← Book details Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 198 OF 267

Sashe 198

Halin Kishi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Khalil ciwon ido kakeyi?" Ta fada tana miqewa tsaye seya daga mata kai still be kalleta ba yace
"I think Apolo ne ya kamani daman Anwar yana yi may be gurinsa na dauka"
"Kai Allah ya sauwaqe gara ma daka saka Glass kar mu dauka muma musammani da idona yake kwalamamme kar na tashi dashi gobe" ta fada tana ja baya kamar wanda yace mata ya gamu da cutar kuturta shidai Sama ya nufa yana riqe da numfashinsa dan ba qaramar qundumbala yayi kafin ya shigo gidan ba. Babban abinda ya bashi qarfin guiwar dawowa tabbacin da Jamila ta bashi akan Lafiya lau gidan yake babu abinda ya faru har suka tafi kai Lefe, kuma ta tabbatar masa da cewar Mama tazo, to meya faru dayaga Umaiman cikin nutsuwa tamkar babu abinda yake wakana wane irin abu Mama tayi amfani dashi da har tayi nasarar shawo kanta haka ta karbi Al'amarin da Salama? Koma dai menene baze tona ba, tunda Allah ya dube shi ya amsa addu'arsa ya tausasa Zuciyar Umaiman shikam ba abinda zeyi sedai ya qara Godewa Allah.

Seda yayi wanka ya gasa jikinsa dan wunin ranar bega ruwa ba tunda ya fita daga gidansu Umaimah office ya wuce babu kowa yau se Masu gadi saboda ba ranar aiki bace ya bude office dinsa kawai ya shiga yana jiran tsammanin jin gidansa ya kama da wuta amma har yamma beji wani labari ba, tunanin ko dai kowa na gidan ya mutu ne yasakashi kiran Jamila ta tabbatar masa da yanzu suka baro gidan Mama Hauwa sun kai Lefe ita ta wuce gida ta tabbatar masa da lafiya lau suka fito kuma gama wayarsu kenan da Hajiya ma da wani abu ya faru bayan fitar su zata gaya musu.

Yunwar da yake ji ta sakashi sake sauka qasan dole, har ya kusa kaiwa qasa ya koma ya dakko Glass dinsa ya saka tubda ya laqawa kansa qaryar ciwon Ido ya ya iya?
Umaimah na zaune tana kallo ya samu kujera daga can gefe ya zauna cikin dar dar kar yaje gadar zare ta shirya masa, Ruqayya ya kwalawa kiraz ta fito ta durqusa daga nesa cikin ladabi ya tambayeta abinci ta wuce Kitchen, a kan Center table ta ajiye masa dan yace baze iya hawa Dining ba. Ua zuba abincin ya fara ci kenan Umaimah ta kalleshi tace
"Dazu Mama tazo ita da Anty Laure"
Shinkafar da yake taunawa ta sarqesgi ya shiga tari babu ji babu gani Umaimah ta matsa ta zuba masa ruwa ya karba yasha kadan ya ajiye idonsa sukayi ja sosai yana maida numfashi, seda taga ya dena tarin kafin taci gaba da maganarta dan ita bata ma lura wai abinda ta fada ne ya kwarar dashi ba.

"To dai tazo tana ta wasu maganganu kayi aure wanene wanene nace ni meye nawa a ciki kaina matar zata zauna ko ni zan ringa ciyar maka da ita ai kanka ka qarowa wahala ko ba haka ba?" Ta qarasa tana kallonsa. Yanda kasan gunko haka Khalil ya zama a gurin, Umaimah taci gaba da cewa
"Ni dana gaji daji ma na shige daki nayi bacci gaba daya bansan me aka daukeni ba wai zata akeyi tsoron kishiya nakeji ne ko Yaya ni yanzu ba mace daya ba ko uku zaka cike an gaya maka hankalina ze tashine nasan duk tsiya badai ka auro wadda ta fini ba kuma koma wacece zatazo a bayana take dan haka Allah ya kawota lafiya ta shigo gata ga gidan ai".

Da yana shaye shaye tabbas ze gasgata abinda ta fada amma ko a magagin mutuwa yake yasan wannan maganar ba gaskiya bace sedai idan ita Umaiman ce ta fara shaye shaye ba kuma ya raba daya biyu akwai wani abun data taka shiyasa tayi wannan ladab din.

"Toh yaushe Amaryar taka zata tare kuma?" Ta sake jefa masa wata maganar seya fara in ina dukda besan ma sanda ya budr baki yayi magana ba yace
"Uhm eh kin gane Umaimah nasan dai Mama tayi miki duk wani bayani ni yanzu bani da bakin da zan kare kaina Allah kuma shine shaidata baniyi komai da niyyar na musguna miki ba, al'amari ne yazo daga Allah babu kuma wanda ya isa ya hana faruwar hakan"

Tsam tayi tana kallonsa har ya kai qarshe seta dauke kanta gefe tana cewa
"Idan ka gama cin abincin Inada Panadol Night zan dakko maka kasha kayi bacci" daga haka ta maida kai kan Tv abinta ba tareda ta bawa maganganunsa muhimmanci ba. Babu shakka shima kan babu dadi ko kuma wani wasan kwaikwayo Mama ta shirya musu to can su gane, kai wannan abun ma babu qanshin gaskiya a ciki, babu yanda za'ayi Khalil yayi aure kamar yanda ake iqirari sannan ya iya zama a gabanta haka ai ba mahaukaci bane shi tsaf yasan abinda zata aikata masa.

Duk yanda yaso yayi mata magana ta hade girar sama da qasa taqi bashi dama haka ya tashi ya koma sama abincin da beci ba kenan dan tunda ya kware ya haqura dashi daman, kwana yayi yana juyi da Jimami, ranar litinin za'a zo yiwa Humaira Jere kamar yanda Baba Abu ya yanke cewar ranar Laraba zata tare, da yamman nan se kashe wayarsa yayi saboda Rigimar data dira masa akan ita ba haka sukayi dashi ba se ya kira Iyayenta yace musu a qara masa lokaci danita ba zasu saurareta ba shiko a sannan yana jiran jin yanda ta qare da Gimbiyarsa bema tsaya wani sauraronta ba yace zasuyi waya daga haka ya kashe wayarsa gashi yanzu Alamu sun Nuna kwakwalwar Umaimah ta qi karbar saqon da ake aika mata, shi kuwa bega abinda ze saka Humaira ta tare a gidansa Alhalin besan makomarsa a hannun Umaimah ba.

Washe gari da safe bayan ya dawo daga Sallar Asuba ya taddota a daki ta idar da Sallah itama tana zaune a qasa, suka gaisa ta kalleshi fuska dauke da Murmushi tace
"Ango Ango"
Gabansa ya yanke ya fadi seya juya ya fasa zaman da yayi niyya Umaimah ta fashe da dariya ganin ya fita kafin ta miqe ta koma kan Gado ta kwanta abinta kafin gari ya qara wayewa tasan abinda zata saka Ruqayya ta shiryawa su Maman Asad da sukace zasu zo yau.

Khalil kuwa bangaren Hajiya ya tafi a daki ya sameta tana sallah dan ta makara tashi yau seda ta idar ta shafa addu'a kafin ya gaisheta ta amsa tana kallonsa ganin yanda duk yayi zuru zuru tace
"Jiya na manta ince maka Hajiya Malika ta zo, wlh banji dadin ganinta ba gaba daya kunya ta dabaibayeni amma naji dadi data fahimci abun kuma Alhamdulillahi gashi ta fahimtar da Umaiman ta karbi qaddara kaga fa yarinyar nan Lubna ashe saboda son tada zaune tsaye da zasu tafi kai kaya har qofa ta kwankwasa mata wai tazo ta gani cikin ikon Allah ta tura mata aniyarta bata kula su ba kaga kuwa ai addu'a tayi tasiri sedai aci gaba da roqon Allah ya sake kore shaidan daga zuciyarta danshi yake ingizata take yin komai amma ba halinta bane".

Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace
"Hajiya ni na kasa fahimtar ta ne gaba daya ma, yanda take magana kamar bata yarda da abinda aka fada bane Kwata kwata fa Hajiya babu alamar damuwa ko wani abu a tattare da ita yanzu fa har tsokanata tayi wai Ango ni wlh Hajiya tsoron ta nake ji saboda Umaimah bata shiru komai qanqantar abu idan akayi mata se tayi magana idan kuwa kikaga tayi shirun to abinda zata aikata se an gwammaci sau dubu ta fitar da abinda yake cikinta wai fa cewa takeyi ina ruwanta idan ma mata uku zan aura ai ba akanta zasu zauna ba Sannan ace lafiya kuwa Hajiya"

"To in banda abunka Babana Mahaifiyarta ce fa tazo da kanta gidan nan kuma dai ka sani a duniya ita kadai take sakata kota hanata abu tayi babu musu yanzun kasan irin abinda ta gaya mata da jan kunnen da tayi mata ka ringa kyautata mata zato mana kuma ma ai wani lokacin idan zuciyar mutum ta qeqashe haqura ma yakeyi da komai. Saboda Allah me kake so tayi kuma aure ne ka rigada kayi to kuma ta wahalar da kanta a wane dalili ai gara ta sallama ta miqa lamarinta ga Allah kawai. Nidai ina da kyakykyawan yaqinin har ranta kamar yanda ta fada babu komai babu din, ka rabu da ita karka ce zaka takurata dole akan seta fitar da fushinta idan ka tunzurota bamu san iya inda rigimar zata tsaya ba dan haka ka barta tunda Allah ya tsayar mana da kansa".

Shidai ko kusa be gamsu da zancen Hajiyar ba amma babu yanda ya iya baze zauna suyi ta ja inja da ita ba amma lashakka yasan babu wata magana da za'a ce wai Umaimah tayi tawakkali farat daya akan maganar auran nan abu biyu ne kuma ciki dole daya ya tabbata, kodai dagaske ta toshe tunaninta taqi fahimtar abinda ake gaya mata saboda tana ganin hakan baze taba yuwuba ko kuma tanada wani tanadi na daban akan al'amarin a cikin biyu babu wanda yake so ya zama gaskiya saboda dukka sakamakonsu baze kasance me kyau ba. Yinin ranar shima beyi shi a gidan ba, kafin ya fita seda ya faki idonta, tana Kitchen tareda Ruqayya ya Ya dakko spare keys din gidan da suke a dakinta ya ciri wadanda yake da buqata. Seda ya bude Part din daya ginawa kansa amma jarabarta tasa ya haqura da amfani dashi gashi yanzu tayiwa kanta baki kuma ya kamata.

Sammani ya kira da wani Yaro Ahmad dake gadin maqotansu, cikin taka tsantsan ya shigar dasu, seda suka share gurin tas suka goge dukda ba qurace kawai babu wani datti a gurin ya duba komai lafiyarsa qalau sannan ya sallame su ya koma dakinsa yayi wanka ya shirya ya fita, gidan Unaizatu ya fara zuwa ya kai musu Key kamar yanda suka buqata, Be samu Humaira ba daman sunyi waya ta sanar masa zataje can gidan Mama da akwai qannen Mahaifiyarta guda biyu da suka zo daga Gashaka jiyan Mama tace taje saboda sunce akwai abubuwan da suka zo mata dasu gashi babu isashshan lokaci dan haka kome zasuyi ya kamata ayi da wuri.
Chapter 198 · 0% Book details