← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 267

Sashe 138

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tayi zurfi a tunani Samarin dake karatu a masallaci suka fito, daya ya kalleta yace
"Malama lafiya kuwa tun dazu kike zaune anan?"
Niqab din fuskarta ta daga dan kar suyi mata zargin rashin gaskiya, wani gida data gota taga kwado a Get din ta nuna musu tace
"Can gidan nazo kuma nayi rashin sa'a basa nan shine na zauna nake hutawa anan"

"Ayya halan bakuyi waya ba, ai bana jin sunyi cikakkiyar awa da tafiya garinsu ma sannu kuma da alama daga nesa kike?" Wanda ya fara mata maganar ya sake fada da ganinsa yana da surutu, se Umaimah ta yamutsa fuska kamar gaske tace
"Kash wallahi ban kiraba dake babu waya a hannuna kuma daga Kura nake"
"Tab sannu gashi kin daki gurbi, seki daure ki tashi ga magriba ta kawo kai yanzu za'a fara shigowa masallaci" dayan da beyi magana ba ya fada me surutun na shirin cewa wani abu yajashi suka tafi. Umaimah ta rakasu da ido daidai nan taga an bude Get din gidan su Zahra ai bata san sanda ta miqe tsaye ba ta nufi gurin.

Khalil ne ya fito wata zuqeqiyar yarinya da a halitta bazata gwada mata komai ba ta biyo bayansa fuskarsu washe suna dariya daga inda take tana jin yarinyar na cewa
"Amma Dear naji dadin zuwanka, harfa su Sury sunyi fushi zasu tafi na ringa lallabasu kaga yanzu ai haka yafi kunga juna kun gaisa ba se lokacin biki yazo ba".

Khalil dake kallonta yana murmushi like an idiot yace
"Ai kuwa dai nima naji dadin haduwa dasu sosai shikenan dai yanzu qorafi ya qare ko?" Ya fada yana aika mata da wani kallo da Umaimah ta zata ita kadai yake yiwa irinsa.

"Baiwar Allah yi a hankali fa karki fadi" taji muryar saurayin dazu ya fada se a sannan ta lura da a guri daya take a tsaye tana kallonsu Khalil din jiri ke neman kadata ta dafe bangon kusada ita shine yake mata magana. Kai ta daga masa ta shiga jan qafarta dakyar numfashinta na mata wuyar shaqa. Khalil da Zahra suka bita da kallo, qirjinsa ya buga da qarfin gaske sanda suka hada ido da matar kafin ta dauke kai taci gaba da tafiya tana cira qafarta dakyar.

Kamar idon Umaimah haka ya gani haka tafiyarta da yanayin jikin sunyi masa kama da nata amma me ze kawota nan? Kuma ya tabbata idan itace tabbas Allah kadai yasan abinda ze faru a gurin. Muryar Zahra yaji tana cewa samarin
"Kai Aliyu wacece wannan din da kuka bari ta shigowa mutane layi da magriban nan da wannan shigar, kunsan dai yanda criminals sukayi yawa ko?" Se wanda ta kira da Aliyu ya bata amsa da cewa
"Gidan Barrister tazo kuma basa nan shine ta zauna gurin masallaci ta huta"

"Dear kaima baka yarda da ita ba ko?" Zahra dataga ya zubawa inda Umaiman tabi ido ta fada se yayi firgigit ya kalleta yana cewa
"An Bari naje na bar Madam a Salon tana jirana zan dauketa".

Fuska ta bata bata ce masa komai ba yayi mata murmushi ya shiga motarsa yana daga mata hannu, hannun itama ta daga masa daga nan yaja ya tafi har sannan zuciyarsa na masa wasi wasi akan wacce ya gani din.
Kiran daya shigo wayarsa ya sakashi dubawa, Umaimah ce, muryarta babu yabo babu fallasa tace
"Base ka biyo daukana ba na wuce gida ban samu kitson ba"
Ajiyar zuciya ya sauke jin cewar ta tafi gida kenab dagaske ba itan bace, lallai tsoron da yakewa Umaimah har ta kai ta fara masa gizo.

UMAIMAH
Dakyar ta iya maida kanta imda Harun yake jiranta, ta zauna a Napep din tana jan numfashi jikinta na wata irin rawa. Harun ya kalleta yace
"Anty lafiya kuwa?"
"Maidani gida" ta fada dakyar kafin ta dora kanta akan qarfen adaidaitan tayi shiru dan ta kasa tunanin komai.
Khalil ya iya yi mata qarya ya taho gurin wata ko?
Wani tunani ne ya fado mata nan ta shiga jan numfashi tana fesarwa har seda taji ta samu nutsuwa kadan kafin ta dauki wayarta ta kirashi ta gaya masa ta wuce gida, gara taje tashirya yanda zataci ubansa a ruwan sanyi. Se yayi danasanin munafuntarta yayi mata qarya wallahi kafin ta juya kan ita qaramar Shegiyar. Wato saboda tsabar ya shirya ci mata mutunchi seda ya samo daidai da ita dan ita da kanta ta yarda ba zata gwadawa Zahran komai ba a halitta sema dai ita ta fita dan ba zaka hada jikin budurwa da Wadda ta haihu har biyu ba.

Bata san ko nawa ta zaro ta bawa Harun ba ta shige gida kai tsaye kan gadon dakinta ta fada wasu hawaye masu dumi suka shiga tsere akan fuskarta idan ta tuna yanda Khalil yake kallon yarinyar yana mata murmushi se taji kamar ta shaqe kanta saboda baqin ciki. Wai meya shiga kanta daya hana ta tsaya tayi musu tijara a gurin? Yanzu meye amfanin dawowar da tayi tazo tana kuka anan?
Wani ihu ta kwara kafin ta miqe ta watso da duk tarin kwalabe da robobin dake kan Mirror dinta, tamkar farin shigan hauka haka ta shiga dukan duk abinda hannu ta ya kai kafin wani lokaci tayi wa dakin rotse hannayenta bada zubar jini babu abinda sukeyi.

A haka Khalil ya dawo gidan, tunda yayi arangama da Hijab da Niqab a kan kujerar palour yaji lakar jikinsa na tsiyayewa, kasa gaba yayi balle baya qirjinsa ya ringa bugawa a sittin wato dai ta tabbata Umaimah ce, kenan bin bayansa tayi, tayi badda kama dan taga inda zeje me yasa sam tunanin zata iya aikata hakan be zo masa ba tun Sanda tace zata bishi ya kamata ace ya zargi wani abu kai tun farko ma shirun da tayi masa yasan ai ba haka kawai ba dole akwai abinda take shiryawa, bashida mafita a yanzu illah yayi mata bayanin komai ko Allah ze sa ta fahimce shi dukda yasan abune me wahala amma ze gwada.

*KAFIN SAUKAR DA KO WACE IRIN CUTA, SAI DA ALLAH SWT YA SAUKAR DA MAGANINTA. DON KIN GWADA MAGUNGUNA DA YAWA BAKI DACE BA BA SHI ZAI SA KI YANKE TSAMMANI BA. KI GWADA MAGANINMU ƳAR'UWA, WATA-ƘILA WARAKARKI NA TATTARE DA MAGANINMU.*
Ƴar'uwa mecece matsalarki? Muna ingantattun saiwoyi da sassaƙe da garin magunguna na gargajiya, waɗanda aka gwada kuma aka tabbatar da ingancinsu.
*Ina matan da basu taɓa haihuwa ba?* Ko kuma sun taɓa yi amma suka samu dogon jinkiri dalilin planning ko kuma haka kawai? Ko kuwa ɓari kike yawan yi, da kin samu cikin sanadiyyar mafarki sai ya fita? Ƴar'uwa albishirinki, da naira 2k kacal za mu baki ingantattun saiwoyin magunguna masu kyau, da za ki dama salala kina sha a jere har na tsawon kwanaki goma sha biyu, bayan gama sha ki zuba ido wata ɗaya, biyu, uku, in Allah ya yarda za ki dawo da kyakkyawan labari.

*Mijinki ne mai matsalar haihuwar?* Akwai magungunan da muke ba maza, shi ma dai da naira 2k kacal za mu haɗa miki magungunan da za kiyi mishi amfani da shi. In Allah ya yarda za ki dawo mana da kyakkyawan labari.

*Ƴar'uwa matsanancin infection/sanyi ne damuwarki?* Ki kwantar da hankalinki. Da naira 3k kacal za mu haɗa miki magunguna kala biyar, waɗanda idan kika yi amfani da su duk yadda sanyi yayi miki illa kuma komai daɗewarsa a jikinki za ki fatattake shi. Sunan wannan haɗi *Bye bye infection.*

*Mijinki ne bai da kuzari a shimfiɗa?* Ƴar'uwa ko ki faɗa ko kar ki faɗa sanyi da basir sun gama yi ma mazajenmu illa, da naira dubu 5k kacal za mu baki dafaffen magani galan ɗaya wanda zai dinga shan ƙaramin kofi safe da yamma. Wannan magani zai taimaka masa wajen fatattakar duk wani sanyi da basir da yake jikinsa, zai dawo da kuzarinsa sosai kamar matashin ingarman doki. Bazai ƙara neman maganin kuzari ba har'abada in Allah ya yarda.

*Ina mata, maza, yara, masu fama da lalurar Cancer/Daji?* Da naira 2k kacal za mu baku ingantattun magunguna kala huɗu da za ku fatattaki daji daga jikinku.

*Ingantaccen haɗin sabaya😍* Haɗin sabayarmu duniya ne ƴar'uwa. Baza muyi miki ƙaryar nonuwanki za su taso su tsaitsaya kamar na budurwa ba, amma fa za su cicciko, suyi kyau, su dinga sheƙi, sannan duk wata rama da take jikinki za ta cicciko, ni'ima bazai yanke miki ba saboda amfani da haɗin sabayarmu.

*Muna da maganin wankin nono ga masu ciki da shayarwa.* Duk ɗauri ɗaya 500.

*Sunana Fareeda Abdallah, a kaduna nake da zama. Amma muna aikawa da magungunanmu ko ina tsakanin Nigeria da Nijer, sai dai duk inda mai siyan magani take ita za ta biya kuɗin mota ko na delivery zuwa gidanta. A tuntuɓeni ta whatsapp ko a kira ni akan lambobin wayata 07039080978, 09077591726. Sai kun zo😍😍😍*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 53

Kamar wani mara gaskiya haka ya tura qofar dakinta da sallama, Umaimah dake zaune a qasa ta dago ta kalleshi da jajayen idanunta dan ba qaramin kuka tasha ba. Yawu ya hade ya shiga qarewa dakin data sauyawa kamanni kallo, besan da me tayi aikin ba amma duk wani abi da yake na glass a dakin ta fasashi kuma tana zaune a cikin gilasan kanta yayi buzu buzu kamar wata hauka sabon kamu. A hankali ya shiga takawa zuwa inda take yana kuma qara baza idonsa dan ya tabbatar da babu wani makami a kusa sa da ita da zata iya yi masa lahani dashi a haka har ya isa gabanta ya durqusa dan tunda tayi masa kallo daya ta maida kanta qasa tana jan Ajiyar zuciya.
Chapter 138 · 0% Book details