayi yawa? Yaya Hafsa ta fada tana dariya, Naziyya ta Harari Umaimah dake jifanta da wani kallo saboda ambaton auro mata wata da tayi tace

" Wallahi fa Yaya baki taba ji bane? Nan ga maqociyata nan da aka mata kishiya matar nan babu ta inda ta ragi bawan Allahn nan amma da yake Namiji Namiji ne se gashi wai zeyi aure saboda ita komai yace mata bata musawa zatayi wani lokacin ma bece tayi abuba zatayi shi kuma baya son haka, yafi so wani lokacin dai itama ta dan nuna nata ra'ayin bawai komai ya fada tace daidai bane, ai kuwa yanzu ya samo me ido a tsakiyar kai, tace tana jinsu wani lokacin zata cancareshi amma mutumin nan ko a jikinsa tunda shi abinda yasa ya aurota kenan toh balle Umaimah me suma akan Saurayi idan akayi auran kuma ai se mutuwa".

Qunquni ta shigayi qasa qasa tana cewa "idan gaba da mutuwa ce zanyi ina ruwan mutum, haka kawai baza'a fadi alkhairi akan abu ba ai se ayi shiru nidai babu ruwana baqin bakin mutum ya qare akansa" ta harare su kafin ta fice ta bar musu falon.

Tattauna abinda ya kamata ayi goben sukayi, abin yazo da sauqin musamman da akace mazane zasu kawo dan haka nan take Yaya hafsa ta kira mutuniyarta *Zuhree snacks bar* suka saka orders Meatpie, samosa da springrolls ta kuma tabbatar musu babu matsala zasu karbi order su goben akan lokaci.

Sosai Yaya Hafsa take jin dadin hulda da ita saboda cika alqawari, bayan dan karan dadi da snacks dinta suke dashi ga sauqin farashi duk wanda yaci se ya qara musamman tunda taje taga yanda takeyin aikinta komai a tsaftace shi yasa duk wata hidima data tashi da ake buqatar snacks bata sanya gurin nemo Zuhrii Snacks.
(Domin order snacks dinku na kowanne irin taro, koma haka kawai ki siya ki ajiye a fridge ki ringa soya abinki kina ci ku tuntubeta takan lambar waya 08146426724)

Se dab da magriba suka gama komai dan hatta da kajin da zasuyi pepper chicken an siya an gyara sukayi marinating nasu kafin aka saka a fridge akan Nuratu zata soyasu da safe kafin suzo a qarasa hadawa. Sun kira Aminu sun gaya masa shi kuma ya sanar da kawun nan su daya kamata su halarci karbar lefen yaceze kawo ruwa da lemo iya adadin da sukace za'a bayar Baba Abdullahi kuma yace ze bada tukuici danshima sun yanke abinda zasu bayar idan an kawo kayan.

Har Kowacce ta dauki jakarta zata wuce kenan Naziyya tace "Af an gama lissafin snacks banji an saka da cake ba, ko iya su Samosan za'a basu?"

"Ai kuwa dai nima shaf na manta, Hafsa ki sake kiranta ki gaya mata dashi kar lokaci ya qure" Hajiyayye ta fada, se Hafsan ta zaro wayarta tana cewa "Ina sane dashi, kunsan ko wanne abu yana da gwani, to wata sabuwar gwana na samo a fannin cake. Sunanta *Mcubes bakery, ranar da Baban Mimi ya shigo da wani loaf cake yace a gurinta akayo musu order tsabar dadi har takaddar na hada na cinye, yanzu kuwa cupcakes din yara na makaranta gurinta muke siyowa kar kuso kuji dadin sa koda yake zaku dandana kuji gobe idan an kawo, kai wannan mata ta iya cake, dadinsa baya faduwa se kawai idan kaci bakinka ya gaya maka"

"Gaskiya Yaya Hafsa ki fara sana'ar tallah irin wannan koda cake haka ni har kinsa na qagu naci naji yanda yake, bani numberta ma na ajiye a wayata saboda tsaro" Naziyyan ta sake fada tana zaro wayarta, se Hafsa ta shiga karanto mata tana cewa (08134606093 Mcubes bakery, cake dinda ba'a bawa yaro me qyuya)
"Bazaki gane bane Naziyya sekinci kinji tukunna keda bakya raina abin dadi ai inaga se sunusi ya saka miki waigi" suka kwasheda dariya gaba daya kafin sukayiwa Mama sallama kowa ta hau motarta tayi hanyar gida.

Hajiya Umaimah  kuwa can quryar daki ta shige ta haye gado, kamarbata jin abinda computer take fada nacewar wayar A Kashe take haka taci gaba da kira har seda aka kira sallar Magriba kafin nan ta haqura ta dauro Alwala tayi sallar,bayan ta idad addu'arta gaba daya akan Allah ya mallaka mata Khalil ce ya kuma saka ta ita kadai a zuciyarsa karya taba kallon wata mace da sunan so ko sha'awa bayan ita, bata tashi a gurin ba sedatayi sallar Isha'i hade da shafa'i da wutri kuma har sannan wayar Khalil dintana kashe abinda yasa jiki ta yayi mugun sanyi kenan.

Ta tuno da sanda za'a kawo lefen Nuratu Ango taDr Sagir dakansa ya kirata ya gaya mata cewar za'a kawo tun kafin ma ayo waya daga gidan su a fada za'a kawo din a lokacin har tana mata iskanci saboda gaba daya wayar da sukayi batafi ta minti daya ba yana gama fada mata saqonya kashe Umaiman ta samu nayi wai kamar Wanda za'ayiwa auran dole babu wani zumudi babu komai kawai wani 'Gobe za'a kawo kaya' ya kashe waya" ta fada tana kwaikwayon yanda Sagir din yayi magana, se gashi ita yau bata samu arziqin ma nata Mijin ya kira ya gaya mata ba. Koma dai yaya ne a yanzu babban abinda yake a gabanta shine tabbatuwar auranta da Khalil, dukda wani abu da ze faru ya faru daga baya kuma kawo lefen nan shine babban mataki na gaba da yake tabbatar da cewar maganar auransu tana nan daram.

KHALIL
Tun bayan da suka rabu da Hajiyarsa da kuma matsayar da ya barta akai ya koma gida gaba daya ya kasa sukuni, duk wata hanya da yake tunani zebi dan ya karkato da hankalin Hajiyar ta fahimci abinda yake nufi ya auna yaga bazata bulle ba musamman da ya zamana da zancen Badawiyya a ranta duk wani qoqari da zeyi na fasa auran Umaimah a gurinta zataga yayi hakane danya komawa Badawiyyan wadda sam shi idan badan Hajiyar ma ta tayar da zancen ba ya manta da ita.

Ganin tunani baze fishshe shi ba ga qarin faduwar gaba a duk sanda ya tuna kalaman Umaimah se ya zubar da komai ya kama Allah, Addu' aya dukufa yi babu dare babu rana akan neman zabin Allah.
Kwanaki hudu a tsakani bayan waccen maganar da sukayi sega kiran Hajiyar da rana yana office take sanar masa da cewar ya kawo kayan da suke gurinsa dan gobe za'a kai lefe. kasa ce mata komai yayi in banda "Toh" ya saka hannu biyu ya dafe kansa bayan daya kashe wayar, a duk kwanakin nan da ya tsananta addu'a tamkar ana sake saka masa Umaimah ne a cikin zuciyarsa.

Wani irin sonta da kewarta ce ta addabe shi, ba qaranar dauriya yayi ba da har ya kwashe kwanaki biyar din nan ba tareda ya nemeta ba amma idan ya tuna itama bata sake  kiranshi ba se jikinsa yayi sanyi dan besan ma'anar wannan shirun da tayi masa ba, ta haquran ne ko kuwa wani abun take shiryowa. Koma dai menene yanzu dai magana ta qare tunda yanzu lissafin sati uku akeyi ta zama matarsa.
A daren bayan ya tashi aiki ya hada dukka kayan da suke a gurinsa ya kai gidan babbar Yayarsu Maryam da suke kira da Ummi, yawanci dogayen rigunane da takalma se su agogo da sauran kayan kyalekyalen mata wanda yawancin  abuwan da idan ya gani yayi sha'awane yake siya ko ita Umaiman ta turo masa tace tana so,besan sun taru da yawa ba seda ya ringa zaqulosu shi kansa ya ri ga mamaki kayan. Sanin Halin Ummi da surutu ya saka ya rage wasu daga ciki musamman qananan kaya ya ajiye idan tazo gidan sa se ya bata kawai.

Washe garin da za'a kai lefen da sassafe ya tafi dutse duba wani site da suke aiki, tun yana hanya wayar sa take kukan rashi chaji dan haka yana isa ya kasheta gaba daya ya jona a chajin kafin shiga aiki dukda yaso ya kira Umaimah suyi magana tunda ita taqi kiransa amma ya bari zuwa dare idan nutsu sayi magana kafinya koma Kano.

Ya rigada ya yanke amfani da shawarar Mansur ta cewar  ya sameta suyi magana ta nutsuwa da ze shigar mata da hankali jikinta dan babu yanda za'ayi suyi aure ta tafi gidan sa da wannan tunanin nata na yin fito na fito da duk macen data shiga rayuwarsa, shi be shiryawa tashin hankali ba dan haka idan har taga zata zubar da makaman yaqin su yi qoqarin gina goben su fine, idan kuma hanyar data zaba ita take ganin me billewa a gareta toh tabbas sedai Hajiya tayi haquri, dan yana da inda ze kai maganar da ita kanta Hajiyan bazata tsalkake umarnin sa ba dole ta haqura ta barshi ya nemo wata da zasuyi aure su zauna cikin lumana ba tareda kullum ya fita yana dardar da faduwar gaba ba.

*********
An kawo lefe da yake sabgar maza ce bata mata ba qarfe sha daya har sun gama komai sun juya da tarin kayan tukuicin da akayi musu. Kaya kam se sambarka duk wanda ya gani se ya yaba abu ne sukayi shi cikin tsari. Basuyi qarya ba haka babu qaranta daidai rufin asirin yanda babu inda za'akai kayan a raina su dan gaba daya kayanta manyan suturune kuma kaloli masu kyau da tsari se tsokanarta sukeyi wai tayi goshi amma ita sam ba wannan ne damuwarta ba, rashin ji daga Khalil har zuwa wannan lokaci yafi komai daga mata hankali.

Da safen har ta quduri niyyar zuwa office dinsa taji ba'asin kashe wayar da yayi sedai wayar da sukayi da Rumasa'u ta hana ta zuwan, dukda haka bata haqura ba, idan har wunin yau ya qare Khalil be kirata duk inda yake seta nemo shi taji matsayar ta a gurinsa, shiyasa ma ta hada kayanta idan Yaya Hajiyayye ta tashi tafiya binta zatayi taje ta kasa ta tsare qofar gidan su ayi wacce za'ayi kawai.
Chapter 27 · 0% Book details