← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 267

Sashe 69

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsaf Hajiya ta gama jinta bata kama zancenta ba saboda sanin matsayar da suke da ita dan har a sannan bata haqura ba tana mata nacin in da hali Khalil ya qara da Badariyyan shiyasa yanzu ma ta dauka duk cikin sharrin tane daman tunda ta damu da suje din tayi tunanib wani abu. Suna gama wayar Khalifa ta kira lokacin ya ajiye Umaimah kenan take tambayarsa meya faru a gidan Goggon tasu tax be sani ba danshi daya gaji waje ya koma ya zauna amma yaga ta fito ranta a bace ya tambayeta bata kulashi ba ya ajiyeta gashi nan a hanyar gida yanzu yana hanyar dawowa.

Maida akalar kiran tayi kan Umaimah, seda wayar ta qaraci qararta tana daf da katsewa sannan ta daga cikin muryar kuka.

UMAIMAH
Tana zaune tana saqa da warwara taga kiran Hajiyar, zuciyarta ta ayyana mata karta daga, wani bangaren kuma yace mata ta daga ta daddana mata Ashar ai duk bakinsu daya ai. Rasa wanne zatayi a ciki tayi har seda taji wayar na neman katsewa kafin ta daga cikin muryar kuka ta amsa sallamar Hajiyan.

"Umaimah lafiya meya faru a gidan Zara'u? Ta kirana tana gaya mun wadansu maganganu da ban ganewa kansu ba sannan na tambayi Khalifa yace be san komai ba" Hajiyan ta fada cikij muryar damuwa musamman yanayin kukan da taji kamar Umaiman nayi.

Kuka Umaimah ta fashe dashi kamar yanda zuciyarta ta kitsa mata ta fara cewa
"Hajiya wacece wadda kika tura mu gidanta, haka kawai da farko baki ga yanda ta karbe mu ba faran faran muka gaisa amma tana ganin Khalifa ya fita ta canzamun fuska ta shiga zagina tana zagin iyayena, bata gaji ba Hajiya ta gayyato wata mata itama tazo suka hadu har tana cemun mayya wai na cinye muku zuciya keda Khalil ya zabeni ya bar yar uwarsa to wallahi ban isa ba se taga bayana, in saka ido in gani seta rabani da Khalil" ta qarasa tana fashewa da kuka.

Salati Hajiya ta ringayi kamar zatayi kukan itama ta ringa bawa Umaimah haquri amma kamar wadda take tunzurawa se qara rusa kuka take tana cewa
"Babban abinda ya fi mun ciwo hajiya har fa cewa takeyi Khalil ya gurbata muku zuri'a ya auro mayya gashi nan na haifi maye wai mu'ayyad ya zura mata ido yana kallonta duk abinda ya sameta bazata yarda ba" seta sake rushewa da kuka.

Ran Hajiya ya baci tace
"Ki kwantar da hankalinki in sha Allahu babu abinda ze faru se Alkhairi, maita kuma data dora miki seba bi miki kadinki ki barni da ita" haka ta ringa lallashinta ita kuwa se sake rura wutar take ta hanyar fadar maganganun qarya akan Goggon ta jefeta dasu da haka sukayi sallama.

Wasa wasa qaranar magana ta zama babba dan korar ne lalle Umaimah tayi tace bazatayi ba ta kuma rantse akan bazata koma gidan Khalil ba an tanbayeta meya faru tayi shiru se kuka takeyi da suka gaji suka qyaleta.

Washe gari Khalil ya dawo, kansa a qulle saboda maganganun da Hajiya ta gaya masa da wanda Badariyya da Mahaifiyarta suka kira suka gaya masa ya rasa wanene me gaskiya a ciki? Haka kawai zuciyarsa tafi gasgata zancen Badariyyah musamman da tun a daren yake neman layin Umaimah yana shiga amma bata dagawa.

Kai tsaye gidansa ya wuce dan duk tunaninsa ya bashi ta koma sedai yana zuwa ya tarar da qofa a rufe, da muqullin hannunsa yayi amfani ya bude qofar ya shiga, gidan tsaf an gyara ko ina dakinsa ya wuce ya ajiye kayan daya shigo dasu ya fada wanka dan ya kwaso gajiya a mota sukayi tafiyar kuma shi yayi tuqin. Seda ya shirya sannan ya wuce gidan Hajiyarsa, a can yaci abinci tana sake maida masa zancen abinda ya faru cikin bacin rai bece mata komai ba se haquri daya bata ya ci abinci ya wuce gidan su Umaimah.

Tana kwance akan gado Saufullahi ya shiga yace tazo inji Mama, doguwar rigar Atamfa ce a jikinta ta mayar da hular data zame daga kanta tabi bayansa, tun daga qofar palour take jiyo qamshin turarensa seta sake tamke fuskarta ta shiga sa sallama ciki ciki.
Yana zaune akan kujera da Mu'ayyad a hannunsa ta samu kujerar bakin qofar ta dofana tana masa sannu da zuwa, fuska babu yabo babu fallasa ya amsa mata hankalinsa na kan yaronsa, abin ya bata mata rai ta sake tunzura baki gaba, bece mata komai ba yana ci gaba da yiwa Mu'ayyad wasa Mama ta shigo tana kallonta tace

Kije ki nunawa su Nazifi kayan da zasu fitar miki dasu ku wuce dare yanayi"
"Nifa Mama na gaya miki babu inda zanje, yaje can ya auro yar uwar tasa su zauna tare" Umaimah ta fada tana tunzura baki se suka kalleta gaba daya, a zuciyaraa yana sake samun tabbacin abinda aka ce ta aikata dagaske tayi shine ta zagaye ta karantawa Hajiya qarya da gaskiya ta sakata ciwa Goggo Zara'u mutunchi har abin ya nemi ya zama rigima seda Baffansu ya tsawatar shine yanzu nan zata nemi ta caja masa kai ko.

"Banason iskanci Umaimah, ki wuce ki hada kayanki nace miki idan ba so kike ranki ya baci ba" Mamanta fada murya babu wasa se Umaimah ta miqe tana cewa
"Wallahi Mama dagaske nakeyi bazan koma gidansa ba, seyaje ya auro duk wadda yaga dama" tana gama fadan haka ta miqe ta bar dakin.
*SUMAYYAS_HERBAL_APHRODISIACS*

*Shin yar uwa kina da wata matsala ce data shafi zamantakewar aure da kika kasa gane kanta? Ko kuwa a bangaren megida ne Al'amura basa tafiyar miki daidai yanda kike so*

*Qaiqayin gaba, farin ruwa ko ruwa me qarni yana fitar miki kinje Asibiti kinsha magani har yanzu ba'a dace ba? Ko kuwa kin kasa gane kan mu'amalar auratayya bakyajin dadi ko kina jin zafi a lokacin saduwa*
*Aa damuwarki inda zaki samu ingantattun magungunan mata marasa illah wadanda masana ilimin suka hada ba yan taka haye to ki garzayo nan domin muna da maganin matsalolinki da yardar Allah*

*A Sumayyas_herbal_aprodiasics* *muna bada ingantattun magunguna wadanda masana sukayi bincike suka tabbatar da suna samar da waraka ga dukkan matsalolin da kuka zo dasu*
*Muna da maganin sanyi ko wanne iri da yardar Allah zamu baki bayan munyi miki tambayoyi domin sanin yanayin lakurarki*
*A bangaren kayan gyara muna da ingantattun tsumi, Gumba, Kaza/ciccibi, Sabaya na gyaran Nono, maganin qiba dana rage qiba ingantattu da babu kwaya a cikinsu*
*Sannan munada tsari na tattaunawa da mata domib musan matsalolinku mu kuma baku shawarar yanda zaku magance su da yardar Allah*
*Adreshin mu Zaria/Abuja muna kuma aika kaya ko ina a fadin qasarnan cikin Amincin Allah kutuntube mu akan*
*07031876677*
Ko a IG *sumayyas_herbal_aphrodisiacs*

*HALIN KISHI*
*NA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WANNAN LITTAFIN KUDINE, KI TURA DA 500 ZUWA ASUSUN*

*8142548705*
*OPAY DIGITAL SERVICE*
*MARYAM UMAR FAROUK*
*SAI A TURA SHAIDAR BIYA ZUWA GA 07061838488*
*A BIYA A KARANTA CIKIN SALAMA* 🙌🏼🙌🏼

PAGE 31

Juyawa Mama tayi da niyyar binta Khalil ya dakatar da ita da cewa
"Ki barta Mama yanzu tana cikin bacin rai idan ta sakko dan kanta seta dawo" ya miqe tareda kwantar da Mu'ayyad akan kujerar yayi mata sallama ya fita, dakin da Umaimah take ciki ya shiga tana tsaye a jikin window tana dakon ganin wucewarsa daman ta waiwayo da sauri tana cewa

"Na gaya maka bazan koma ba, harni za'a tura gidan su budurwarka su wukaqantani, daman kuna tare har yanzu qarya kayi mun da kace kun rabu toh Allah ya tona maka asiri na sani kuma zama dakai na gama sedai kaje ka aurota ragowar wasu can ka qarata da ita".

Cikin bacin rai ya kalleta yace
"Karki sake aibata ta dan jinina ce bazan iya canzata ba sabanin ke da zan iya rabuwa dake, sannan ita wadda kikaje kika yiwa rashin kunyar qanwar mahaifina ce uwa daya uba daya har kika iya tsayawa a gabanta kika zageta idan da kinsan darajar babba kome zatayi miki ai bazaki tanka ba taci albarkaci na amma shikenan kici gaba da duk abinda kikeyi akwai ranar da zaki kwashe kashinki a hannu. Zama kuma kiyi ta zama gaki ga gidan nan har sanda kika gaji" Yana gama fadar haka ya fice daga dakin cikin bacin rai ya bar gidan a ransa ya qudurce shekara dari daga yanzu baze sake waiwayarta ba, duk abinda ta yanke a wannan gabar akansa ze tafi. Saboda bacin rai be iya komawa gida ba gari ya shiga ya ringa yawo abinda be iya ba ga wutar sha'awarta dake damunsa sabida ya gama saka ran a ranar zata dawo, har wasu hadi Abokinsa ya bashi acan sokoton yasha danma bacin ran da yake ciki ya danne kaso hamsin na buqatar da yake ciki amma duk da haka yana cikin wani yanayi.

Gajiya yayi da yawo ya samu wani gurin shaqatawa ya zauna, daga gefe can yana hango yammata da yawa sunsha anko kamar dai wani shagalin biki suke gabatarwa a gurin dan yaga wata da tafi yin kwalliya kamar Amarya. Yana zaune a gurin har suka gama suka fara watsewa hankalinsa yayi nisa a tunani yaji sallama a kusa dashi. Firgigit yayi ya kalli masu sallamar, yammatane guda biyu suna sanye da kalar Ankon daya gani suka gaishe shi ya amsa yana kallonsu da rashin sani.

Wadda tafi kalar rawar kai a ciki tace
"Sannu Malam kayi haquri mun dameka ko dan Allah taimako muke nema"
"Toh, taimako kamar na me kenan?" Ya fada yana kallonsu a ransa yana tunanin me ze taimaka musu dashi.
Chapter 69 · 0% Book details