← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 267

Sashe 128

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kukan Bibi daya keta jiyowa ya saka shi shiga dakin nata dan a zatonsa ko ta shiga bamdaki ta barta ne sedai yanayindaya tarar da ita dole ya kwasheta suka tafi Asibi babu shiri hankali a matuqar tashe, seda tayi jinyar sati kafin aka sallameta yan gidansu dasu Hajiya gaba daya sun dauka ciki ne da ita musamman saboda muguwar ramar da tayi ta dashe kowanne bangare da suna mitar tunda Mijinta ya dawo ta yada kowa ba inda take zuwa se suka bata uzurin qila bata so a san daga komawa tayi ciki shiyasa ta guji kowa.

Randa aka sallameta suna komawa ta dasa masa kukan gida zata tafi, ba zata zauna ta mutu a banza ba tunda ya dena sonta ya sallameta kawai ai haquri babu irin wanda bata bashi ba idan baze yafe mata ba gara ya sauwaqe mata kawai ta kama gabanta akan baqin cikinsa ya kasheta. Isaraa tayi da surutan banza, dukda jikinta har sannan da saura haka ya jata sula shilla sama lulaye amma wannan karon ya banbanta da wancan, tafiya ce akayita ta nutsuwa suka goge duk wani Virus daya shiga memoryn su ya dawo sabo fil daga nan aka bude sabon babin soyayya da zaman lafiya tsakanin Sabuwar Umaimah da Khalil din nata.

BAYAN WANI LOKACI
Zama yayi dadi tsakanin Habibi Khalil da Habibtynsa Umaimah. Zama ne sukeyi irin wanda Khalil ya dade yana mafarki cikin zallar soyayya, zaman lagiya da tattalin Juna dan Umaiman tasa ta kintsu irin kintsin daya bawa kowa Mamaki ta kowanne banni yanzu ta dauki gyara. Tuni ta koma Islamiyya kamar yanda Maman Asad ta gaya mata, bayan dogon nazari da karatun ta nutsu da tayiwa kanta ta fuskanci gaskiya ta gaya mata dan haka ta sanarma da Khalil son komawa Islamiyya da bokon ya kumayi na'am da Islamiyyar, bokon ne yace tayi haquri. Da akwai shirin da yake dashi idan Allah ya tabbatar zatayi dan haka ta rungumi Islamiyyarta, sau uku sukeyi a sati litinin zuwa Laraba Goma na safe zuwa qarfe daya dan haka da ta gama ayyukan ta na safe zata fita makaranta idan ta dawo ta huta kafinta shiga aikin girki da tarbar Khalil bata da matsalar yara dan Bibi sam bata da rigima Mu'ayhad ko ya zama dan gidan Hajiya sedai yazo musu ya tafi.

Sosai ta qaru da komawar tata Islamiyya ta farfado da karatunta ga kuma sabon karatun darasin rayuwa da take samu a gurin sababbin gogaggun qawayen da tayi matan da suka san me sukeyi ba tarikican qawayen banza data sabayi ba wadannan matane da duk maganar da zasu fada ta qaruwa ce me amfani haka ta sake shiga whatsapp group a karo na biyu bayan Rufaida tasa an cireta daga duk wanda suke ciki a baya sedai wannan karon groups ne na qaruwa da har seda ta gayyato su Nuratu dasu Mamab Asad duk suka shiga harda Anty ba'a barta a baya ba ta shige suna kwasar darasussukan rayuwa daga Matan da sukaga jiya suka ga yau.

A dai taqin shekara da wani abu Abubuwa da dama sun faru na dadi dana akasin haka. Babban abin dadi daya faru shine budin da Khalil ya samu da har ta kai ga ya bude construction company nasa na kansa wanda ya kafu bisa jajircewarsa da kuma aiki me nagarta da yakeyi wanda shine ya janyo masa samun manya manyan kwangiloli da beyi tsammani ba qarqashin Jaririn Companyn sa dake tasowa a yanzu.

Bayan nan se tafiyar Sa Umaimah da Hajiyarsa aikin Hajji wanda suka sauke faralli cikin wannan shekarar. Base na baku labarin Hajiya Umaimah a saudiyya ba, anyi ibadah dai matuqa addu'a kam Khalil ya shata ta Allah ya hana idonsa ganin wata mace bayan ita, Rikici kuwa babu abinda ta fada dan sedai idan basu fita siyayya tare ba. Haka kawai idan abinta ya motsa zatace wata na kallonsa, idan anyi sa'a yar uwarta ce Bahaushiya ta zageta su kwashi fada kowa ya kama gabansa, idan kuwa ba yarenta bane zagi take musu na tsamar nama sedai su kalleta su dauke kai toh basu ma san abinda rake fada ba kuma duk abin nan bata tabayi a gaban idon Hajiya ba, dan yawanci yawon Kasuwar su Hajiya bata binsu se tayi zamanta a masauki shidai Khalil Sallar sa da dawafi kaf babu a wanda baya roqarwa Umaimah shiriya da kuma zabin Allah akan komai na rayuwarsa, haka dai aka sauke Hajji lafiya aka dawo gida nan kuma Umaimah ta tarar da sabon abu, ginin gidansu da akeyi an canza masa fasali daga yanda aka qirqire shi zuwa zaman Mace biyu a tata fahimtar.

Asalin ginin komai anyi shine a cakude, bangarenta dana Khalil din a hade suke amma suna dawowa yace taje ta duba gida a fara shirin zuba kaya dan damansun siyo wasu abubuwan irinsu Labulaye da Carpet tana zuwa taga wannan tashin hankali, part guda Khalil din ya warewa kansa saboda rainin hankali a cewarta fa harda Kitchen da store, guri dai tsaf kamar mace za'a ajiye.

Babu kalar rantsuwa da bayanin da beyi mata ba ta toshe kunnenta, ta ringa tijara tana rashin mutunchi a gaban ma'aikata, bokitan penti da aka ajiye dan ana pentin gidanne haka ta ringa bi tana zubar masa dasu penti masu tsadar gaske. Ran Khalil ya baci matuqa, babban abin kuma daya qara bata masa rai da sukaje gaban Hajiya ta goyi bayanta.

"Akan me zaka canza tsarin gidan kuma ba tareda kayi shawara da ita ba?" Hajiya ta fada cikin fushi tana kallonsa. Khalil ya kalli Hajiya ya kalli Umaimah dake faman share hawaye bayan tazo ta gama zayyanawa Hajiyar qarya da gaskiya ya hadiye wani abu me daci daya tsaya masa. Badan be taba kama Umaimah da wani abu dayayi kama da Bin Malamai ba da tabbas zece Asirce Hajiya tayi, wannan makauniyar soyayar da Hajiua take mata ba kuma ta ganin laifinta abin yayi yawa. Gyara zamansa yayi yana cewa

"Hajiya ni sam ba abinda take tunani bane yasa nayi hakan. Kinga dai tsarin ginin a farko komai a cakud akayi shi, babu wani kebantaccen guri ko ina kowa yana iya shiga akoda yaushe babu sirri ni kaina se daga baya naga rashin dacewar hakan a matsayi na na me gida ya kamata ace ina da turakata data qunshi komai da komai a ciki bana buqatar fita idan ina buqatar wani abun.
Sannan iyali muke tarawa dole yaranmu wata rana zasu girma, be kamata ace muna cakude dasu a koda yaushe ba dole akwai buqatar sirri tsakaninmu ni wannan ne kawai dalili na ba wani shirmenta mara tushe ba"

"Kuma ahine harda Kitchen da store duk a bangaren naka? Three bedrooms ga qaton palour da dining duk me zakayi dasu?" Umaimah tayi tsugul ta fada kafin ma Hajiyar tayi magana, Harara ya galla mata kamar idonsa ze fado ba tareda yayi magana ba jin Hajiya nacewa
"To ai kamata yayi tun kafin ayi seka gaya mata, base kawai tazo taga abu ba ai koma wacece tunanin daze zo mata kenan a zuciya"

"Idan qara auren tana da hujjar Hanani ne ko kuma akwai Haramci a cikin Hakan?" Yayi wa Hajiya tambayar amma idonsa akan Umaimah data gwalo nata idanun saboda jin wannan gingimemen tashin hankali,

"Bana son neman rigima Khalil, bana so. Ke kuma kinji abinda ya fada dan haka karna sake jin wata magana bayan wadda akayi a nan" Hajiya ta fada musu gaba daya Khalil be jira yaji koda sauran maganar tata ba ya tashi ya fice daga gidan cikin bacin rai. Iya Asarar pentindata masa da yawa kuma wallahi zata sani a cikin kudin da yayi niyyar bata na gyaran gidan idan yaso in basu isa ba ta tare da tsofaffin kayanta. Ya gaji da iskancin Umaimah ba kuma ze sake biye mata ta mayar dashi kamar wani takalmin sawarta ba.
Ya dauka nutsuwar da tayi tun bayan wancan Al'amarin ta gaske ce tunda gashi kusan shekara daya da wani abun bata sake masa shirme ba suna zaune lafiya se yanzun kuma baze dauka ba.

Da daddare be koma gida ba se gurin sha daya sabodaya zauna meeting da wasu campany da zasuyi hadin guiwar wani aiki. A palour ya tarar da ita daman kuma ya tsammaci hakan maganar ba zata mutu ba kamar yanda hajiyar ta yanke hukuncin son rai dan haka yana ganinta ya qara hade fuska ya wuce ze shiga dakinsa tasha gabansa tana cewa

"Kai nake jira tun dazu dan gara ma ka sani bazan koma gidan nan ba idan baka rushe wannan gurin ka maida shi yanda yake ba" ta fada tana karkada qugu kamar Mazari, kallon sama da qasa yayi mata takaici ya rasa abinda ze fada mata seya zagaye ta ya wuce cikin dakin ta bishi cikin daga murya bata ko tunanin yara na bacci karta tasahe su tace
"Khalil dakai fa nake ka wuce ni wato ga mahaukaciya tana magana ko?"

"Ai sunan daya dace dake kenan Umaimah, na yarda baki da hankali kuma idan baki fita kin bani guri ba se ranki ya baci wallahi. Gida kuma karki koma, ke kika rasa gobe idan naga dama zan samo ukun ki na zuba a gidan kin kuma san yana da girman da ze dauke su dan haka ki fita ki bani guri ki koma ko karki koma keta shafa bani ba" Khalil ya fada yana kallon tsakiyar idonta kamar yanda itama ta zuba masa ido kafin ta juya da gudu tabar dakin nasa.

"Mtsw" yaja wani matsiyacin tsaki ya zauna a gefen gado yana dafe kansa da yake masa ciwo ciwo,Umaimah bazata canza hali ba, shekara dubu tana abin kirki idan tsiyarta ta juyo cikin minti daya zata wargaza komai. To wannan karon kam sedai abinta ya qare mata dan bashi da lokacin da ze tsaya yana batawa akanta abubuwan gabansa ma su Ishe shi.
Chapter 128 · 0% Book details