← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 267

Sashe 41

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar ta dakko Allah ya taimaketa bata fashe ba bata bata lokaci ba ta goge chats din tsaf bayan ta shiga gallery ta goge hotuna da videos din data bude kafin ta koma ta fice daga group din yanzu ace Khalil ya dauki wayar yaga wannan aika aikar wane kallo zeyi mata ita ko da wane baki zata fara masa bayani?

"Allah kayi mana maganin masifa da bala'i su kuma masu yin wadannan rubuce rubucen da tura video ka shirye su" ta fada a fili tana rafka tagumi. Abin ya daure mata kai da yawa daman tun suna makaranta Nabila tana cikin ire iren wadannan groups din na matan aure wani lokacin haka za'a turo rubututtuka akan sirrin kwanciyar aure ko makamantansu harda ma video a lokacin suyi ta mata fada sai tace wai gara ta koya ta san komai kafin lokacinta wanda ita dai a iya saninta ta san wannan ilimine da bashi da malami ko baka sani ba da zarar lokacinka yayi ka shiga Ajinsa zaka sani amma shine wasu marasa tsoron Allah suke fakewa da fadakarwa suna yada badala a cikin Al'umma suna lalata yaran mutane dan da yawan matan da suke taruwa a groups din da sunan Matan aure qananan yara wanda basu kai matakin ace sun san wannan abin da wata babbar banzar take zama tana koya musu ba Allah dai ya rufa asiri ya ganar da masu ganewa.

Wannan abun ya sakata ajiye wayar ta shiga aikin gida jiki a sabule har aka kira La'asar bata gama goge goge ba. Se gurin qarfe biyar ta samu ta kintsa gidan, ta shiga wanka kenan ta jiyo horn din motar Khalil gabanta ya bada ras shaf ta manta da ya gaya mata da wuri ze dawo tayi abincin rana dashi nan da nan ta shiga tunanin qaryar da zata shirga masa, haka tayi wankan tayi ta fito tana lankwashewa ido zuru zuru kamar mara lafiya ta jingina da bango tana jan numfashi daidai danda Khalil din ya shiga dakin da sallama.

"Lafiya Babe meya sameki?" Ya fada yana qarasawa kusa da ita ya ruqota jikinsa.
"Subhanallahi ya naji jikinki da dumi zazzabi kikeyi?" Ya sake fada yana taba fatar jikinta data kwararawa ruwan zafi dukda zafin da akeyi a garin, daman tayi ne saboda ya dauka zazzabin takeyi.

"Tunda ka tafi kaina yake ciwo dakyar na iya tashi nayi aikin gida ma na sake kwanciya se yanzu na yi wanka kuma naji zazzabi yana neman rufeni" ta fada tana matso kwallar qarya.
Gaba daya yabi ya rikice ya zaunar da ita a gefen gado se faman sannu yake mata tana ita kuwa tana qara lankwashe wa.

"Bari na dakko miki kaya muje asibiti ko ga jikin nan da zafi" ya fada yana bude wardrobe dinta, seta sake marairaice masa, kar aje Asibiti suce babu abinda yake damunta dan haka tace
"Aa kabarshi nasan zuwa anjima ze dena daman kwana biyun nan haka nake yi idan ka fita zan tajin babu dadi yamma nayi kuma zan warke"

"Yanzu baki da lafiya shine zakiyi shiru baki fada mun ba har kwana nawa? Bana so karki sake yimun wasa da lafiyarki, duk idan kikaji ba daidai ba ki gaya mun muje Asibiti karki sake zama da ciwo a jikinki" Khalil ya fada cikin bacin rai, shiru tayi daga neman hanyar kare kai ta sake kunno wata matsalar.
Ba yanda ta iya ya tasata a gaba suka wuce asibiti yana ta mata mitar qin gaya masa bata da lafiya da batayi ba ya kuma jaddada mata idan sunje duk abinda yake damunta ta gayawa likita, kamar ta gaya masa gaskiya itafa lafiyarta qalau shiririta ta zauna bata yi aikin gida da wuri ba shi yasa ta masa qarya amma dai tayi shiru dan a yanda ya hasalan nan bata san yanda zasu kwashe ba kuma.

Kai tsaye wani private Asibiti me kyau ya kaita, babu bata lokaci aka bude mata file kafin suka zauna jiran ganin likitan dan sun tarar da mutum biyu a gabansu. Da suka shiga gurin likitan ya tambayeta me yake damunta shiru tayi seda Khalil din ya zazzare mata ido kafin ta yanko qarya tace kanta da cikinta ne suke ciwo se jiri wannan kuma da gaske kusan sati daya kenan ko a zaune setaji kamar jiri na dibanta, data gayawa Mama se tace mata ta ringa yawan shan ruwa kuma ta ringa hutawa da tayin kuma ta samu sauqi amma yanzu tunda an qureta duk ta harhada qarya da gaskiya tace suna damunta.

Tambayarta yayi yaushe tayi Al'ada na qarshe ta gaya mata se a sannan ta tuna ya kamata ace tun satin daya wuce ma jinin ze dawo mata amma bezo ba, da yake wani lokacin yana mata delay shiyasa ma bata damu ba amma dai be taba qara har sati daya ba.

Test din jini dana fitsari likitan ya basu bayan daya auna jininta ya dudduba idonta suka wuce gurin biyan kudi daga nan ya rakata qofar lab din ta shiga shi kuma ya tsaya daga waje aka dauki jininta suka bata robar da zatayo fitsari a ciki tayi ta mayar musu kafin suka koma can inda ake zama ayi jira.
Suna zama aka kira Sallar Magriba Khalil ya wuce masallacin Asibitin ya barta yana tashi ta zaro wayarta dake cikin Aljihub doguwar rigarta ta shiga WhatsApp.

Da saqon Rufaida ta fara cin karo
"Wannan mata ko mayya ce se haka ta haihun ma bazata zauna ta huta ba seta addabi rayuwata da takura haba" Umaimah ta fada a fili kafin ta bude saqon tambayarta take me yasa ta fita daga group tace mata babu komai groups din ne sun mata yawa. Daga nan take gaya mata qarfe goma na dare zata gabatar da ita a Qasaitacciyar Mace group din dan haka sukeyi, idan sabon Member ya shigo ze gabatar da kansa saboda kowa ya sanshi daga nan ya zama dan gida dan haka ta zauna online kafin lokacin.

Cigaba da duba saqonnin mutane tayi seda ta hango Khalil tayi sauri ta kashe Data ta jefa wayar a Aljihu, yana qarasowa aka miqo musu Test result din kai tsaye suka koma office din likita ya karba ya duba fuskar sa dauke da murmushi ya miqawa Khalil hannu yana cewa
"Ina tayaka murna madam nada shigar ciki".

Daga ita har shi bude baki sukayi suna kallonsa da mamaki, cikin tabbatarwa yace
"Kuna mamaki ne? Gashi nan abinda sakamako ya nuna kenan, yanzu zaku dawo nan da Two weeks zaku dawo ayi scanning musan cikin sati nawane" ya hau rubutu a takadda ya basu yace su karbi maganin a pharmacy kafin ya qara musu da shawarwarin yanda zata kula da kanta da abinda yake cikinta.

Khalil da Umaimah dai se yar kallo kallo ake bakin nan kamar ya tsage dan tsakanin su bazakace ga wanda yafi wani farin ciki ba, 'ikon Allah daga qaryar cuta ashe silar jin abin arziqine' Umaimah ta raya a ranta haka suka dauki hanyar gida bayandaya tsaya yayi musu take awayn abinci da kayan kwalama, duk abinda ya gani a hanya seya tambayeta zata ci abin nasa ma tun yana bata dariya har ta fara jin haushi.

Da suka isa gidan ma hanata fita yayi daga motar, kamar wata yar baby haka ya dauketa ya kaita kan kujera ya ajiye yana cewa
"Kina ji dai likita yace a kula dake dakyau banda aikin wahala, dan haka duk wani aiki me yawa a gidan nan na sauke miki shi, kiyi wanda zaki iya ki bar sauran idan na dawo zan ringayi.

A daren nan taga tarairaya da ririta ta kuma shaida yanda Khalil yake son haihuwa dan harya fara lissafin abubuwan da zasu siya da sunan da za'a sakawa Babyn idan Macece ko Namiji.
"Nidai nafison Namiji" Umaimah ta fada tayi daidai akan cinyarsa yana bata Ayaba a baki bayan da suka gama cin abinci.

"Ni kuwa koma menene indai Mutum ne kika haifa ina so" Khalil ya bata amsa yana jan hancinta kafin ya qara cewa

"Wai, yanzu fa hancin nan nan da kwana kadan ze bude ya zama qato naga haka hancin su Jalila yakeyi idan suna da ciki duk su fita a kamanninsu, bari ma na kirata na gaya mata su shirya samun sabon baby a family" ya qarasa yana janyo wayarsa dake gefensu, hade rai tayi tace

"Kawai kuma seka wani fara kiran mutane kana gaya musu ai ka bari dai muji ma kwanakin cikin kafin a fara yayatawa".

Daga yanda tayi maganar yasan halin tsiyar ne ze motsa dan haka ya bata rai shima yace
"Eh na yayata din yan uwana zan gayawa kema ban hana ki kira naki ki gaya musu ba" ya fada yana danna kiran layin Jalila babu dadewa ta daga tana cewa

"Dan qanina kamar kasan yanzu nake so na kiraka kwana biyu dai Amarya ta kwace mana kai baka neman mu muma bama samun ka"

"Ba haka bane wallahi kin san na koma aiki idan na fita bana samun zama dana dawo kuma kashe wayar nakeyi saboda masu damuna, amma zan ware layi daban dai inaga" ya fada cikin jin kunya dan dagaske ya yada su, kai hatta Hajiyarsa seda tayi qorafin rashin zuwansa gidan kamar farkon auransa da kullum idanbeje da safe ba zeje da yamma yanzu kuwa seya jera kwana biyu uku be leqa su ba sedai ya kirata a waya shima tace Umaimah tafi kiransa akanta dan kullum ta Allah ne seta kirata sun gaisa da safe.

"Toh ai shikenan daman lafiya ce ai take buya, yanzu ya akayi ta samu ne naga kira da tsohon daren nan" Jalilan ta sakw fada,
"Albishir na kira nayi miki kin kusa yin sabon baby, Amarya nada ciki" ya fada yana shafa kai dan wata yar kunya kunya yaji na neman kamashi.

Cikin muryar farin ciki Jalilan tace "Ah kace dan qanina ya girma no wonder ka buya ashe kai kasan aikin da kakeyi irin wannan sharp sharp haka? Ta bari na shiga group yanzu na shelanta musu a saka sabon adashi matar Usaini tayi ciki, ka gayawa Hajiya ko na gaya mata?" ta qarasa cikin dariyar shaqiyanci.
Chapter 41 · 0% Book details