← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 159 OF 267

Sashe 159

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai fa Allah ya dawo da Nura se kuma abinda aka gani. Yanzu dai makaranta zaki fara dole ki tsayar da hankalinki idan ba haka ba kuma ya fito kawai a hada a kaiki ku qarata can, wannan soyayya taku se kace kanku a ka fara. Yanzu ina takaddar ranar yaushe zakiyi?" Mama ta tambayeta,, seta miqa mata takaddun dake hannunta tana cewa
"Jibin zanyi, mune farkon yi ma" Mama ta karba ta duba tana cewa
"Toh Allah ya bada sa'a. Se ki maida hankali kiyi karatu dan ka ganta nan tunda ta samu wayar nan babu sakat, aikin gida ma se anyi da gaske take tashi tayi bini bini suna hira da wannan yaron Nura daman abinda yasa Mansur yaqi bari a bata waya kenan toh kuwa inaga kwace ta zanyi har se sun gama jarabawar".

Shidai Khalil shiru kawai yayi yana hadiyar zuciya, Humairah ta wuce dakinta tareda Mu'ayyad shi kuwa Mama na tayi masa hira amma sam hankalinsa baya kanta tunanin waye wannan Nuran yakeyi ya dai gane shine yaron daya gansu tsaye to kuwa dole yayi maganinsa.
"Bari muje Mama, Magriba ta kawo kai zan tsaya kuma wani guri bayan nan" Khalil ya fada yana miqewa, se Mama ta kwalawa Humairah kira suka fito tana riqe da hannun Mu'ayyad kamar Yaya da qaninta, Mama tace
"Megida kazo ku tafi, ko zaka kwana anan"

Mu'ayyad dake shan chocolate ya maqe kafada alamar baze kwana ba Humaira tace
"Kai ba yanzu kace mun zaka zauna ka kwana ba tunda babu School?"
"Aa ni bazan kwana ba, sedai kizo mu tafi gidan mu".
Dariya Mama tayi tana cewa
"Ja'iri, wato sedai ta bika naku gidan ko ai shikenan, laifinka ne da baka kawo mana shi daya saba damu ai" ta maida maganar kan Khalil, yaqe kawai yayi dan tsayuwarsu a kusa ma damunsa take dan haka yayi gaba daya yiwa Maman Sallama. Humaira ta koma daki da sauri ta hado Alawoyi da biscuit wanda Noor ya kawo mata ta biyo su dashi. A bakin mota ta same su, ta miqawa Mu'ayyad tana murmushi tace
"Yah Khalil me yasa baku zo da qanwarsa ba? Yace su biyu ne ni ban santa ba".

Yanda take maganar fuskarta dauke da murmushi yasa ya zuba mata ido kawai yana kallonta wani abu na sake fizgarsa akanta, ganin yana nema ya shagala yasa ya bude motar ya shiga yana kallonta yace
"Qarfe nawa ne Exam din naki?"
"7am suka rubuta" ta bashi amsa seya gyada kao yace
"Zanzo na kaiki".

Baki ta bude kamar zatayi magana kuma se ta fasa tace
"Toh Allah ya kaimu ku gaida gida, Mu'ayyad bye" ta daga masa hannu kafinta juya ya bita da kallo saboda yanayin da tayi maganar ya nuna kamar bataji dadin cewar da yayi ze kaita ba.

Tana shiga gida ta zube akan kujera Mama ta kalleta ganin fuskarta ba kamar yanda ta fita ba tace
"Ke kuma lafiya kike hada fuska?"
"Mama wai Yah Khalil ne yace ze zo ya kaini rubuta Jamb, kuma ni munyi magama da Noor tare zamuje" ta yi maganar cikin shagwaba. Mama ta kama haba a ranta tana mamakin jin Khalil ze kaita a fili kuma tace
"To menene abin bacin rai dan yace z kaiki? A dadinki ai"

"Mama da Noor fa zamuje na gaya miki" ta sake fada se Maman tace
"Se ki gaya masa Yayanki ne ze kaiki ai".
Bubbuga qafa ta shigayi zatayiwa Maman shagawaba tace ta tashi ta bata guri. Tana shiga daki ta kira Noor ta sanar masa da abinda aka ce
"I'm sorry My Humy nima ina shigowa gida yanzun Hajiya take gaya mun zan kaita Gabasawa Ranar kuma da wuri zamu tafi, daman anjima nake shirin idan nazo na gaya miki" Noor din ya fada seta sake bata fuska amma bata ce komai ba. Lallashinta ya shigayi har seda ta sauko suka shiga hira kiran Dallar Magriba ne ya katse su daga nan ya gaya mata yana idar da sallar Isha ze zo sukayi sallama.

Humairan Noor kenan, kusan yan unguwar kaf da haka suke kiranta saboda irin so da shaquwar dake tsakaninsu babu wanda be sani ba. Noor Matashi ne dan kimanin shrkaru Ashirin da hudu, gidajr uku ne tsakanin gidan su dana su Noor din haka zalika tun suna Makarantar Primary suke tare dukda ba ajinsu saya ba soyayya ce tunta quruciya akeyinta har zuwa yanzu da suka kawo hankalin kansu dukda mutane da yawa suna ganin soyayyar tasu bata da matsaya da yawa suna ganin Humairan tayi masa girma a irin matakin da yake a yanzu da ko Makarantar gaba da Secondary be kai ga shiga ba dan ya dage akan aikin soja yake so yayi. Baya ga haka baya wata sana'a da za'ayi tunanin zata iya riqeshi har yayi aure kuma be fito daga wani babban gida ba da zasuyi masa auran gata iyayensa masu rufin Asiri ne kawai amma dashi da Humairan tasa sun yarda cewar suna son junansu a hakan kuma zasu jira har zuwa lokacin da burikansu zasu cika suyi aure akan hakan suke yanzu musamman da suka samu goyon baya daga Iyayensu Mata, Mama da Hajiya Asabe mahaifiyar Noor din sunyi Na'am da hadin dan qawayene sudin wasu daga cikin yayyensa da nata ne dai suke ganin batawa kansu lokaci kawai sukeyim dan yayyensa sun sha nuna masa akan ya rage irin zafin son da yake mata dan sun tabbata wata rana zata shammaceshi ta tafi ta auri wani, Macece ita babu yanda za'ayi ace ta jira Namiji amma yaceshi ba haka ba yasan ko nan da shekara dubu Humaira tasa ce kuma bazata iya barinsa ta auri wani ba abinda take fada mas akenan lullum.

Kamar yanda yayi alqawari ranar da zata rubuta Jamb qarfe shida da yan mintina a qofar gidansu Mansur tayi masa, be shiga ba a waya ya kirata kawai yace ta fito. Tana zaune gaban Mama tana shan shayin data takurata seta sha kafin ta tafin tana ganin kirankuwa ta miqe, Hijabinta ta zura dogo ta dauki qaramar Jakar data zuba abubuwan da za'a buqata tayiwa Mama sallama dake mata fatan nasara ta fita. Seda ta zauna cikin motar kafinta gaida shi ya amsa mata suka fara tafiya. Har suka isa inda zatayi jarabawar babu wanda yayi magana a cikinsu se sautin karatun daya kunna ne kadai ya karade motar. Seda ya tabbatar ayi mata screening ta hau layi kafin ya koma inda ya ajiye motarsa.

Ciki ya shiga ya kwantar da kujerar saboda yaji dadin hutawa kafin ta gama. Jakarta data bari a motar ya janyo ya ciro wayarta dake ciki. Hotonta dake kan screen dinya kalla tayi kyau tana sanye da Uniform din Islamiyya fuskarta dauke da murmushi. Bude wayar yayi yaga da key akai, zuciyarsa ta raya masa ya gwada sunan Saurayin nan nata da take sakawa a status yana rubuta Haskena kuwa wayar ta bude, yaja kwafa kai tsaye WhatsApp ya shiga amma ta rufe da Fingerprint seya ja tsaki rufe. Messages ya koma wannan Hasken ne kadai yaga suna musayar kalamai dashi daman babu wasu numbobi da yawa akan wayar duk na yan gidansu ne se qawayenta.

Qarar wayarsa ce ta tsayar dashi daga binciken da yake mata, ya janyo wayar daga Aljihunsa Umaimah ce. Bayan ya daga take tambayarsa ina ya tafi da sassafe ta farka baya nan,
"Wata Jana'iza na tafi, Baban wani Ma'aikacinmu ne ya rasu yanzu ana shirye shiryen kaishi ne da an gama zan dawo" Khalil ya shiryo mata qaryar dashi kansa besan sanda Idea tazo masa ba. Jajantawa tayi da Addu'ar Allah ya jiqan wanda ya mutu kafin sukayi sallama seya kashe wayar gaba daya ya ajiyeta. Kwanciyarsa ya gyara ya rufe idanunsa yana tunanin abinda zuciyarsa take ayyana masa yayi ko kar yayi yana cikin haka bacci ya daukeshi.

Besan iya Adadin lokacin daya kwashe yana baccin ba kwankwasa Glass din da akeyi ya farkar dashi. Humaira ce, ya cire lock din motar kafin ya gyara kujerar da yake kai ya tashi zaune. Bakinta a washe ta shigo motar ya kalleta yace
"Har kun gama kenan"
"Mun gama kuma tayi sauqi sosai wlh" ta bashi amsa tana duba jakarta.
"Allah ya bada sa'a" ya fada kafin ya tada motar seta kalle shi ganin bata ga wayarta a jakar ba, shima kallonta yayi yace
"Yaya dai?"
"Waya ta ce bangani ba kuma na taho da ita" ta bashi amsa. Da ido ya nuna mata Aljihun motar taja ta bude sega wayar ta dakko, satar kallonsa tayi dan tana budewa a kan Gallery ta tarar. Hotunanta na shirme ta shiga dubawa a ranta tana addu'ar Allah yasa be bude ba da kuwa tasha kunya Khalil dake ankare da ita yayi murmushi a zuciyarsa kawai.

Wani gurin cin abinci taga ya tsaya, ya kalleta bayan ya kashe motar yace
"Muje kiyi breakfast"
"Na qoshi, seda na sha Tea kafin na fito daga gida" ta bashi amsa. Fita yayi ya barta be jima ba ya dawo da Ledoji masu tambarin gurin a jiki ya saka a bayan motar kafin ya shiga suka ci gana da tafiya.
"Wanene Noor?" Ya jefa mata tambayar dake ta cin zuciyarsa. Humaira dake danna waya ta dago da sauri ta kalleshi ganin shima itan yake kallo yasa ta sadda kai kamar munafuka qirjinta na bugawa saboda wani abu da taji ya tsarga mata saboda irin kallon fa yayi mata.

"Uhm na tambayeki kinyi shiru" ya sake mata magana seta qara sunkuyar da kai tace
"Abokinane" dan haka kawai taji ba zata iya ce masa saurayinta bane, karya mammaketa irin na Yaya Mansur da yace tayi qanqanta da fara kula samari shekara sha bakwai.
"Aboki, shine naga kina saka hotunansa kullum kina rubuta haskenki?" Ya sake jefa mata wata tambayar seta kalleshi kamar zatayi kuka tace
"Toh ai fassarar sunansa ce haka, Noor ba Haskenan ba?" Ta qarasa da sigar Tambaya.
Chapter 159 · 0% Book details