← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 255 OF 267

Sashe 255

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikin Hadiza yayi sanyi da jin maganar Umaiman, sun rabu da Khalil kenan take nufi meya faru?"
"Ki yafe mun Hadiza" Umaiman ta sake fada cikin tsananin kuka. Hajiya Huda da tayi shiru tana kallon Dramar tasu ta sauke numfashi tace
"Ya isa Umaimah ki dena kukan haka, Hadiza meya hadaki da ita haka da take kuka tana neman gafararki?"
Se Umaimah ta sunkuyar da kai ba tareda ta dena kukan ba wata irin kunya da nauyi sukayi mata rubdugu. Idan Hajiya Huda taji labarinta tabbas duk wani girma da mutuntawa da ake mata a ma'aikatar ya qare daga yau zasu ringa mata kallon mara mutunchi da bata tsoron Allah amma hakan ya fiye mata idanhar Hadiza zata yafe mata a shirye take data sake yin Video ta roqi yafiyarta kamar na wancan karon.

Hadiza kuwa murmushi tayi tana kallon Yar uwar Mijin nata tace
"Babu komai Anty Huda, can an dade mun taba samun sabani da ita amma ya wuce a gurina kuma tun a lokacin mantawa tayi amma na fada mata na yafe har gaban Allah babu komai a raina" seta koma kan Umaimah tana cewa
"Wallahi na dade da yafe muku Umaimah tun a wancan lokacin banida wani abu dana riqe akanki amma naji kince kin rasa Khalil, kardai Rasuwa yayi ban sani ba?"

"Khalil be rasu ba Hadiza amma bama tare kusan shekara shida kenan ya sakeni" Umaimah ta bata amsa tana sunkuyar da kai qasa se office din yayi shiru na wani lokaci kafin Hadiza ta sauke numfashi tace
"Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi a rayuwarku gaba daya".
Umaimah dake kuka har sannan ta daga kai ta kalleta tace
"Harda haqqinki da yake bibiyata ki yafe mun dan Allah"

"Umaimah, na gaya miki nifa ban riqeki da komai ba amma dai tunda so kike na sake fada kiji na Yafe miki Umaimah na yafe miki abinda kikayi mun Allah ya yafe mana gaba daya".

Ajiyar zuciya me qarfi ta sauke tana jin nauyin zuciyarta na raguwa. Hajiya Huda ta miqe da kanta ta dakko ruwa me sanyi ta miqa mata a sanyaye tana cewa
"Kisha seki shiga ki wanke fuskarki tunda tace ta yafe kukan ya isa haka".
Ta karbi ruwan tasha kamar yanda tace ta shiga bandakin dake cikin office din, Hajiya Huda ta kalli Hadiza data sunkuyar dakai, maganar rabuwar Umaimah da Khalil din ta tabata seta dafa kafadarta tana cewa
"Madallah da kyakykyawar zuciya irin taki Hadiza, Ubangiji yana son masu yafiya Allah ya yafe miki kurakurenki kema kamar yanda kika saka sharri da Alkhairi, ubangiji yaci gaba da dabaibayeki da Ahalinki da Albarka mara yankewa, dan uwana yayi sa'ar mata"

Hadiza tayi murmushi daidai nan Umaimah ta fito ta wanke fuskar amma har sannan bata dena hawayeba tana jan majina, Hajiya Huda ta nuna mata kujera tana cewa
"Zauna a nan har se kin dena kukan zaki fita, ba zaki ja a fara tuhumar me akayi miki ba ina tace ta yafe to kukan ai ya isa haka ko" kamar tace ta qara kuwa ta sake fashewa da wani kukan. Auna qirman laifin da tayiwa Hadizan takeyi a zuciyarta wai duk ina tunaninta yake tafiya a baya idan zata aikata mugun Abu? Khausar da Rufaida sun cuceta, su sukayi mata ingiza me kantu akan Hadizan, wannan be zamar mata darasi ba ta sake janyo Safina rayuwarta gashi yanzu ta tarwatsa komai ya lalace ta rasa komai da take taqama dashi. A ranar se Hajiya Hudace ta maidata gida dakanta saboda irin kukan data ringayi harya haifar mata da ciwon kai me tsanani. Seda ta kwana biyu tana jinya kafin ta koma aiki ta kuma yi maruqar qoqari gurin danne duk wata damuwa ta cigaba da walwalarta.

KHALIL

*HALIN KISHI*

*NA MARYAM FAROUK*
*(UMMU-MAHEER)*

*FIKRA WRITERS ASSOCIATON*
*(DON CIGABAN ADABIN HAUSA)*

Page 87

BAYAN SHEKARA DAYA

A hankali kamar wadda akayiwa kiran yan zawarawa suka fara kawo mata caffa. Idan ta fita bata dawowa gida ba tareda wani ya taya ba saboda yanzun Alhamdulillahi ta murmure, jikinta ya fara dawowa dukda bata maida cikarta irin tada ba amma tayi kyau fatarta ta goge musamman da yanzu take daukar Albashi tana kula da kanta ta siyi mayuka masu kyau dan har Supplement Maman Asad ta sakata dole ta siya masu gyara fata bana qarin wata halitta ta jiki ba ya kuwa karbeta ya bude mata ciki ta ringa cin abinci sosai kuma me gina jiki nan da nan se gata ta dawo hayyacinta tayi tas shiyasa duk idan ta gifta Mazan basa iya dauke kai akanta amma a bangarenta ta shata musu layi, babu Wanda ta bawa dama duk irin yanda Yan uwanta suke mata magana akan bafa zata zauna haka ba, gara ta sako ranta ta bawa wani dama su daidaita dan mutunchin Mace gidan auranta.

Anty Hafsa ma da take zaune tayi aure tuni, daman ita tace saboda Yaranta Mata take zaune duk manemanta idan ta kawo musu zancen da yaranta zata zauna se su zame ita kuma tace ba zata barsu hannun dangin Mahaifinsu ba dan basu nuna musu zumunchi ba, tunda ya rasu aka rana gado suka karbi rabonsu kowa ya zame ya barta da wahalar Yayan nata hudu da suke duk Mata. Tashi daya Allah ya aurar mata da uku, babbar ta gama Jami'a, me binta tana level 3 se ta ukun ta shiga kenan duk suka samu Miji Mama tace babu abinda za'a jira haka aka hada da Sharifan Anty da itama ta gama makarantar tuntuni se sannan ta samu Mijin aka sha biki. Auran yaran da wata uku ita ma ta daura nata da wani tsohon Abokin Baban yaran shima matarsa ta mutu shikenan ta tare da sauran yarta data rage ta hada da nasa ta riqe masa.

Auran Anty Hafsa yasa suka taso Umaiman itama a gaba. Dole badan tana ra'ayi ba ta fara barin maneman nata suzo gida saboda Mitar Mama ma kadai ta isheta sedai kuma wata sabuwar jarabawa data bullo mata duk wanda yayi zuwa daya gidan baya dawowa sedai su shiga yi mata wasa da hankali a waya da son cewar su hadu a wani gurin, wasu ma daga haka se zancen banza ya shigo ciki duk wanda kuwa ya kawo mata zancen banza zagewa take tayi masa tijara dan ba wai tayi sanyi ne gaba daya ba daman rayuwa ce kawai ta bida ita.

Mama ta sakota a gaba da cewar ita take korarsu da baqin halinta. Sassauci da rahamar data samu a gurinta ta fara ja baya suka koma yar gidan jiya fada kyara da hantara kullum ta dira mata mitar taqi fitar da Miji tunda ba maneman ne bata dasu ba korarsu takeyi.
"Nasan me kikeyiwa qulafucin komawa gidan Khalil kikeyi to tun wuri Idan zaki cire ranki akan sa ma ki cire dan baze maidake ba, ke idan kina da kunya ma in aka ce ki koma se ki yarda? Ki kalli Hajiya Aisha da wane idon bayan dibar Albarkar da kikayi mata? To idan ma zaki fiddashi a ranki tun wuri dan rigada ya miki nisa, tazarar ku tamkar ta sama da qasa ne. Yana can yana rayuwarsa cikin jindadi da kwanciyar hankali tareda matarsa da take sonsa take girmama mahaifiyarsa shekara bakwai kenan kina zaune idan da ze waiwayeki da tuni ya nuna alamu dan haka gara tun wuri ki samu wani ya rufa miki asiri ya aureki dan ke kam a yanzu sedai kiyi auran rufin asiri" haka Maman take yaba mata magana duk kuwa sanda ta fada mata haka ranar wuni zatayi tana kuka.

Amma ta yarda da ita datace Khalil baze waiwayeta ba. Yaranta suna yawan kiranta da wayarsa musamman Bibi, sau da yawa suna tare dashi tana jin muryarsa yana hira cike da nishadi amma koda wasa be taba gaisawa da ita ba ita ma kuma tayi namijin qoqari gurin riqe kanta bata tambayar yaran shi haka indai ba su suka kira ba bata kiran layin nasa, daga bayane ma da zuciyarta ta gaza, tana ganin idanhar bata nemi yafiyarsa ba bazata qarasa samun cikakkiyar nutsuwa ba se ta ringa tura masa da Text message na ban haquri amma ko sau daya be taba maida mata da amsa ba haka ko ya kawo yara sun hadu be taba yi mata kallon wata halitta da zaman aure ya taba hadasu ba balle har tasa ran ganin soyayyarta a kwayar idonsa. Idan ta gwada kiran layinsa ma baya shiga sedai idan yaran ne suka kira da kansu tasan kuma shiya saka lambar tata a wani tsarin ta yanda bazata same shin ba, seta koma canza layuka dukda hakan batayi nasara ba dan baya dauka, daman tun Asali ta sani da wuya ya amsa baquwar number in dai ba me ita yayi masa saqo ya fadi wanene shi ba, dan haka kota kira baya dagawa. Daga baya ma har wayar Mama take dauka ta kirashi, tayi haka kusan sau uku duk be daga ba sedai daga baya ko da daddare zataji suna waya da Maman alamar se sannan ya samu sukunin kira kenan akan hakan Mama tayi mata tatas data gane ita ce take kiransa da wayar, ta ringa mata gori da Tijara kai ba zakace ita ta haifeta ba, irin wadannan abubuwan kadai sun isa su sanar mata da matsayinta a gurin Khalil yanzu dan haka dole taja jikinta ta kuma karbi qaddara a yanda tazo mata koma meya faru itace sila, ita ta siya da kudinta. Data haqura ta zauna dashi kamar yanda yasha fada mata ta sani babu wata Mace da zata zo ta zarce ta matsayi a gurinsa seta biyewa kururuwar shaidan ya kaita ya baro gashi ta qare a nadama da dana sani mara amfani.
Chapter 255 · 0% Book details