← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 267

Sashe 14

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani turaren hayaqi ya debo ya zuba ya bata ta ajiye a gaban Umaiman data zura musu ido tana kallon ikon Allah jin hayaqin yasa ta kauda kai, matar ta janyo fuskarta ta dawo da ita saitin Hayaqin, Umaimah ta fara zuga Atishawa saboda sam bata shiri da hayaqi, Mama dake gefe ji tayi kanta ya fara mata wani Yuummm dan daman tunda ta shafa mata maganin nan warinsa yake damunta, miqewa tayi tace "Alhaji bari naje daga waje hayaqin nan ya dameni" ta fice baranda inda iska take kadawa ai kuwa Umaimah bata san sanda ta fashe da dariya ba har seda Abba yai saurin matsawa dan abin yazo masa a bazata.

A ranta tace "Allah shi qara, idanni baa tayar mun da Aljanu ba ai gashi nan zaa tsokalo miki naki"

"Allah gafarta Malam sunzo ko?" abba ya fada yana raba ido dan fa shi yana da tsoron Aljanu daman, murmushi Malam yayi yace
"Aa, shaqiyanci ne irin na dan yau baka gani ba da mahaifiyarta take saboda hayaqin ya koreta kar nata na gado su motsa"

"Allah ya rufa asiri" Abba ya fada ya sake rabewa gefe. Har hayaqi yaci ya cinye dai babu Aljanun Umaimah babu dalilinsu, Matar ya umarta da ta sakeyi mata karatun, ta zauna a gabanta ta kama babban dan yatsan hannunta kafin ta fara mata karatu a kunne nan ma dai shiru ba labari.

"Gaskiya Alhaji sabo duk wani ilimi da dabara da nake dashi akan al'amarin nan na gwada ka gani kuma, yarinyar nan bata da shafi ko rabar jinnu a tare da ita. Sedai idan wata matsala ta daban ce take damunta da tayi kamanceceniya da matsalar Iska" Malam ya fada yana duban Abba, shima ya gamsu da hakan dan haka ya gyara zama yana cewa

"Toh Allah gafarta malam, a yanda mahaifiyarta take fada abin nata yawanci yana tashi ne dalilin Kishi, tana da tsananin Kishi kaga karo uku kenan ana fasa auranta kuma duk ita take jawowa da baqin HALIN KISHIN ta, shin ko akwai wasu Aljanu da suke saka mutum ya zama me tsananin Kishi haka??"

"Murmushi Malam yayi kafin yace " Shi Kishi halittace Alhaji Sabo kuma ko wanne dan Adam yana dashi sedai na wani yafi na wani zafi, ko kuma wani yafi wani sanin yanda ze sarrafa kishin nasa. A yanayinta tana da zafin zuciya da saurin fushi, kuma kaga su wadannan siffofine da basu da kyau, sam fushi bashi da kyau. A duk sanda mutum yayi fushi, idan ba anyi dace ba yana iya aikata abinda daga baya zezo yana dana saninsa shi yasa da wani mutum ya taba zuwa gurin Manzon Allah SAW yace yayi masa Nasiha se Annabi yace masa 'kada kayi fushi' ya maimaita masa hakan har sau uku.

Bayan haka akwai hanyoyi da dama da mutum zebi gurin ganin ya kare kansa daga fadawa dana sani dalilin fushin zuciya shine ta hanyar lazimtar ambaton Allah, a duk sanda kaji zuciya ta yunquro maka tana raya maka aikata abinda yake ba daidai ba kayi qoqari gurin kama Ambaton Allah, kayi hailala kayi Istigfari kayi tayi har se kaji wannan Fushin ya sauka.

Bayan haka abu na biyu shine yin shiru a duk sanda kake cikin Fushin, idan kasan bude bakinka a lokacin fushi baze sa ka furta a khairi ba to kayi shiru ka kama salati

Na uku shine nisantar duk abinda ze jawo motsuwar Fushinka, idan gurine kake zuwa ake bata maka rai to ka nisance shi, idan wani mutum ne ko wasu mutane suke tunzura ka zuwa ga fushin toh ka rabu dasu hakan shi yafi zama Alkhairi a gare ka, idan ma wani abu ne kake yi duk ka dena se kaga mutum ya zauna lafiya a rayuwar sa.

Ke kuma yata maganar kishi kiyi qoqari ki sassautawa kanki, mace ce ke wata rana gidan wani zakije ba kuma ki da tabbacin ke kadai zaki zauna dashi a rayuwarki. Baya ga haka a koda yaushe ki tuna cewar Allah ne ya halastawa maza damar ajiye mace sama da daya dan haka ba wani abu bane ba kuma abin da zesa ki daga hankalinki bane kama ta yayi ki ringa Addu'ar koda Allah ze kawo miki abokiyar zama ya baki wadda zaku zauna lafiya, amma wannan mugun kishin baze haife miki Da me ido ba dan bama ko wanne Namiji ne zeyi sha'awar auranki ba saboda gudun abinda ka iya faruwa a gaba".

"Saboda kalamsa basuyi mata bama sam hana kanta fahimtarsu tayi ta hanyar tafiya dogon tunanin, seda Abba ya kira sunanta da qarfi kafin tayi firgigit ta farka, malam ya hada mata yan magunguna na tsari da baki ya bata itama Mama aka bata wasu kafin sukayiwa Malam sallama suka kama hanya.

"Yanzu Alhaji meyw abinyi, tubda matsalar nan bata Iska bace inaga fa toh sedai asibiti ko abin a kwakwalwarta yake" Mama ta fada cikin Jimami, Umaimah dake bayan mota ta tunzura baki, daga iskoki kuma yanzu Tabin hankali ake yayibo mata? To ai shikenan aje duk inda za'aje kudinsu ne zeyi ciwo tunda dai ita tasan lafiyarta qalau.

"Gaskiya Hajiya Babu inda zan sake zuwa kuma, kindai ji abinda Malam ya fada ita zatawa kanta fada ruwanta ta sakawa zuciyarta salama ruwanta taci gaba da abi da takeyi mudai Allah ya gani iyayi munyi namu zagi kuma da take jawo mana ita ta sani" Abban ya fada a fusace maganar Malam ta babu me auranta tana dawo masa, kwarai gaskiya ya fada dan duk wanda yayi aure yayi ne dan ya samu cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankali, waye ze siyi tashin hankali da kudinsa ya kai gida? Duk ma wanda yazo yaga halinta doke ya gudu ai su kansu dan babu ya da suka iya da ita ne sun kuma karbi hakan a matsayin tasu Jarabawar.

"Haba Alhaji ka dena fadar haka, gatan da zamu mata kenan a yanzu mu tabbatar da lafiyarta saboda nidai wadannan abubuwan da takeyi ban dauke su a mutum me cikakken hankali ba, kaga yanzu idan Asibiti suka tabbatar da lafiyar kwakwalwarta daga nan zamu san matakin da zamu dauka akan ta tu da munsan zallar iskanci ne abinda takeyi" Mama ta sake fada cikin kwantar da murya.

Yi yai kamar bazeje ba sedai meya tuna ya zaro wayarsa ya kira wata lamba, bayan sun gaisa a taqaice ya tambayi mutumin yana gida ne ko Asibiti kamin ya kashe ya mayar da ita Aljihu. A lokacin har sun kusa isa gida ya karkata kan mota suka qara gaba, a zaton Mama zasuje Asibitin Malam ne ko Murtala se gani tayi Abban ya dauki hanyar Dawanau.

"Alhaji Dawanau zamu je ne?" Ta fada tana kallonsa, se ya juyo a fusace yace
"Can zamuje Malika, ko akwai inda suke da kwararrun likitocin manya da qananan mahaukata ne banda can din? Ki fa rabu dani idan ba haka ba tam" ya buga sitiyari, shiru Mama tayi dan da alama ran maza ya baci, shi kansa zafin ran na Umaimah ai daga gurinsa ta gado kawai dai nata ya zarce nasa ne amma shima ai ba baya bane a yanzu ne da shekaru suka ja ya rage wa kansa hayanjya da fada saboda hawan jini ammada akan qanqanin abu be qi ya wuni yana fada da mita ba.

Tsuru Umaimah tayi a bayan mota, Dawanau fa yanzu haka zaa kaita a daura mata injinan da ake saka mahaukata karfa a garin neman gira a lalubo mata haukan da bata dashi. Kamar tace kar aje amma tasan yanda Abban ya hasala beqi ya tsaida mota ya lallasa ta suji gaba da tafiya ba, tana ji tana gani suka isa Asibitin da tundaha haraba ha kalinta ya fara tashi ganin masu lalurar rangwamen Hankali kala kala an fito dasu suna ta hidimominsu. Harta hango kanta ance zaa ajiyeta anan, ai bata san sanda ta ruqunqumo mama ta baya ba ta zabura tace

"Subhanallahi jikin ne Alhaji kaga ni ko daga zuwa abu ze kuma rikicewa". Tsabatmr takaici ko kallonsu Abban beba har ya qarasa yayi parking motarsa a bakin Clinic din. A dardar suka fito suka bi bayanshi da alama yasan gurin suka ringa ratsa mutane suna wucewa abinda ya dan kwantarwa da Umaimah hankali kenan ganin mutane fes fes masu lafiya babu alamar wata lalurar hauka a taredasu, dagaske dai da akace ba Asibitin mahaukata bane, duk wani me lalura data shafi Kai ko kwakwalwa yana zuwa tana wannan tunanin har suka isa qofar wani office Abban ya kwankwasa.

Kamar ana jiransu daman aka bude, Babban Mutum dan kadan ne bazasuyi Sa'anni da Abbaba ya miqe ya tare shi ya bashi hannu da gani akwai kyakykyawar Alaqa a tsanin su.

"Mukhtar Mukhtar ashe ana ganin ku daman" Likitan ya sake fada fuska dauke da Murmushi bayan da suka gaisa da Mama, Mukhtar da taji ya kira ya tabbatar mata da Abokinsa na quruciya ne da sukayi makaranta tare ne.

"Wallahi fa Dr Kabiru haduwa tayi wuya, rabona da kai fa tun Daurin auran yar gidan Faruk Saleh daga nanaka ce ka bar qasar, se kwananan muka sake jiyo ka" Abban ya fada shima.

"Toh ya zaayi, rayuwar se a hankali, zumunchi yayi qaranci, amma lafiya kuwa na ganka tareda Madam da yarinyata, daka kirani fa na zata kawai tsohuwar Aminta ce ta motsa yau zaka kawo mun ziyara"

Umaimah Abban ya nuna masa lokaci daya bacin rai na taso masa yace"Ga tanan Dr, duk wani gwaji da akeyi a gane lafiyar kwakwalwar mutum ayi mata. Acaje ta tsaf ta yanda zan san abinyi a gaba".

"Subhanallahi ta samu Accident ne ko me" Dr ya fada yana miqewa tsaye, kan Umaimah ya dafa ya shiga duba kwayar idonta yana sake cewa

"Ina referral letter da file dinta muga menene matsalar?"

"Ba accident tayi ba, abubuwa take yi irin na masu tabin hankali kuma mun kaita Ruqiyya ance na Aljanu bane shiyasa nace bari na kawo ta nan".

Dariya Dr Kabiru yayi kafin ya koma kujerar sa yana cewa "Haba Mukhtar wani irin abu takeyi haka da har kake zaton tana da matsala a kwakwalwa?"
Chapter 14 · 0% Book details