← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 267

Sashe 28

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana kwance a daki saboda gajiya da tsokanar da masu shigowa kallon lefe suke mata wayarta dake gefe ta dauki qara, tasan wanene saboda shi kadai ta sakawa wannan kidan, cike da doki da shauqi tareda kewar sa da duk suka taso mata lokaci daya ta daga wayar da sallama kamar wata ta Allah.

Daga dayan bangaren Khalil ya saki ajiyar zuciya saboda yanda muryarta ta ratsashi amma saboda karya bada kansa se yayi gyaran murya a dake ya amsa mata sallamar tareda dorawa da tambayarta ya take

"Ba lafiya ba Khalil, na kusa mutuwa da yanzu sedai kaji wani ya dauki wayar nan ba ni ba" ta qarasa tareda fashewa da kukan da tasan yana karya masa zuciya ai kuwa tayi nasara dan nan da nan ya rikice ya shiga lallashinta, batayi shiru ba seda tayi me isarta taji sanyi a ranta sannan ta fara magana cikin sheshsheqa

"Nifa ba dagaske nake ba duk abinda na fada maka wallahi bacin raine ya saka amma kayi fushi ka dena kirana idan na kiraka ma baka dauka ko naji wayar a kashe har kwanciya nayi a asibiti kwana uku ban mayi zaton zan rayu ba"

"To yanzu dai ai baki mutu ba koh gaki da sauranki" ya bata amsa, seta bata fuska kamar tana gabansa dan sam yanda yake magana ba irin yanda suka saba a baya bane da alama har yanzu da wani abun a ransa, be haqura gaba daya ba kenan.

"Haka ma zakace, da na mutun ai se kafi kowa shiga damuwa tunda kaine kayi silar mutuwata" ta fada tana tura baki, murmushin da beyi niyya ba yayi yace

"Ko a mafarki kikaga me kama dani ya cutar dake ki tabbata shedan ne yake so ya shiga tsakanin mu dan in har ina numfashi bazan taba bari wani abu mara kyau ya same ki ba".

Wani sanyi taji har ranta dan Khalil dinta ya fara dawowa, seta gyara kwanciya tace
"Nayi kewarka sosai, you have no idea yanda kwanakin nan suka kasance mun ba tareda kai ba, dagaske Khalil idan na rasa ka zan iya rasa raina...."

"Umaimah, rayuwa da mutuwa duk na Allah ne dan haka kik dena cewa idan babu ni bazaki rayu ba, kafin nan Umaimah ina son magana dake, ina so mu zauna akwai maganganun da nake so mu tattauna masu muhimmanci" Khalil ya katseta, daga yanda yayi maganar ta fahimci da gaske yake dan haka itama ta tattara nutsuwarta tace

"Daman yau zan biyo Maman Asad idan zata taho gida, da baka kirani da sedai kawai Hajiya taga baquwar da babu sanarwa kaga shikenan idan nazo se mu hadu a gidanta hakan yayi?"

"Yayi, yanzu zan taso daga Dutse, zuwa bayan sallar Isha idan Allah ya kaimu zan ganki" ya fada daga daya bangaren, jin yana qoqarin kashe wayar yasa Umaimah saurin tare shi da cewa

"Kashewa zakayi, bazaka bari muyi magana ba?"

"Umaimah na gaya miki zan hau hanya ne i see you in the evening alright?" Ya fada sounding pissed off

"Shikenan, Allah ya tsare hanya ya kawo ka lafiya" ta fada a sanyaye saboda yanayin da yayi maganar qarshen yasa taji babu dadi. Haka ta ajiye wayar amma ko babu komai kiran da yayi mata ta ji sanyi a ranta ta kuma tabbatar da sanin sa ake ci gaba da shirin auransu.

Tashi tayi ta bude wardrobe dinta ta shiga neman kayan da zata saka anjiman dan gaba daya dogayen rigunan material ta diba da hijabai tunda tayi shirin zuwa wasan kwaikwayo ne, yanzu kuwa da aka samu change of plan dole ta dibi kayan kwalliya.

Kala biyu masu kyau ta diba da mahadin su tana murmushi ta zuba a cikin jaka, koma wace magana ce tasan dai bazata wuce ta shirin biki da abinda zasuyi ba, ita kuwa bata da ra'ayin yin komai daze halarta ballantana yammata su gane mata shi.

Ganin Yaya Hajiyayye ta shantake ta azalzaleta akan ta tashi su tafi, qarshe da taga zata bata mata lokaci ma gaba tayi ta hau adaidaita dan tana so taje ta dan samar masa wani abin tabawa  ta kuma shirya a nutse kafin lokacin da zasu hadu.

Ana idar da sallar Magriba ta hau shiri dan tana zuwa me delivery ya kawo saqon cup cakes da Yaya Hajiyayyen tayo order daga *MCubes bakery* (08134606093) bayan data ci na dazu da safe ta gigice da dadi nan da nan ta saka order wa Baban Asad da yayi tafiya ze dawo washe gari da safe.

Umaimah na karba ta bude ta samu bowl me kyau ta zubawa Khalil, ga Pepper chicken da ta bata tayo musu gaba dashi ta dumama a microwave shima ta ajiye samman ta hada da ruwa da lemo masu sanyi komai yayi mata daidai ta shiga shirya kanta.
Doguwar rigar Atamfa ta saka A line data yi matuqar yi mata kyau ta kafa dauri a gaban goshi ita da kanta tayiwa kanta kyau, turarukan Yaya Hajiyayye sun ci qaniyarsu dan feshin banza ta fadi tayi musu bayanta gama ta shiga daukar hotuna tana canhar bata san an idar da sallah ba saboda tana fashin ta ne ita.

Sallamar me gadi ce ta katse mata daukar hoton, ta leqa suka gaisa yace tana da baqo a waje, seta dafe qirji shaf ta manta ta zare Sim din daga babbar waya ta saka a qarama dazu kafin ta fito daga gida ta maye shi da data Sim, fuskarta ta sake gyarawa ta fito, tana hangoshi ta narke fuska ta sake ragewa tafiyarta sauri kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta qarasa inda ya tsaya ya harde hannu biyu a qirji yana qare mata kallo.

Khalil
Tun fitowarta ya zuba mata ido yana jin yanda sonta yake qara huda zuciyarsa yana shiga, tayi masa kyau, yanda take qara narke fuska kamar wata qaramar yarinya ba qaramin tafiya yayi da shu ba har besan sandata qaraso ba seda ta tafa hannayenta a fuskarsa, a shagwabe tace

"Wannan kallon fa? Qiris ya rage ka saka na fadi".

Murmushinsa me kyau ya sakar mata kafin yace
"Kinyi kyau", fari tayi da ido itama tace
"Kaima kayi kyau" ta bashi amsa suka saki murmushi gaba daya kafin tayi gaba ya take mata baya zuwa inda kujeru suje ajiye a tsakar gidan.

"Bari na kawo maka ruwa" ta fada tana juyawa ya rakata da ido harta bacewa ganinsa a ransa yana hasaso irin asarar da zeyi idanya rasata, amma idanya tuno wannan dayan side dinnata gaba daya se yaji komai yana juya masa. Yana can tunani yaji qarar ajiye try akan table dake gabansu, ta bude ruwan ta tsiyaya a glass cup ta miqa masa ya karba da murmushu yace
"Thank you".

Seda ya shanye ruwan ya miqa mata ta qara masa ya shanye ya ajiye cup din yana kallonta yace

"Umaimah, kin shirya aure na dagaske?"

PROMO
PROMO
PROMO

BEFORE 4K NOW 2500

3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
KITURA SHEDAR BIYA 👇🏻

08162859027

AUNTY ZEE MOM MUJAHID KATSINA

INGANTACCEN MAGANIN SANYI MAI WANKO DUK DATTIN MARA CIWON MARA CIWON JIKI HANA HAIHUWA RASHIN NI IMA RASHIN JIN SHA AWA FITAR FARIN RUWA KAIKAYI KURAJEN PP DA NA JIKI JIN ZAFI YAYIN SADUWA FITAR FARIN RUWA MAI WARI BASUR KOMAI DADEWARSHI CIWON NONO

SHIRYE NAKE ZANYI MAKU PROMO SABODA WA ANDA BASU SHA BA SU ZO SU DA DANA MAGANIN AUNTY ZEE MOM MUJAHID DUK LABARIN DA AKE BAKU GASKENA MAGANINA KANKAT NE KOBAKISHA KOMAI BA YA ISHEKI
*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

PAGE 14

Kallon rashin fahimta ta bishi dashi kafin tace
"Kamar yaya na shirya auranka da gaske, daman ana auran wasa ne?"

Gajeran murmushi Khalil yayi tareda gyara zamansa ya tattara hankalinsa gaba daya a kanta ya zuba mata ido, dole tayi qasa da nata idanun saboda yanda yayi mata kwarjini ta shiga juya zoben Azurfar dake hannunta a ranta tana so ta gano ma'anar tambayar da yayi mata wai ta shirya auransa, to me Khalil yake shiryawa ne?

"Tambayarki nayi kuma amsa nake da buqata taqaitacciya Eh ko Aa, Umaimah kin shirya aure na?" ya fada still idonsa akanta, seta dago tayi masa kallo daya kafin ta juyar da fuskarta dayan gefen tace
"Eh"
"Good, kinsan me Aure yake nufi?" Ya sake jefa mata wata tambayar har sannan yana kallonta, seta juyo itama ta kalleshi, harara taso maka masa amma yanda ya tsare gida dole yasa ta saita idonta ta bige da qiftasu kamar an jijjiga bera a jarka kafin ta bude baki tace

"Wai me yasa kake mun irin wannan tambayoyin ni ban...."
"Umaimah! Ba wasa ya kawo ni ba, magana nake so muyi kuma dole ki amsa mun duk tambayoyin da nayi miki kai tsaye ba na son wata magana ko nuqu nuqu" yayi saurin katseta, seda ta watsa masa harar qasan ido kafin tace

"Aure ibadah ce da Mace da Namiji suke zama a qarqashin inuwa daya matsayin mata da miji dan su bautawa Allah kuma su zama ababen debe kewa ga junansu".

"Menene matsayin Namiji a cikin aure?" Ya sake jefa mata wata tambayar,
"Guy din nan fa ya raina mun hankali ji wasu tambaya kamar dan jarida" Umaimah ta fada a ranta, a fili kuwa tace

"Namiji shine shugaba wanda haqqin ci, sha, sutura, muhalli, neman lafiya da biyan buqatar matarsa ya rataya a wuyansa"

"Ita kuma mace fa" Khalil ya sake fada yana bin bakinta da kallo, yanda take bayanin tana murguda bakin ba qaramin birgeshi yake ba. A'uziyya yake taja lodi lodi a zuciyarsa saboda yanda shedan yake sake qawata masa bakin nata.

"Ita mace Allah ya wajabta mata yiwa mijinta biyayya akan duk wani abu da be sabawa Mahalicci ba saboda Aljannarta ta koma qasan qafarsa daga sanda tabar gaban iyayenta. Sannan dole ta girmamashi, babu musu ko jayayya a tsakaninsu, ta kuma mutunta Iyayensa da yan uwansa sannan zata kula dashi tayi tattalin dukiyarsa data qunshi Arziqi na Yaya da kudi" Muryar Umaimah ta dawo dashi daga tunanin daya tafi.

Kai ya jinjina ya dan tabe baki kafin yace "se kuma me?"
Chapter 28 · 0% Book details