← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 168 OF 267

Sashe 168

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin gidan kuwa suna shiga palour Mama ta kalli Humaira dake kuka tana yarfe hannaye tace
"Yi mun shiru sakarya, idan wannan dan kurarin nata ya firgitaki ta ya zaki iya zama da ita a matsayin kishita kuma a cikin gida daya? Dole ki bude baki ki kuma cire duk wani tsoro da sokonci daga ranki ki kwatarwa kanki yanci dan daga sanda tasan kina tsoronta ta samu hanyar Azabtar dake".

"Ni wlh Mama bazan aure shi ba daman na gaya miki kece kika dage akan sena na amsa masa kin gani yanzu tun ma ba'ayi auran ba tazo tana cewa zata kasheni idan kuma aka kaini can daga ni se ita fa baki san abinda zata mun ba sedai kawai a kiraki ace kizo ki dauki gawata" Humaira ta fada tana sake rushewa da kukan tashin hankali. Tsaki Maman taja ta zauna akan kujera tayi shiru tana tunani, tabbas seta koyawa Umaimah hankali kuma zata tabbatar bata zageta a banza ba, setayi mata bazatan da zata girgiza har ta kusa rasa hankalinta. Ganin Humairan nata kuka yasa ta janyota jikinta ta shiga lallashinta.

"Kiyi shiru kinji auta karki bari maganganunta suyi tasiri a zuciyarki kishi ne yake damunta amma babu abinda zatayi mki. Kuma ma ai ba gida daya ze ajiye ku ba na sani kinga babu ruwan kowa da yar uwarta balle har wani abu ya hadaku ma kedai kawai kici gaba da Addu'a Allah ya tabbatar miki da Alkhairi tunda kina sonsa yana sonki ai magana ta qare babu ruwanki da wata matarsa" Maman ta fada tana shafa kanta seta dago da guntun Hawaye tace

"Nidai Mama na haqura ni daman ba wani sonsa nake ba gara na auri Noor dina na zauna ni kadai babu me daga mun hankali"
"Humaira kenan, shikenan tunda kince haka amma kina da tabbacin idan kin auri Noor din shima wata rana baze qaro miki wata irinta ba? Koma bashi ba duk Wanda kika aura dayan biyu ne ko ki tarar ko tazo ta tarar dake kuma baki sna Mijin ba ko ya zamana matar ce takr juyashi kinga wahala zaki sha. Wannan kuwa kin sanshi kin san komai nasa na tabbatar baze taba bari ta cutar dake ba kefa da kanki kike bani labarin Yanda Ibrahim yake riritaki da alqawarin da yake miki idan kunyi aure"

Saurin rufe ido tayi alamar kunya, duk hirar da sukayi seta bawa Maman labari dan haka ta koya mata ta dauke ta kamar qawa tana hira da ita a haka take sanin duk abinsa take ciki na daidai ta qara dorata akai na kuskure ta gyara mata.
"Toh kin gani shine kuma kike so ki bar mata ita kadai ta shanye duk soyayyar nan da akayi miki alqawariz ita kanta kishin da takeyi kenan bata so kizo kiji dadin da takeji a gidan shiyasa fa take wannan kururuwar ba wani abu ba so take ta tsorata ki ki bar mata mijinta ita kadai kuma duk mata haka sukeyi amma da anyi auran zaki ga ta saduda ta haqura tunda babu yanda zatayi".

Haka taci gaba da lallabata tana bata baki tareda qara mata qarfin guiwa tana bata misalai akan wasu mutanen sannan taja mata kunne akan koda wasa karta gayawa Khalil zancen zuwan Umaiman gidan. Sefmda ta saki ranta kafin ta fita ta gyara barin da tayi ta shiga hada musu wani sabon abin karin amma fa can qasan ranta cike yake fal da tsoron Umaiman. Bata son Hayaniya a rayuwarta ita bata iya fada ba sannan ace za'a hadata kishi da wannan matar da take cewa zata kasheta gaskiya bazata yarda ba kawai tayi shiru ne bata musawa Maman ba amma dole daga baya a san abinyi tana son rayuwarta bazata kai kanta Mahallaka tana sane ba.

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

Page 62

HUMAIRAH
Duk yanda taso ta gujewa Khalil din da auransa ya gagara saboda wata irin sabuwar kulawa da tattali da yakeyi mata suka rufe mata ido take jinbazata iya rabuwa dashi ba. Soyayya yake gwada mata irin wadda take mafarkin samu a gurin Noor dinta, kuma kamar yanda takejin ana fada idanka auri Yaro kafi samun soyayya sabanin babba da ze ringa ganin kamar bata lokaci ne sedai a yanzu da ta hadu da Khalil ta qaryata hakan. Kamar yanda Mama ta kwabeta da karta gaya masa zancen zuwan Umaimah gidan haka kuwa akayi bata gaya masa ba, shi ya ringa insisting akan ta yardar masa yaje can Jalingo ya gaida Dangin Mahaifinta dana Mahaifiyarta amma taqi saboda ita duk lissafinta fa babu maganar aure a yanzu, so take su ci gaba da soyayya kawai yana lallabata yana sangartata har zuwa ta shiga Jami'a ta gama Kafin sannan Noor dinta shima ya samu abinyi se suyi auransu dan fa bajin zata auri Mijin Umaimah ta kasheta a banza tayiwa Iyayrnta a sarar meyi musu Addu'a bayan ita kadai suka haifa.

Ranar da yamma suna zaune da Mama a tsakar gida suna shan iska saboda garin ya dauri da zafi gashi babu wuta, a kishingidr take suna chat da Khalil da ya tafi Anambra yana tsokanarta wai zeyo mata tsabar garin kwaki da kwakwar manja tana dariya Mama ta kalleta tace
"Wai ni dariyar me kikeyine tun dazu kamar wata tababbiya kina danna waya?'
Seda ta bashi amsa kafin ta tashi zaune sosai tana kallon Maman fuskarta da murmushi tace
"Nida Yah Khalil ne Mama, wai tsarabar Garin kwaki zeyi mun shine nace bana so".

"Kiji sokuwa aikensa kikayi da zece ze kawo miki abu kice bakyaso in banda rashin wayo aiko qasar garin tax and qullo a leda ya kawo miki godiya zaki masa ba kushewa ba. Ni da ace ma magana tayi qarfi ai inaga gidan Unaizatu zaki tafi ki zauna can tayi miki karatun aure da zama da kishiya dan da wannan salubancin naki kam wuya zakije kisha Mijin ma baki san yanda zaki tarairayeshi ki kula dashi ba balle azo ga batun kishiya" Mama ta fada tana kallonta, seta tura baki tace
"Nifa Mama ki dena mun fatan zama da wata kishiya, shiyasa ma da Yah Khalil din yake ta wani cewa zeje Jalingo nace masa ba yanzu ba, haka kawai ni jira nake Noor ya samu aiki kawai muyi auranmu bazan iya ba taje ta zauna da Mijinta ita kadai".

Kallonta Maman take harta kai qarshe kafin ta girgiza kai tayi kwafa kawai bata ce mata komai ba. Noor din da tun ran da wancan abun ya faru be sake zuwa gidan ba tana lura da ita kuma kullum ta kirashi baya dauka har takadda ta bawa Amir yaron maqontansu ya kai masa jiya tana zaune Humairan ta fita Islamiyya ya dawo da ita wai yaqi karba shine take lissafi akansa ko to zataci qaniyarta kuwa tunda ita ta hana Khalil din zuwa to da kanta ita zata bashi umarnin yaje ya nemi auran kawai dan ta qudurcr seta nunawa Umaimah ba ita kadai bace yar banza, kuma ita shirme takeyi da hauka aure da yardar ubangiji se anyi shi se dai in ta hadiyi zuciya ta mutu.

Washe garin ranar kuwa da dare sega Khalil yak gurin Humairan, da Maman suka fara gaisawa ba kuma tayi qasa a guiwa ba ta bude masa magana akan idan da gaske yakeyi tofa ya kamata manya su shiga ciki harta qara masa da cewar a can garin nasu akwai Yayan dangi da ake so ayi musu hadin zumunta da Humairan dan haka idan ya tsaya sanya ze iya rasawa da wannan maganar ya bar gidan yana fita ya shiga kiran Mansur da tunda maganar sa da Humairan ta fita ya shiga gaba dashi. Takanas ya kirashi ya gaya masa magana akan ya kyale musu qanwa baze aureta ba tun kuma daga wannan wayar idan ya kirashi ma baya dagawa dan ya gaya masa in dai ba ya janye ba tofa zasu samu matsala dan baze zuba ido a hada yarinya da Umaimah ta lahanta ta ba.

Gida ya wuce, dukda dare yayi dan goma ta wuce amma ya shiga bangaren Hajiyarsa. Habiba ya tarar a palour da Halima me aikinsu suna kallo ga Mu'ayyad na bacci a qasan carpet suka gashe shi gaba daya ya amsa yana tambayarta Hajiya fa tace tana daki jin haka yayi tunanin tayi bacci seya juya Habiba ta tareshi tana cewa
"Ba bacci take ba Yaya yanzu na kai mata shayi zata bawa Bibi idonsu biyu".
Juyawa yayi ya hau saman. A dakin ya samu Hajiyar ta gama bawa Bibi shayin harta kwanta ita kuma tana ninke kayan data cire da alama itama kwanciyar zatayi.

A kan one sitter dake dakin ya zauna yana sake gaisheta ta ajiye kayan hannunta ta zauna tana cewa
"Babana baka kwanta ba, da alama ma yanzu ka shigo gidan?"

Kansa ya shafa yace
"Eh wlh Hajiya naje gurin Humaira ne daga can kuma na tsaya wani guri s yanzu na shigo"
"Toh ya suke? Ya Hajiya Hauwan? Kaga inata zuci zucin na kirata tun ranar nan da mukayi magana Allah beyi ba ni da naji shiru daga bangarenka dana Matarka ma.na zata kun daidaita maganar ta wuce ne ashe kana kan bakanka" Hajiya ta fada seya dagao ya kalleta yace

"Wace magana kenan Hajiya?"
"Maganar auran naka mana tun waccan ranar bata sake tada maganar ba kuma naga ta shiga sabgoginta kamar babu abinda ya faru"

"Toh nima dai haka na gani kuma bata sake mun magana ba, dukda dai gaskiya nima tun waccen ranar ban sake tada mata da maganar ba yanzu ne dai nake so nayi mata saboda dazun da naje Mama tace mun ya kamata Nayi magana idan da gaske nake aje a samu iyayen Humairan abinda ya kawoni yanzu ma kenan na gaya miki saboda ki sanarwa dasu Baba Abu se su saka ranar da zasuje ayi shirye shirye kinga tafiyar da nisa".
Chapter 168 · 0% Book details