Sashe 134
Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kunce ta tayi taja drawer ta saka a ranta tana mitar Safina ai seda tace sihiri ne tace mata ba haka ba to kuwa sauran abubuwan ma data ce zaa kawo mata bata so dan bata san wace jarabar suke qullawa a ciki ba. Dukda ta cire din dai seda suka kwashi kusan kwana uku a haka dukda dai ya rage amma fa be koma kamar daba ga ciki ga takurar sa gaba daya ta rasa nutsuwarta haka dai suka ci gaba da lallabawa ta kira Safina ta qare mata tanadi tas ta ce kuma bazata biya kudinba, Safina ta ringa dariya tana cewa
"Au daga gwaninta ai bansan ke shar kike ba bakida matsala da wancan fannin shiyasa ashe wannan ba harkar ki bace, to wlh haka kuwa zakiyi ta haquri se randa Mayen turaren jiki ya bar jikinki sannan zaki samu sa'ida dan ni kaina idan ta kwana biyu daman cirewa nake na ajiye in yayi sanyi na mayar"
"Shegen turare kamar na yan bori aikuwa Dilka zanje a mun tas a goge shi" Umaimah ta fada Safina ta ringa mata dariya wannan dalilin yasa zancen Zahra ya bar zuciyarta na dan lokaci kafin abubuwa su qara rikicewa.
Da safiyar Talata cikin sauri sauri suke shiri dan tare zasu fita gaba daya a sauke Mu'ayyad a makaranta kafin itama ya sauketa gidan Maman Asad data haihu jiya da daddare se ya wuce gurin aiki. Ba yanda beyi da ita ba akan ta bari gari ya qara waye wa sannan ta tafi amma qarfe bakwai tajewa mutane gida kaman tashin hankali amma tayi biris, baya son jan magana ya sa ya rabu da ita, Bibi ko wanka batayi mata ba ta tasata a gaba bayan ta dibar mata kaya suka fice daga gidan, seda aka fara aje Mu'ayyad kafin ya dauki hanyar gidan Maman Asad din da su yanata Mita ita dai bata tanka shi ba kuma tunda ta niyyata se taje.
A waje ya tsaya, Bibi ta sauka da Jakar goyonta da aka zubo mata kaya Umaimah na mayar da takalmanta data cire saboda qafarta da ta dan tasa wayar Khalil dake tsakiyarsu ta shiga qara. 'Zahra S' ta gani, ta dago ta kalle shi yanda ya zabura ya dauke wayar ya qara qona mata rai me ze boye to bayan ta gani? A fusace ta bude murfin motar ta fice ko jakarta bata tsaya dauka ba ya bita a bayabda jakar wani yaro ya bawa yace ya kai mata kafin ya koma mota yana jin wayarsa daya saka a Aljihu nata faman qara.
Seda yaci rabin tafiya office kafin ya tsaya ya dauki wayar da kamar mayya har sannan bata gaji ta dena kira ba. A fusace yace
"Wai Zahra wace irin yarinya ce ke me nacin bala'i, da kika kira sau daya ban dauka ba base ki haqura ba ai kinsan idan na gani zan biyo ki ko? Wai ma akan me zaki kirana da safiyar nan bayan kinsan ta yuwu matata tana kusa dani?"
Daga can bangaren Zahra cikin ko in kula da banbamin da yakeyi tace
"Tun jiya kace zaka kirani har nayi bacci baka kiraba, da Asuba na kiraka wayarka a kashe ni kuma na kasa samun nutsuwa banji muryarka ba shi yasa nake ta kira"
"To ai seki zuba ruwa a qasa kisha hankalinki ya kwanta kin hadamun rigima a gida, ke bari kiji daga yau ma karki Sake kirana idan ni naga dama zan kiraki haba duk kibi ki addabi mutum ba dare babu rana ke ko dan jan ajin nan na mata ma baki dashi haba, nin yanzu na fita aiki, karki sake kirana ki bari idan na samu free time zan kiraki dan Allah" Khalil ya katseta yana gama fadar haka ya kashe wayar yana sauke numfashi, wannan kwarzaba ta Zahra ta ishe shi Allah ya kawo masa lokaci Contract din nan ta tabbata kowa ya kama gabansa dan wallahi babu yanda ze iya da wannan yarinya me shegen nacin jaraba sedai Dr Sabitu yayi haquri.
Motarsa ya tayar yaci gaba da tafiya, ba'a ko ci minti biyar tsakanin wayarsu da Zahra ba wani kiran ya shigo masa, gabansa ya fadi ganin Me kiran, Dr Sabitu Bashir seya gangara gefe ya kashe motar jikinsa har rawa yake ya daga wayar cikin ladabi yana cewa
"Barka da Asuba Dady"
"Riqe gaisuwarka Injiniya, wato har kayi kaurin wuyan da zaka saka mun yarinya kuka da safiyar nan ko? To bari kaji wallahi ko ka kira Zahra ka bata haquri ka lallabata ko yanzun nan kira saya zanyi a kwace kwangilar nan daga hannunka a bawa wasu. Kasan dai akwai wadanda suka fika cancanta na shiga na fita aka baka saboda to karka manta da yarjejeniyar da take tsakanin mu kuma duk wani shirme da zakayi ka tabbatar kana rage chances na tabbatuwar kwangikar ka ne, foolish boy kawai" Dr Sabitu ya fada cikin saurin bakin sa wanda a maganganun gaba daya kwangila da Zahra kaai Khalil ya iya tattarawa ya fahimci abinda yake nufi.
Wallahi bada ban wuyar daya sha gurin tsara paper work da sauran abubuwan da yayi akan aikin nan ba da saki zeyi ya haqura, ina dalili? Shin tun farko ma waya kaishi shiga wannan bala'in da yayi haquri idan rabonsa ce kwangikar nan yana kwance zata same shi. Gaba daya Anwar Saleh ne yaja masa, Abokinsa ne tare sukayi karatu kuma yanzu yana aiki a Companynsa shi ya fara kwadaita masa Zancen kwangilar wanda tunda ya gaya masa a lokacin yace baze iya shiga ba dan Kwangila ce ta dubunnan miliyoyin kudi yasan babu yanda za'ayi ma ayi considering qaramin company irin nasu. Anwar ne ya ringa pushing akan suje su nema ai abin na Allah ne baya ga haka ai shima yayi ayyuka da yawa manya a Company daya bari kuma mutane da yawa sun sanshi dan haka kar yaji komai suje suyi Addu'a qila sa'ar tasu ce haka ko akayi suka shirya takaddun tsare tsare da budget da komai Anwar yaje yayi submitting se gashi cikin ikon Allah an kirasu cikin Kamfani goma na sama da a ciki za'a zabi wanda zaayi awarding aikin.
Anwar be haqura ba seda ya binciko masu fada aji a Ministry da za'ayi aikin a ciki ya gano Dr Sabitu Bashir daya daga cikin Directors din gurin yace ya sanshi abokin Uncle dinsa ne ze roqi Uncle din ya hadasu dashi haka kuwa akayi cikin Sa'a se gashi sun samu appointment da Dr Sabitu ya basu lokaci yace suje gida su same shi.
Sun samu Dr Sabitu a gida ya tarbe su da fara'a saboda akwai kyakykywar alaqa tsakaninsa da Uncle din Anwar. Sun gabatar masa da abinda ya kaisu ya karbi Blueprint din da sukaje dashi ya duba kai tsaye babu kwana kwana ya gaya musu suyi haquri bazasu samu wannan kwangila ba dan akwai manya manyan kamfanunuwa da suka shafe su yamayi mamakin yanda akayi suka fito a Top Ten dan kamfanin nasu dako cikakkiyar shekara beyi da kafuwa ba amma hakan na nuni da idan an samu kwangila daidai dasu za'a neme su kenan haka suka tattara suka tafi gida jiki a sanyaye.
Sati daya tsakani Anwar ya same akan Dr Sabitu ya kira shi yace yana son ganinsu haka suka dunguma suka tafu bayan sunje suka same shi yasa aka kira masa yarsa suna zaune wata zuqeqiyar yarinya me kyan sura dukda ba fara bace tas ta shigo palour, jikin Dr ta tafi ta lafe kamar mage ba tareda ta ko kalli bangaren da suke zaune ba.
"Kalle su ki gani Daughter wanne ne a cikinsu?" Dr ya fada yana shafa kanta seta dago da sauri ta kalli inda baban nata yake nuna mata dan sam bata ma lura da mutane a gurin ba karaf idonta ya sauka cikin na Khalil, baki ta washe kamar wata wawuya ta nuna shi tana cewa
"Wannan ne Daddy".
Khalil da Anwar suka kalli juna cikin rashin fahimtar abinda yake faruwa. Dr dake dariya shima kamar yar tasa ya shafa kanta yana cewa
"Oh My daughter Allah ya shiryaki, to tashi ki koma ciki kinji" seta noqe kafada kamar wata yarinya Dr ko ya sake washe baki yana cewa
"Idan mun gama zan saka a kiraki kinji maza kije kiyi wanka kiyi kwalliya kafin nan" se a sannan ta miqe ta fice fuskarta kamar gonar Auduga tana aikawa da Khalil wani kallo da ya kasa tantance na menene.
"Zahra baby kenan, tun ranar da kuka zo gidannan yarinyar nan ta shiga wani hali bata da aiki se kuka da damuwa qarshe ko abinci se munyi dagaske take iya ci kuma taqi fada mana damuwarta sam se jiya dana matsa mata sannan take sanar mun da a cikin baqin da suka zo gidannan ne ta kamu da son wani, bayan ta fada mun ranar ne nayi tunanin wadanda na gana dasu ya zama ku biyu nan ne ze Aminina Alhaji Zakari dalilin daya saka na kirawo ku kenan dan ta tantance wannan ne ne a cikinku kuma kunji, kai Khalil kaine kayi mun fashin zuciyar yarinya daga zuwa neman kwangila" ya qarasa cikin barkwanci.
Kallon Anwar Khalil yayi lokaci daya yaji ransa ya baci, daya ce Dr Sabitu na neman su ya dauka wata kwangilar ce ta samu a she wani zancen shashanci ne kawai ya saka ya kirasu, to shi yayi me da wannan sangartacciyar yarinyar da kana ganinta kasan bata qoshi da tarbiyya ba? Taba shi Anwar yayi ganin yayi nisa a tunani dan sam be ma san Dr na magana ba
"Yanzu dai kunji dalilin kiran, zaku iya tafiya idan yaso ka jirata a waje tazo ku gaisa daga nan se ku musayar lamba ko amma kafin nan zan ja maka kunne, kaga Zahra ita kadaice yata mace.
Ina bala'in sonta yanda baka tsammani kuma zan iyayin komai akanta dan haka ka lallabamun ita dan badan ita tace tana sonka bama kai baka kai ajin da zan baka auran Zahra ba".